Thursday 22 December 2011

GABATARWA

                                                      Sayyid Zakzaky {H}

BISA LA'AKARI DA ZANCEN DA MALAM MUHAMMAD MUHAMUD TURI YA YI A KASET
DIN DA NA TSARABAR IRAN, INDA YAKE CEWA: "AKAWI BUKATAR 'YAN UWA SU MAIDA HANKALI SOSAI WAJEN YADA DA'AWAR SAYYID ZAKZAKY {H} A KAFAFEN SADARWA NA ZAMANI KAMAR SU JARIDU DA GIDAJEN REDIYO, GIDAJEN TV, 'INTERNET' {YANAR-GIZZO} DA DAI SAURAN SU IN JI MALAMIN.

SANNAN KUMA AKWAI MAGANAR DA MALAMA ZAEENATU IBRAHIM TAKE YAWAN MAIMAITAWA KUMA HAR TA TABA FADIN WANNAN 'KAULIN' A WAJEN 'PROGRAM' DIN DA 'YAN UWA MATA DA SUKA SHIRYA A 'HALL' DAKIN TARO NA YARBAWA WATO 'GOOD-WILL HALL' DA KE TSOHON KWATA, INDA TAKE CEWA: "DUK WANI DAN UWA KO 'YAR UWA DA SUKE DA WANI ABU DA ZA SU YI DON CI GABAN WANNAN HARKA, TO, KOFA A BUDE TAE"

WADANNAN KALAMAI SUKA SA MUKA GA CEWA YA DACE MUMA MU BADA TAMU GUMMAWA JAJEN CI GABAN WANNAN HARKA A ZAMANANCE. ZA MU RIKA KAWO MAKU RAHOTANNIN 'PROGRAMS' MUSAMMAN WADANDA SUKA SHAFI SULEJA DA KEWAYE, RABUCE-RUBUCE NA MUSAMMAN, TARIHIN MANYAN MALAMAI DA KUMA CIGABAN DA DUNIYAR MUSULMI KE SAMU A WANNAN LOKACI NAMU DA KUMA TAFSIRAI DA LACCOCI DA JAWABAN PROGRAMS WADAN SUKA SAWWAKA NA SAYYID ZAKZAKY
[H} DA DAI SAURAN SU. INSHA'ALLAN!

MUNGODE
NAKU A KODAYAUSHE: SULEJA MEDIA WATCH

TARIHIN HARKA A NIGERIYA

                                                    Sayyid Zakzaky {H}      


                                         TARIHIN HARKA A NIGERIYA! 
                                                      
Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta tsiro ne tun kafin cin nasarar juyin juya hali na kasar Iran, watau tun lokacin shi Sheikh din yana dan makaranta a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria. Sai dai a hankali ne harkar ta rika daukan siffa yayin da su yan uwa na harkar suke kara yawa kuma suke kara samun tarbiyya da ilmi na addinin musulunci. Daga cikin irin ayyukan tarbiyya da harkar ta dauka akwai irin su karantarwa da ake kira Ta'alim,Ijtima, Daura,Ribat...




TA'ALIM

Wannan wani dandali ne na karantarwa da ake yi mafi yawa a masallatai na unguwowi daban daban na garuruwan da yanuwa din suke. Akan sa rana guda ne ko biyu gwargwadon yadda zai zama daidai da zarafin su yan uwa din inda ake taruwa maza da mata tare da jagorancin wakilin wannan gari inda za'a karanta hadisai da ayoyi na tarbiyyar dabi'u da ruhi don kara samun kusanci da Allah tabaraka wa ta'ala. Baya ga wannan ta'alim na kowa da kowa kuma kawai wani na daban wanda mafi yawa ake yi tsakanin wasu zababbu daga cikin yan uwa don karantarwa ta musamman ta yadda su wadannan yan uwa sun kasance sun fi sauran fadin ilmi da fahimta da dai sauransu.

IJTIMAH

Wannan ma wani bangare ne na ayyukan da aka sa agaba a harkan domin ganin an inganta tarbiyyan yanuwa koda yake ita ijtimah ta kasance tun a farko-farkon kafuwan harkan inda ake taruwa a daya daga masallatan jummu'a na garuruwan Kano da Zaria domin gudanar da manyan ijtima'oi ko kuma masallatan jummu'a na garuruwa daban daban don gudanar da kananan ijtimao'i. Daga baya bayan da harakr ta kara bunkasa sai ya zamana wannan nauin tarbiyyar ba zai yiwu ba saboda dalilai masu yawa ciki har da yawan jama'a don haka sai aka koma yin "Daura" maimakon ijtimah.

