Sunday 20 May 2012

ABDULLAHI BIN SABAH DA SHI'A

SHI'A DA ABDULLAHI BIN SABAH
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Daya daga cikin hanyoyin da makiya suka dinga bi duk tsawon tarihi wajen shafa bakin fenti da toshe hasken Ahlulbaiti (a.s), duk da cewa dai ba za su iya ba, ita ce hanyar kirkirar karya da jingina ta ga Ahlulbaitin ko kuma ga tafarkinsu. Daya daga cikin mafi girman irin wadannan kararraki shi ne batun Abdullah bn Saba da suka kirkiro da jingina shi ga wannan tafarki na Ahlulbaiti (shi'a) a matsayin wanda ya kirkiro shi, kamar yadda muka yi bayani a rubutun da muka yi a baya kan "Asalin Kafuwar Shi'a". Malamai da masu bincike daban-daban sun yi rubutu kan wannan labari na 'Abdullah bn Saba' da kuma nuna rashin ingancinsa, suna masu cewa shi ma dai wannan mutumi (Ibn Saba) ba a ma halicce shi ba, wato a duniyan nan babu wani mutum mai suna Ibn Saba, face dai makiya ne suka kirkiro shi don wannan buri da muka yi bayani a sama.

Daya daga cikin malaman da suka yi bincike kan wannan kirkirarren mutum (Ibn Saba) da tabbatar da rashin ingancin samuwarsa shi ne Allamah Sayyid Murtadha al-Askari da ke zaune a birnin Tehran na Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin littafinsa mai suna Abdullah bn Saba wa Asatir Ukhra ya yi cikakken bayani kan wannan batu inda ya tabbatar da karyar masu ikirarin samuwar wannan kirkirarren mutum.

Don haka abin da ke biye kadan ne daga cikin abubuwan da wannan littafi ya kunsa da kuma hujjojin da Allama al-Askarin ya kawo da ke tabbatar da rashin ingancin wannan ikirari:

Tun shekaru aru-aru malaman tarihi suke ta rubuta labarurrukan ban mamaki dangane da 'Abdullah bn Saba' da mabiyansa da suka kira Sabi'awa. Abin tambaya a nan shi ne:

Wane ne Ibn Saba sannan kuma su wane ne Sabi'awa (mabiyansa)?.
Mece ce da'awar da yake yi, sannan kuma wasu muhimman ayyuka ne ya aikata?
Yanzu bari mu yi dubi kan kadan daga cikin abubuwan da irin wadannan malumman tarihin suka fadi dangane da wannan kagaggen mutum: Malumman dai sun ce shi bayahude ne da ya zo daga Sana'a na kasar Yemen inda ya yi ikirarin karbar Musulunci a lokacin halifancin halifa Usman sannan ya ci gaba da kulla makirce-makirce ga Musulunci da musulmi ta hanyar yawace-yawace tsakanin garuruwan musulmi irinsu Kufa, Basra, Sham da Masar yana ta yada akidar cewa Manzon Allah (s.a.w.a) zai dawo duniya kafin karshenta kamar yadda Annabi Isa (a.s) zai dawo, da kuma cewa Ali shi ne wasiyyin Manzon Allah (s.a.w.a) kamar yadda kowani Annabi ya ke da wasiyyi, kuma Ali shi ne cikamakin wasiyyai kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a) shi ne cikamakin Annabawa, sannan kuma halifa Usman ya kwace hakkin wannan wasiyyi (Ali) ne don haka wajibi a kawar da shi da dawo da wannan hakki ga mai shi.

Su dai wadannan malamai sun kira wannan gwarzo na tarihin nasu da suna 'Abdullah bn Saba' kuma suka masa lakabi da 'Ibn al-Amatu al-Sawda' (wato dan bakar baiwa). Har ila yau sun ci gaba da cewa shi wannan mutumin ya watsa da dama daga cikin mabiyansa zuwa kasashen musulmi da ikirarin cewa suna yada asalin Musulunci da kuma umarni da ayyuka na kwarai da hani da munana, da kuma kiran jama'a da su yi tawaye ga shuwagabanninsu. Daga cikin mutanen da suka karbi wannan kira nasa har da wasu manyan sahabbai da tabi'ai irin su Abu Zar, Ammar bn Yasir, Muhammad bn Abi Huzaifa, Abdurrahman bn Udais, Muhammad bn Abi Bakr, Sa'asa'a bn Sauhan al-Abdi , Malik al-Ashtar da dai sauransu daga cikin manyan musulman farko.

Har ila yau kuma sun ce: Sabi'awa a duk inda suke suna kokarin janyo mutane zuwa ga tafarkinsu, sun kasance sukan tunzura mutane a kan shuwagabanni abin da har ya sanya mutanen suka nufi Madina da kuma mamaye gidan halifa Usman kana daga karshe suka kashe shi. Sannan kuma sun ce wai: bayan da musulmi suka yi mubaya'a ga Ali, Talha da Zubairu sun yi masa tawaye inda suka nufi Basra don yakar Ali (a yakin Jamal). Lokacin da wadannan Sabi'awa suka ga za a yi sulhu tsakanin bangarorin biyu (na Ali da 'yan tawaye) sai suka fahimci cewa hakan zai sa a nemi diyyar jinin halifa Usman da aka zubar, don haka sai suka fara kulla makirce-makirce da rura wutan yakin a fakaice ba tare da bangarorin biyu sun gane ba. Suka shiga cikin dukkanin rundunonin da haifar da yaki a tsakani, wato dai a takaice haka yakin ya faru ba tare da jagororin bangarorin biyu sun ma san abin da ke gudana ba.

Haka dai kissar Sabi'awan ta kare ba tare da malaman sun sake ambatar wani abu dangane da su ba.

To amma don karin haske kan rashin gaskiyar wannan labari da kuma tabbatar da kirkirarsa aka yi don wata manufa, bari mu yi dubi cikin rayuwar kadan daga cikin wadannan fitattun bayin Allah da aka ce suna daga cikin Sabi'awa, wadanda wani bayahude (Abdullah bn Saba) ya yi wasa da hankulansu da kuma tusa musu mummunar akidarsa.