DAURA

Kamar yadda muka ambata a sama "Daura" ce ta maye gurbin ijtimah bayan da matsayin ijtimah din ya zama ba mai yiwuwa ba. Yadda aka saba gudanar da wannan abu kuwa shine ta hanyar shirya jawabai na malamai tare da mauduai daban daban da suka shafi tunani watau kyautata fikra kyautata dabi'au gayaran ruhi da dai sauran su wanda ake yi da manufar budawa yanuwa hanyar gyaran kai na tsawon kimanin kwanaki kamar bakwai watau sati daya. Mafi yawa a karshen ko wacce daura akan rufe ne tare da jawabin  jagoran harkan Mallam Ibrahim Zakzaky. Galibi wannan daura kan banbanta da Mu'tamar wanda ake gabatar da shi ta hanyar gayyatan sauran musulmi na gari kowa da kowa kuma galbi yakan fi yawan jama'a.

MU'TAMAR 

Kamar yadda muka ambata wannan shima wata hanya ce ta haduwan yanuwa da kuma bayar da tarbiyya domin akan hadu ne a daya daga cikin dakunan taro na zamani ko daya daga cikin masallatai na gari don gudanar da shi. Inda ake gayyatar Malamai daga bangarori daban na kasar don gabatar da laccocin su akan mauduai daban daban don kyautata tarbiyyar juna. Shima a mafi yawan lokutta ana rufewa ne tare da jawabin jagoran harkar Mallam Ibrahim Zakzaky.

WA'AZOZIN RANAKUN JUMMA'A

Wa'azozin ranakun jummu'a na daya daga cikin manyan ayyukan wannan harkar inda ake samun haduwa da jama'ar musulmi a garuruwan daban daban don bijirar da matsaloli na duniya da kuma musamman ma abin da yake damun musulmi a wannan lokacin saboda samun karin haske kan abin da kuma shiray tunanin musulmi din don ingantacciyar mafihimta game da yanayi da kuma siyasar dake cikin irin wannan abu. Haka nan kuma ta wannan hanya ana samun yin magana kan al'amurran da suke bijirowa kamar irin su lokutan watannin azumi, Hajj, da dai sauran watanni na ibada na musulmi, don karin haske kan irin abin da suka doru akan al'ummar musulmi na farilla da mustahabbai.
Babu shakka a wasu masallatai da ya zamana ba zai yiwu a aiwatar da wannan abu kafin huduba ba ana samu ne a aiwatar bayan salla jumma'a kafin mutane su watse su nufi gidajen su.

BUKUKUWA DA RANAKUN JUYAYI.

Daga cikin abin da yanuwa suka sa a gaba akwai tunawa da ranakun farin ciki da kuma na bakin ciki watau bukukuwa da kuma juyayi na munasabobin ma'asumai da magabata don yin nazari kan rayuwarsu mai albarka da kuma daukan darasi a cikin rayuwar mu ta yau da kullum. Shima wannan wasu lokuta ana yin su ne ta hanyar wakilan wannan harka din a garuruwa daban daban ko kuam ta jagoran hakar Mallam Ibrahim Zakzaky. Cikin irin ranakun da ake gabatar bukukuwa don tunawa da su akwai kamar su ranar 17 ga watan Rabiul Awwal watau ranar haihuwar fiyayyen halitta Manzon Allah[SAWA], 15 ga watan Sha'aban watau daidai da ranar da aka haifi Sahibuzzaman Imam Mahdi[AS], ranar haihuwar sauran a'imma da dai sauran bayin Allah na gargaru.  Ranakun juyayi sun hada da ranar wafatin Manzon Allah[SAWA], ranar shahadar Imam Hussain[AS] a Karbala... da dai sauransu.

MUZAHARORI

Muzaharori ko kuma jerin gwano na daya daga cikin hanyar da wannan harka ke bi saboda bayyana abu muhimmi daya shafi al'ummar musulmi kamar ranakun Qudus wanda akae gabatar da jerin gwano na gaba dayan kasar sannan kuma ko wanne gari su gabatar nasu na daban don nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinawa da kuma yin tofin Allah ya tsine ga su haramtacciyar kasar Isra'ila kan irin ta'addancin da take tafkawa a yankin na Palasdin. Koda yake dai a mafi yawan lokaci ana kokarin gabatar da wannan muzahara ta ruwan sanyi amma lokuta da dama ana samun matsalar kawo hari daga bangaren yan sanada da jami'an tsaro. 

MENE NE HADAFIN HARKAR MUSULUNCI A NIGERIYA?
Babban hadafin da wannan harka ta musulunci a Nigeria karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta sanya a gaba shine neman mafita da uzuri[.....ma'aziratan ila rabbikum.....] wajen Allah ta'ala. Watau neman yardan Allah da kuma sauke takalif shine babban hadafin wannan harka, kamar yadda yazo a kissan Al-kur'ani mai girma cikin kissar Bani Isra'ila [ashabussabt].



"Duk lokacin da mutum ya sami kanshi cikin al'umma wadda ta bar tafarkin Allah kuma ta kama wata hanya ta daban to lallai akwai abin da ya doru a kanshi na yin amr-bil ma'aruf da nahyu anil munkar.. gwargwadon halin sa da kuma mukamin sa, wannan kuma shine hadafin da wannan harka ta sa a gaba."

NAKU: SULEJA MEDIA WATCH