Wadannan manyan mutane dai su ne:

Abu Zar al-Gaffari.
Ammar bn Yasir.
Muhammad bn Abi Huzaifa.
Abdurrahman bn Udais.
Muhammad bn Abi Bakr.
Sa'asa'a bn Sauhan al-Abdi.
Malik al-Ashtar.
1- Abu Zar al-Gaffari, Jundub bn Junada:

Shi ne mutum na hudu daga cikin mutanen da suka fara karban sakon Musulunci. A da dai ya kasance daga cikin masu bauta wa gumaka, amma lokacin da ya musulunta sai ya zo dakin Ka'aba ya bayyanar da Musuluncinsa, inda Kuraishawa suka ta dukkansa har sai da suka sumar da shi, bayan da ya farfado sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya umarce shi da ya koma garinsu, bayan yakin Badar da Uhud, ya dawo Madina inda ya ci gaba da zama tare da Manzo har lokacin da ya rasu, sai ya koma Sham ya ci gaba da zama, to sai dai daga baya halifa Usman ya dawo da shi ya kuma tura shi gudun hijira zuwa wani kauye da ake kira Rabaza, inda ya rasu a can shekara ta 32 bayan hijira.

Akwai ruwayoyi daban-daban da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) da suke fadin falala da daukakan Abu Zar, daga ciki kuwa har fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Hakika tsakanin kasa da sama babu mai fadin gaskiya kai tsaye da sadaukarwa kamar Abu Zar"(1).

2. Ammar bn Yasir:

Wanda kuma ake kira da Abu Yakzan, ya kasance daga cikin kabilar Bani Tha'alaba, mahaifiyarsa ita ce Sumayya. Shi da mahaifansa suna daga cikin mutanen da suka fara karban sakon Musulunci, shi ne mutum na bakwai daga cikin wadanda suka fara karban Musulunci. Bayan karbar Musuluncinsu, Kuraishawa sun ta azabtar da su har suka kashe mahaifansa.

Akwai ruwayoyi da dama da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) da suke magana kan daukakarsa. Daga cikin akwai fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Hakika (zuciyar) Ammar cike take da imani". Ya kasance tare da Amirul Muminina Ali (a.s) a yayin yakin Jamal da Siffin, ya yi shahada ne a fagen fama (a yakin Siffin) yana dan shekara 93 a duniya(2).

3. Abul Kasim Muhammad bn Abi Huzaifa:

Mahaifinsa shi ne Utbah bn Rubai'a al-Abshami, mahaifiyarsa kuwa ita ce Sahlah bint Suhail Ibn Amr al-Amiriyya, an haife shi ne a Habasha lokacin Manzon Allah (s.a.w.a), halifa Usman ya dauki nauyin kula da shi bayan shahadar mahaifinsa a Yamama. Lokacin halifancin halifa Usman, ya amince wa Muhammad da ya tafi Masar, to sai dai daga baya Muhammad ya yi wa gwamnan Masar din Abdullah bn Sa'ad bn Abi Sarh tawaye lokacin da ya tafi Madina a shekara ta 35 hijiriyya da nada Ukba bn Amir da ya yi a matsayin mataimakinsa. Daga baya kuma ya hana gwamnan dawowa garin bayan da jama'a suka masa mubaya'a. Bayan wani lokaci kuma (saboda wasu dalilai) ya aika da kimanin mutane 600 karkashin jagorancin Abdurrahman bn Udais zuwa Madina don yakan Usman. Ya ci gaba da mulki har lokacin da Mu'awiyya ya iso Masar a hanyarsa ta zuwa Siffin, inda Muhammad ya tsare shi a Fostat (wani gari ne da ke Masar da Amru bn al-Aas ya gina bayan cin Masar da yaki) da hana shi shiga, to sai dai daga baya an yi sulhu kan cewa Muhammad da mutanensa 30 (ciki har da Abdurrahman bn Udais) za su fita daga garin ba tare da Mu'awiyya ya cutar da su ba. Amma daga baya Mu'awiyya ya karya wannan yarjejeniya inda ya kame su da tsare su a Damaskus, daga baya kuma bawan Mu'awiyyan mai suna Roshdain ya kashe shi. Muhammad yana daga cikin sahabban Manzon (s)(3).

4. Abdurrahman bn Udais al-Balwi:

Yana daga cikin sahabban da suka yi mubaya'a ga Manzon Allah (s.a.w.a) a karkashin bishiya (Bai'at al-Shajara), yana daga cikin wadanda suka ci Masar da yaki, sannan kuma shi ne ya jagoranci mutanen da suka kai hari wa halifa Usman (saboda wasu dalilai) daga Masar. Mu'awiyya ya kama shi tare da Muhammad bn Abi Huzaifa bayan sun bar Masar da tsare shi a Palastinu kana daga baya ya kashe shi a shekara ta 36 hijiriyya bayan tserewar da ya yi daga gidan yari da sake kame shi da ya yi(4).

5. Muhammad bn Abi Bakr:

Mahaifiyarsa ita ce Asma'u bint Umais, halifa Abubakr ya aure ta ne bayan shahadar mijinta Ja'afar bn Abi Talib inda ta haifi Muhammad. Bayan mutuwar mahaifinsa, Imam Ali (a.s) ya dauke shi da kula da shi. Ya kasance tare da Imam Ali (a.s) a yakukuwan Jamal da Siffin, daga baya kuma ya nada shi gwamnan Masar. Mu'awiyya ya tura da runduna karkashin jagorancin Amru bn al-Aas don yakansa a Masar inda suka sami nasarar kama shi da kashe shi, daga baya kuma suka sanya gawarsa cikin cikin wani macaccen jaki da kona shi(5).

6. Sa'asa'a bn Sauhan al-Abdi:

Ya musulunta ne a lokacin Manzon Allah (s.a.w.a), ya kasance mutum mai fasaha wajen magana, sannan kuma ya kasance tare da Imam Ali (a.s) a Siffin. Mu'awiyya ya kore shi zuwa Bahrain bayan da ya dare karagar mulki, inda ya rasu a can(6).

7. Malik al-Ashtar al-Nakha'i:

Ya riski Manzon Allah (s.a.w.a) sannan kuma yana daga cikin mutane masu gaskiya da rikon amana, ya samu wannan lakabi na al-Ashtar ne bayan ciwon da ya samu a idonsa a yakin Yarmuk. Ya kasance tare da Imam Ali (a.s) a yakukuwan Jamal da Siffin kuma ya taka gagarumar rawa a cikinsu. Imam Ali (a.s) ya nada shi gwamnansa a Masar a shekara ta 38 hijiriyya, to sai dai a hanyarsa ya yi shahada sakamakon guban da Mu'awiyya ya sanya masa cikin abinci(7).

To wannan dai shi ne labari ko tatsuniyar samuwar Abdullah bn Saba, sannan wadannan mutane kuma da ma wasunsu su ne fitattun Sabi'awa da wasu malaman tarihi (abin bakin ciki) suka ce su ne mabiya wannan 'bayahude', wanda ko ba a fadi ba sun fi karfin a ce wani bayahude ya zo dare guda ya yi wasa da hankulansu da mai she su yaransa. Daga baya dai za mu ga manufar wadannan mutane na kirkiran wannan labari maras tushe na samuwar mutumin da suka kira Abdullah bn Saba.

Tushen Wannan Kagaggen Labari:

Bayan mun ga wannan kagaggen labari, yanzu kuma bari mu ga tushe da kuma inda labarin ya fito sannan kuma mu ga rashin ingancinsa.

Cikin karnoni goma da suka wuce da wuya ka samu wani malamin tarihi da zai yi rubutu kan sahabbai da bai tabo wannan tatsuniya ta Abdullah bn Saba ba. Don gane inganci ko rashin ingancin wannan labari dole ne a koma ga tushen da wannan labari ya fito da kuma inda masu kawo shi suka samo shi. Yanzu bari mu yi dubi cikin wasu daga cikin mutanen da suka yi rubutu kan wannan kagaggen mutumi, don ganin inda suka dauko labarin nasu:

1. Muhammad Rashid Ridha:

A cikin littafinsa mai suna al-Sunna wa al-Shi'a shafi na 4-6, Muhammad Rashid Ridha na cewa: "Shi'ancin halifa na hudu Aliyu bn Abi Talib (r.a.) dai shi ummul aba'isin kana mafarin rarrabuwan wannan al'umma ta Muhammadu a bangaren addini da siyasarta. Wanda ya kirkiro ta kuwa shi ne wani bayahude mai suna Abdullah bn Saba, wanda ya ce wai ya musulunta don yaudara, ya yi kira wajen wuce gona da iri (guluwi) akan Ali (karramallahu wajhahu) don rarraba kan wannan al'umma da lalata mata duniyarta da lahirarta". Daga nan sai ya ci gaba da cewa: "Duk wanda ya duba kissar Yakin Jamal cikin tarihin Ibn Athir zai ga irin tasirin da Sabi'awa suka yi wajen hana wanzuwar sulhu,".

A nan za mu ga cewa tushen da Muhammad Rashid Ridha ya dogara da shi wajen wannan labari na sa shi ne Tarikh al-Kamil na Ibn Athir.

2. Abul Fida' Isma'il bn Ali Imaduddeen

Shi ma yayin da yake kawo wannan labarin cikin littafin al-Mukhtasar fi Akhbar al-Bashar cewa ya ke yi: "Na takaita wannan labarin ne cikin littafina daga abin da na dauko daga littafin Shaikh Izzuddeen Ali wanda aka fi sani da Ibn Athir al-Jazari".

A nan za mu ga tushen labarin wadannan malamai biyu dai shi ne Ibn Athir. To yanzu ba ri mu ga shi kuma Ibn Athir daga ina ya samo nasa labarin.

3- Ibn Athir:

Idan muka duba littafin tarihi na Ibn Athir (wanda ya rasu a shekara ta 630 hijiriyya) za mu ga ya kawo wannan labari dukkansa cikin abubuwan da suka faru a shekara ta 30-36 hijiriyya sai dai kawai bai kawo tushen da ya dogara da shi ba sai cikin gabatarwar littafin nasa, inda ya ke cewa ya dibo labarin nasa ne daga littafin Imam Abu Ja'afar al-Tabari, wanda ya ce shi ne littafin da malamai suke komawa gare shi a lokacin da suka sami sabani.

Wannan dai shi ne abin da Ibn Athir, wanda Muhammad Rashid Ridha da Abul Fida' suka samo daga gare shi, yana cewa tushen labarinsa shi ne al-Tabari.

4. Ibn Kathir:

Haka nan shi ma Ibn Kathir, wanda ya rasu a shekara ta 774 hijiriyya, ya kawo wannan labari cikin juzu'i na 7 na littafinsa Al-Bidaya wa al-Nihaya, shafi na 167, inda yake cewa: "Saif bn Umar yana cewa musabbabin boren da aka yi wa Usman shi ne wani mutum da ake ce ma Abdullah bn Saba - asalinsa bayahude ne sai ya bayyanar da musuluncinsa inda ya tafi Masar ya sanya wasu maganganu da ya kirkiro ga wasu mutane". Daga nan sai ya ci gaba da bayani har ya kai batun yakin Jamal, inda yace: "Wannan shi ne takaiceccen bayanin da Abu Ja'afar bn Jarir - Allah Ya jikansa - ya rubuta".

A nan muna iya fahimtar cewa al-Tabari dai shi ne tushen labarin Ibn Kathir.

5- Ibn Khaldun:

Shi ma Ibn Khaldun cikin littafin tarihinsa mai suna Al-Mubtada' wa al-Khabar ya kawo labarin Sabi'awa yayin da yake magana kan kashe halifa Usman da kuma yakin Jamal, cikin juzu'i na 2, shafi na 425 na wannan littafi cewa ya ke yi: "Wannan abin da na kalato ne daga littafin Abu Ja'afar al-Tabari saboda tabbaci da ingancinsa...".

Shi ma dai al-Tabari shi ne tushen labarinsa.

6. Ahmad Amin:

Ahmad Amin wanda ya mutu a shekara ta 1373 hijiriyya yana daga cikin malumman wannan zamani da suka yi magana kan Sabi'awa da Abdullah bn Saba, inda a cikin littafinsa mai suna Fajr al-Islam ya yi bayani sosai kan wannan batu da kuma jingina wannan mutum da suka kira Abdullah bn Saba ga kafuwar shi'anci. Shi ma dai tushen labarin nasa shi ne al-Tabari.

Wannan kadan kenan daga cikin malumman da suka ruwaito wannan tatsuniya daga wajen Tabari. To yanzu bari mu yi dubi kan shi kansa Tabarin mu ga shi kuma daga ina ya samo nasa labarin:

Tabari Da Tushen Labarinsa:

Abu Ja'afar Muhammad bn Jarir bn Yazid al-Tabari al-Amuli, wanda ya rasu a shekara ta 310 hijiriyya ya samo kissar Sabi'awa cikin littafinsa mai suna Tarikh al-Umam wa al-Muluk daga wajen Saif Ibn Umar al-Tamimi ne kawai. Yayin da yake magana kan abubuwan da suka faru a shekara ta 30 hijiriyya cewa ya ke yi: "A wannan shekara , wato shekara ta 30 an ambaci abubuwa daban-daban kan abubuwan da suka faru tsakanin Mu'awiyya da Abu Zar, ba na so in ambato su duka, al-Sari ya rubuta min dangane da wadanda suke ba wa Mu'awiyya uzuri kan batun Abu Zar. Shu'aib ya gaya wa al-Sari cewa Saif yana cewa" Lokacin da Ibn Sawda' (Abdullah bn Saba) ya iso Sham ya gana da Abu Zar yana ce masa: Ya Aba Zar ba ka ga abin da Mu'awiyya ya ke aikatawa ba..."(8).

Daga nan sai Tabari ya kawo kissar Ibn Saba da Abu Zar ta hanyar Saif kawai, inda ya cika maganar tasa da cewa: "Amma wasu sun ruwaito dalilai da dama kan wannan lamari (mayar da Abu Zar Madina da Mu'awiyya ya yi) da kuma wasu munanan abubuwa da ba na son kawo su a nan".

Har ila yau kuma yayin da yake batun abubuwan da suka faru a shekara ta 30-36 hijiriyya ya kawo kissar Ibn Saba da Sabi'awa wajen kashe halifa Usman da kuma yakin Jamal ta wajen Saif shi kadai dinsa ba tare da dogaro da wata hanya ta daban ba.

Don haka Tabari dai yana samo bayanansa daga Saif ne ta hanyoyi biyu:

Ubaidullah bn Sa'id al-Zuhuri daga baffansa Ya'akub bn Ibrahim daga Saif. A nan Tabari ya kan samo hadisan Saif ne ta harshen baki.
Al-Sari bn Yahya daga, daga Shu'aib bn Ibrahim, daga Saif. A nan Tabari ya kan samo hadisan Saif din ta hanyar rubutu, wato ta hanyar littattafan nan nasa guda biyu Al-Futuh al-Kabir wa al-Ridda da kuma Al-Jamal wa Masir A'isha wa Ali.
Daga nan za mu fahimci cewa tushen kissar Tabari shi ne Saif bn Umar al-Tamimi.

Akwai kuma wasu malumman na daban wadanda su ma sun ruwaito kissar Abdullah bn Saba da Sabi'awa sai dai ba ta hannun Tabari ba, su sun ruwaito tasu kissar ne ko dai kai tsaye daga Saif bn Umar ko kuma wasu da suke kusa da shi. Daga cikin wadannan malumma akwai:

1. Ibn Asakir

Ibn Asakir wanda ya rasu a shekara ta 571 hijiriyya yana da nasa tushen da ya samo wannan labari na Ibn Saba da Sabi'awa a cikin littafinsa mai suna Tarikh Damashk. Wannan tushe ko hanya ta Ibn Asakir zuwa ga hadisan Saif kuwa ita ce: Abul Kasim Sarmakandi, daga Abul Husain al-Nakkur, daga Abu Tahir al-Mukhallas daga Abubakar bn Saif daga al-Sari bn Yahya daga Shu'aib bn Ibrahim daga Saif bn Umar(9).

Wannan dai shi ne tushen da Ibn Asakir ya ruwaito nasa labarin da yake karewa zuwa ga Saif bn Umar.

2- Al-Zahabi:

Shi ma Zahabi wanda ya rasu a shekara ta 747 cikin littafinsa Tarikh al-Islam ya ruwaito wannan labarin yayin da yake magana kan kashe halifa Usman da kuma abubuwan da suka faru a shekara ta 35 hijiriyya, cikin juzu'i na 2 shafi na 122-128 na wannan littafi ya kawo wannan labari inda yake cewa: "Saif bn Umar daga Atiya daga Yazid al-Fak'asi yace: 'Lokacin da Ibn Sawda' (Abdullah bn Saba) ya isa Masar...".

A nan ma za mu ga tushen wannan labari na al-Zahabi shi ne Saif bn Umar al-Tamimi. Da dai sauran malamai da suka yi magana kan wannan batu.

Daga abin da ya gabata za mu ga cewa tushe da mabubbugan dukkan wadanda suka yi magana kan Abdullah bn Saba da mabiyansa (Sabi'awa) shi ne Saif bn Umar al-Tamimi shi kadai dinsa. Wato wasu daga cikinsu sun samo wannan labari ne kai tsaye daga wajen Saif wasu kuma sun samo shi ba kai tsaye ba.

Wane Ne Saif bn Umar Da Kuma Ingancin Labaransa:

To yanzu bari mu yi dubi mu ga shin wane ne wannan Saif din da ake magana a kansa, sannan kuma mene ne ra'ayin malamai dangane da labaran da ya kawo.

Shi ne dai Saif bn Umar al-Tamimi al-Usayyadi kamar yadda ya zo cikin Tabari, juzu'i 1shafi 1749 da Urobba wa Lubabul Ansab juzu'i na 1, shafi na 49. Shi dai asalinsa mutumin Kufa ne amma ya rayu ne a Bagadaza. Kuma kamar yadda wasu bayanai suka nuna ya mutu ne a shekara ta 170 a lokacin mulkin Haruna Rashid. Wasu kuma suna ganin ya mutu ne a shekara ta 200.

Kimanta Hadisan Saif

Da yake mun ga dan kadan daga cikin tarihin Saif, yanzu kuma bari mu ga kima da mizanin inganci ko rashin ingancin hadisansa a mahangar malamai.

Yahya Bn Mu'in (233 H): "Hadisansa raunana ne marasa tushe". (Dubi Mizan al-I'itidal, juzu'i na 2, shafi na 255)..
Abu Dawud (275 H): "Shi ba a bakin komai yake ba, makaryaci ne".
Nisa'i (303 H): Cikin Sunan yana cewa: "Hadisansa masu rauni ne, yasassu ne, ba bin dogara ba ne kuma ba abin amincewa ba ne".
Ibn Abi Hatam (327 H): "(hadisansa) yasassu ne".
Ibn al-Sakan (353 H): "(hadisansa) raunana ne".
Ibn Udaiy (365 H): raunana ne, wasu daga cikin hadisansa sanannu ne amma dai ba a aiki da su.
Al-Hakim (405 H): "(hadisansa) yasassu ne, ana tuhumarsa da zindikanci".
Ibn Abd al-Bar (463 H):Ya nakalto daga Abu Hayan cewa: Hadisan Saif yasassu ne, mun kawo su ne kawai don masaniyya kawai.
Firuz Abadi (817 H): Ya ambaci (Saif) tare da wasu mutane ya ce (hadisansu) raunana ne.
Ibn Hajar (923 H): Bayan ya karanto wani hadisi sai ya ce akwai raunana cikin (maruwaitansa) amma wanda duk ya fi su rauni shi ne Saif.
Wannan dai shi ne ra'ayin wasu daga cikin malumma dangane da Saif bn Umar da hadisansa da suke nuna mana rashin nitsuwarsu kan maganganunsa.

To kafin mu je ga karshen wannan bahasi da kuma fitar da natija (sakamako), bari mu kawo labari guda da aka samo daga wajen Saif din da kwatanta shi da yadda sauran malamai suka kawo shi don ganin rashin ingancin maganarsa da kuma irin yadda ya ke juya labarin don biyan bukatu da son zuciyarsa. Wannan labari kuwa da za mu yi dubi a kansa shi ne: Batun Rundunar Usama. Za mu yi wannan nazari ne kuwa ta hanyar dubi cikin masdarori da malaman da suka dogara da hadisan Saif din, wanda Tabari shi ne a gabansu saboda yawan ruwayoyin da ya debo daga Saif din.

LABARIN RUNDUNAR USAMA:

Yadda Saif Ya Kawo Shi:

Ga yadda Saif Ya kawo wannan labari kamar yadda Tabari cikin Tarihinsa juzu'i na 1,da Ibn Asakir juzu'i na 1, shafi na 426 yayin da suke magana kan abubuwan da suka faru a shekara ta 11 bayan hijira, inda suke cewa:

"Manzon Allah (s.a.w.a), kafin rasuwarsa, ya tara rundanar soji ta sahabbai cikinsu har da Umar bn Khattab ya sanya su karkashin jagorancin Usama bn Zaid (don fita yaki), to amma ba su fita daga Madina ba, sai Allah Ya yi wa Manzo rasuwa, don haka sai Usama ya tsaya tsakankanin mutane ya bukaci Umar: da ya koma ga halifan Manzon Allah da ya ba shi izinin dawo da rundunar zuwa Madina". Daga nan sai ya ci gaba da cewa sai wasu daga cikin Ansarawa (Mutanen Madina) suka bukaci Umar da ya ce wa Abubakar ya sake musu Usama da wani mutum a matsayin kwamanda, lokacin da Umar ya gaya wa Abubakar wannan bukata sai ya (Abubakar) mike tsaye ya kama gemunsa yana cewa: "Kaiconka Ya Ibn al-Khattab, Manzon Allah ne fa ya nada shi kai kuma kana son in tube shi da nada wani a madadinsa!!!. Daga nan sai Abubakar ya yi musu wasu wasicci sannan kuma ya yi musu ban kwana..."

Wannan dai shi ne labarin Saif kan abin da ya faru dangane da batun tura sojoji karkashin jagorancin Usama da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi.

To yanzu kuma bari mu ga abin da wasu malumman suka fadi dangane da batu:

"Wata rana ranar Litinin kwanaki hudu kafin fitar watan Safar, Manzon Allah (s.a.w.a) ya umarci sahabbansa da su yi shirin fita yaki da Romawa. Washe gari sai Annabi (s.a.w.a) ya kira Usama ya ce masa kama hanya da (wadannan sojoji) zuwa inda mahaifinka ya yi shahada na nada ka shugabansu….a ranar laraba sai ciwo ya kama Manzon Allah (s.a.w.a), ranar alhamis sai Annabi da kansa ya dauko tuta ya ba wa Usama ya ce masa ya kama hanya…daga cikin sahabban da suke cikin wannan runduna har da manyan Muhajirai da Ansarawa irin su Abubakar al-Siddik, Umar bn al-Khattab, Abu Ubaidah bn al-Jarra, Sa'ad bn Abi Wakkas,Said bn Zaid da dai sauransu. Wasu daga cikinsu sun nuna rashin jin dadinsu kan wanna zabe da Manzo ya yi wa Usama da dora shi a kan manyan Muhajirai, Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi tsananin fushi lokacin da ya ji wannan kunkuni, don haka sai ya fito cikin tsananin rashin lafiya ya hau kan mimbari yana cewa: "Wata magana ce na ke ji daga wajen wasunku dangane da shugabantar da Usama da na yi, haka ku ka yi a baya lokacin da na nada mahaifinsa, wallahi ya cancanci wannan shugabanci kamar yadda dansa ya cancanta, daga nan sai ya sauko……ciwo dai ya ci gaba da zafi wa Manzon Allah (s.a.w.a), ranar lahadi ciwo ya ci gaba da tsananin wa Manzon Allah (s.a.w.a) sai Usama ya shiga zuwa wajensa, amma saboda zafin ciwo Manzon Allah (s.a.w.a) bai iya masa magana ba sai kawai ya sumbance shi don ba ya iya magana. Ranar litinin sai Usama ya sake dawowa a lokacin jikin Manzon Allah (s.a.w.a) ya dan yi sauki sai ya ce masa: Kama hanya cikin kulawar Ubangiji, sai Usama ya yi masa ban kwana. Daga nan sai ya tafi sansaninsa ya umarci mutane da su kama hanya, zai hau abin hawarsa kenan, sai ga manzon ma'aifiyarsa Ummu Aiman yana ce masa Manzo fa zai rasu don haka ka zo. Sai Usama da Umar da Abu Ubaidah suka koma Madina, a wannan ranar ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya rasu. Bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma zaban Abubakar da aka yi a matsayin halifa, sai ya umarci Usama da ya ci gaba da tafiya kamar yadda Manzo ya umarce shi….". Don karin bayani sai a duba Dabakat na Ibn Sa'ad juzu'i na 2, shafi na 190-192 da Uyun al-Athar juzu'i na 2, shafi na 281. Kanzul Ummal juzu'i na 5, shafi 312, Ansab al-Ashraf kan tarihin Usama, juzu'i na 1, shafi na 474 daga Ibn Abbas da kuma tarihinsa (Usama) cikin al-Tahzib na Ibn Asakir juzu'i na 3, shafi na 291 da kuma Tarikh al-Ya'akubi juzu'i na 2, shafi na 74 da kuma Ibn Athir cikin tarihinsa, juzu'i na 2, shafi na 123.

Kwatanta Labaran Biyu:

To yanzu kuma bari mu kwatanta labarin da Saif ya kawo da wanda sauran malamai suka kawo mu ga irin banbancin da ke cikinsu da kuma abin da Saif din ya ke son cimmawa:

Saif ya ce: Sojojin Usaman ma ba su gama fita daga Madina ba sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya rasu, alhali kuwa sauran malamai sun ce sun ma fita har ma sun zauna a sansaninsu da ke wajen Madina na kwanaki.

A nan Saif dai na so ne ya boye kunkuni da ta da jijiyoyin wuya da wasu suka yi ne saboda nada Usama da Manzo ya yi, lamarin da ya sa Manzo din ya yi tsananin fushi, ga shi kuma ya na cikin rashin lafiya, har ma ya ke ta jaddada cewa Usama ya kama hanya ya tafi.

Haka nan Saif ya ce wai lokacin da Usama ya ji labarin cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya rasu sai ya tura halifa Umar wajen magajin Manzon Allah (s.a.w.a) don neman izininsa kan sojojin su dawo gida, alhali kuwa sauran ruwayoyi cewa suka yi lokacin da ya ji labarin jikin Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi tsanani sai ya tafi Madina tare da Umar, Abubakar da Abu Ubaida. Sannan bayan rasuwar Ma'aiki da kuma nada halifa Abubakar ne ya tura sojojin suka ci gaba.

A nan ma dai Saif yana son ya boye wani abu da kuma bayyanar da wasu abubuwa, daga cikinsu kuwa shi ne nuna cewa an ma zabi halifa Abubakar ne tun Annabi (s.a.w.a) yana da rai da dai sauran abubuwa.

Haka nan kuma Saif ya ce Ansarawa ne suka bukaci halifa Abubakar da ya tube Usama da nada wani kwamanda na daban, alhali sauran malumma kuma cewa suka yi Muhajirai ne suka bukaci hakan.

A nan ma dai Saif ya yi kokari juya tarihi ne don biyan bukatan masu mulki na wancan lokacin wadanda Muhajirai ne.
Da dai sauran irin wadannan karo da juna da aka samu cikin labarin Saif din da na sauran marubuta, wannan ke nuna mana kaurin sunan da ya yi wajen kago karya da jingina ta ga sauran mutane.

A hakikanin gaskiya a kusan dukkanin abubuwan da Saif ya kawo labarinsu sai an samu karo da juna idan aka kwatanta da na sauran malaman tarihi, batutuwa kamar su abubuwan da suka faru a Sakifa, yadda aka nada halifa na farko, yakin da ake kira Yakin Ridda da dai sauransu, duk dai da nufin goya wa wadansu mutane baya da kuma cin mutumcin wasu.

Mai karatu, daga abubuwan da suka gabata za mu iya fahimtar rashin ingancin wannan ikirari na samuwar Abdullah bn Saba ballantana ma a jingina shi da kafuwar Shi'anci, hakan kuwa saboda rashin tushen da kuma ingancin yadda aka samo wannan labari. Don kuwa:

Kashin farko na wadanda suka kawo wannan labari sun samo shi daga wajen Tabari, shi kuma Tabari ya samo shi ne daga wajen Saif bn Umar al-Tamimi, wanda aka san shi da karya da kago labarurruka marasa tushe don biyan bukatun wasu mutane.
Kashi na biyu na wadanda suka kawo wannan labari sun samo shi ne kai tsaye ta wajen Saif din da ba a karbar labarinsa saboda karya da kage.
Don haka wannan labari ba shi da wani tushe, don kuwa ya fito ne daga hanyar da ba a yarda da ita saboda cike take da karya da kage-kage, wannan hanya kuwa ita ce Saif bn Umar al-Tamimi.
Wannan dai bayani ne a takaice wanda kowa da kowa zai iya fahimtarsa, don haka babu bukatar mu zurfafa wajen bayani.

Allah dai Ya tsare mu da son zuciya da kuma murguda gaskiya da bayyanar da karya don son zuciyarmu da kuma bakanta wani abu ba don komai ba sai don ya saba wa ra'ayinmu da kuma biyan bukatan wasu mutane
____________

(1)- Tabakat na Ibn Sa'ad, Musnad Ahmad, juzu'i na 2, shafi na 163, 175,223, da kuma juzu'i na 5, shafi na 147, 155, 159, 165, 166, 172, 174, 351, 356 da kuma juzu'i na 6, shafi na 442 da kuma al-Mustadrak na Hakim, juzu'i na 3, shafi na 342. Sai kuma Sahih Bukhari, babin Manakib Abi Zar cikin Kitab al-Manakib, da kuma Sahih Tirmizi da Sahih Muslim Kitab al-Manakib, da Sunan Ibn Majah juzu'i na 1, shafi na 55 da Tabari da Ibn Athir yayin da suke magana kan Yakin Tabuka da dai sauransu.

(2)- Muruj al-Zahab na Mas'udi, juzu'i na 2 shafi na 21 da 22, Tabari da Ibn Athir da Ibn Kathir yayin da suke magana kan abubuwan da suka faru a shekara ta 36-37 hijiriyya, Ansab al-Ashraf na Balazuri, juzu'i na 5, shafi na 48-88, Musnad Ahmad juzu'i na 1, shafi na 99, 123, 125, 130, 137, 404 da juzu'i na 2 shafi na 161, 164, 206 da juzu'i na 3 shafi na 5, 22, 28, 90 da juzu'i na 4, shafi na 76, 89, 90, 197, 198. 319 da juzu'i na 5, shafi na 214, 306 da juzu'i na 6 shafi na 289, 300, 311, 315, 450 da kuma Sahih Bukhari, Kitab al-Jihad, Sahih Muslim cikin Kitab al-Fitan, Sunan al-Tirmizi babi na 33 cikin Kitab al-Manakib da dai sauransu.

(3)- Dubi Tabari, Ibn Athir da Ibn Kathir yayin da suke magana kan abubuwan da suka faru a shekara ta 30-36 hijiriyya al-Isabah karkashin harafin Mim, da al-Isti'ab juzu'i na 3, shafi na 321-322.

(4)- Dubi Tabari, Ibn Athir da Ibn Kathir yayin da suke magana kan abubuwan da suka faru a shekara ta 30-36 hijiriyya da Asadul Gabah, 3/309.

(5)- Dubi Tabari, Ibn Athir da Ibn Kathir yayin da suke magana kan abubuwan da suka faru a shekara ta 37 hijiriyya, al-Isabah karkashin harafin Mim, da al-Isti'ab juzu'i na 3, shafi na 328-329.

(6)- Duba tarihinsa cikin al-Isti'ab da Asadul Gaba da al-Isaba bugun Misira.

(7)- Dubi abubuwan da suka faru a shekara ta 38 hijiriyya cikin littafin Tabari juzu'i na 6 shafi na 54, Ibn Athir, juzu'i na 3 shafi na 14, Ibn Kathir, tarihinsa cikin al-Isaba karkashin harafin Mim da al-Isti'ab juzu'i na 3, shafi na 328 da Muruj al-Zahab juzu'i na 6 shafi na 29 babin Hurubihi (r.a.) ma'a Ahl al-Nahrawan.

(8)- Dubi Tabarin cikin Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 3, shafi na 335.

(9)- Don karin bayani dubi shafi na 304, 484, 485, 496, 513, 545, 547 da 551 na juzu'i na 1 na wannan littafi na Ibn Asakir.

(10)- Suratul Kasas; 28:85.

(11)- Don karin bayani ana iya duba Tarikh al-Tabari, juzu'i na 3, shafi na 378.

(12)- Mai son karin bayani yana iya duba Ibn Athir, cikin al-Kamil, juzu'i na 2, shafi na 24; da Biharul-Anwar, juzu'i na 18, shafi na 164; da Fikihul-Sirah, na Sheikh Muhammad Gazzali, shafi na 102.

(13)- Wadanda suka fitar da wannan sun hada da: Baihaki cikin Sunan da Dala'il da Tha'alabi da Dabari cikin tafsiransu, wajen fassarar Surar Shu'ara'i; da Dabari cikin tarihinsa, juzu'i na 2, shafi na 217; da Ibn Athir cikin al-Kamil, juzu'i na 2, shafi na 22, da Siratul-Halabiyya, juzu'i na 1, shafi na 381; da Ahmad bin Hambali, cikin Musnad, juzu'i na 1, shafi na 11; da Nasa'i cikin Khasa'isu Amirul Mu'uminin, shafi na 6; da Kanzul Ummal, juzu'i na 6, hadisi na 6008, da wasun wadannan da lafuzza masu kusantar juna.

TARIHIN SHI'A DA AKIDOJINTA

TARIHIN SHI'A DA AKIDOJINTA
Ma'anar Kalmar Shi'a:
________________________

A takaice kalmar Shi’a kalma ce ta larabci, wadda ke nufin ‘mabiya’ ko ‘mataimaka’, wannan kuwa shi ne ma’anarta na lugga. Amma so tari ana amfani da ita a kan duk wanda ya fifita Imam Ali dan Abi Dalib (AS) a kan sauran Sahabbai da wanda ya mika wilayarsa gare shi. Wannan shi ne ma’anar kalmar a muhawara da zantukan yau da kullum. Wannan shi ne abin da malaman lugga suka dace a kai. Firuz Abadi yace:

Shi’ar mutum (na nufin) mabiyansa da masu taimaka misa…..

Har zuwa inda ya ce:

Amma hakika wannan kalma an fi amfani da ita a kan duk wanda ya mika wilayarsa ga Ali (dan Abi Dalib) da mutanensa, har kalmar ta takaita da su.[1].

Haka Ibin Athir ya fadi cewa:

Asalin kalmar Shi’a na nufin wani sashi na mutane. Akan fadi kalmar ga mutum daya, ko biyu ko jam’i; kamar yadda akan yi amfani da ita ga namiji ko mace. Amma an fi amfani da ita ga duk mai da’awar (?) cewa ya mika wilayarsa ga Ali dan Abi Dalib (RA) da mutanen gidansa, har wannan suna ya kebanta da su. Idan aka ce “wane dan Shi’a ne” za a fahimci cewa yana cikin su[2].

Har ila yau, a kan haka an fadi cewa:

Shi’a na nufin mutanen da suka hadu a kan wani al’amari. Duk wadanda suka hadu a kan wani abu su Shi’a ne; haka duk wadanda al’amarinsu ya zama daya, wasun su na bin wasu, suma Shi’a ne. Shi’a dai na nufin mabiyan wani mutum da masu taimaka masa. Jam’in kalmar shi ne Shiya’u ko Ashya’u…. Hakika wannan suna ya yi galaba a kan wadanda suka mika Wilaya ga Ali, yardar Allah ta tabbata gare shi, har ya zama sunansu na masamman, idan aka ce wane dan Shi’a ne ana sanin yana cikin su.[3]

Haka bayanin yake a sauran littaffan lugga irin su al-Sihah[4], da al-Misbahul-Munir[5], da Tajul-Arus[6] da wasun su.

a) Kalmar Shi’a Cikin Alkur’ani Mai Girma

Amma a cikin Alkur’ani mai girma, ambaton kalamar Shi’a ya zo a wasu wurare, wani lokaci da sigar mutum daya kamar fadar Allah Madaukaki:-

Wannan na daya daga cikin Shi’arsa (mabiyansa) daya kuma na cikin makiyansa. (al-Kasasi:15)

Da fadarSa Madaukaki cewa:-

Lallai daga cikin ’yan Shi’arsa akwai (Annabi) Ibrahim.. (Al-Safati:83).

Da wasu wuraren.[7] Kamar yadda ya zo da sigar jam’i a wasu wuraren a Alkur’ani mai girma.[8]

Da haka ta bayyana cewa kalmar Shi’a ta zo cikin Alkur’ani mai girma a wasu wurare biyu dauke da ma’anar ‘mabiya’ da ‘mataimaka’. Haka nan Alkur’ani mai girma ya yi amfani da kalmar da sigar jam’i yana nufin kungiyoyi.

b) Kalmar Shi’a A Zantukan Malamai

A duk lokacin da malaman addini da marubuta tarihi –Musulminsu da wadanda ba Musulmi ba, Shi’a da Ahlulssunna daga cikin Musulmi- suka ambaci Shi’a, suna nufin wadannan wadanda suka fifita Imam Ali (AS) a kan sauran Sahabbai, kuma suke ganin cewa shi ne Imami kuma Khalifan Musulmi wanda Manzon Allah (SAWA) ya yi wasici da shi da wasu kebabbu daga cikin zuriyyarsa a bayansa. Ga kadan daga maganganun malamai a kan haka:-

1- Shahid al-thani ya fada a cikin littafinsa na Sharhul- Lum’ah, cewa:

Shi’a (shi ne duk) wanda ya bi Ali, ma’ana ya gabatar da shi a kan waninsa wajen Khalifanci, koda kuwa bai yarda da Khalifancin sauran Imaman Ahlulbaiti ba; don haka Imamiyya, da Jarudiyya, da Zaidiyya da Isma’ilyya duk sun shiga ciki. Amma banda mulhidai daga cikin su, haka nan (ban da) Wakifiyya da Fadahiyya.

2- Sheikh al-Mufid ya fada a cikin littafinsa Musi’atul-Utbah cewa:

Shi’a su ne wadanda suke bin Ali, suke kuma gabatar da shi a kan (duk) Sahabban Manzon Allah (SAWA), suka kuma yi amanna da cewa shi ne Khalifa da wasici daga Ma’aiki ko da son Allah Madaukaki (sawa’un sun yi amanna da haka) bisa dogaro da nassi ne, kamar Imamiyya, ko da siffa, kamar Jarudiyya[9].

3- Shaharastani ya bayyana haka a cikin littafinsa al-Milalu wal-Nihalu cewa:

Shi’a su ne wadanda suka bi Ali, suka yarda da shugabancinsa da Khalifancinsa ta (dogaro da) nassi da wasiyya, ko dai a bayyane ko a boye; suka kuma yi amanna da cewa Khalifanci da ja-gorancin al’umma ba sa fita daga hannun ’ya`yansa; in kuwa har ya fita to hakan ya faru ne daga zaluntarsu da aka yi ko daga takiyya daga gare su.[10]

4- Nubkhati ya fada cikin littafisa Firak al-Shi’a cewa:

Shi’a su ne kungiyar Ali dan Abi Dalib, wadanda ake kira da suna Shi’ar Ali tun lokacin Annabi (SAWA) da duk wanda kaunarsa ta dace da kaunar Ali.

5- Muhammad Farid Wajdi ya fada a cikin littafinsa Da’iratul-Ma’arif cewa:

Shi’a su ne wadanda suka bi Ali cikin Imamancinsa, suka yi imani da cewa ja-gorancin al’umma ba ya fita daga hannun ’ya`yansa. Sun yarda da cewa Imamai ba sa kuskure (wato an kiyaye su) daga manyan zunubbai da kanana, sun kuma yarda da (wajibcin) mika wilaya (ga Ahlulbaiti) da (wajibcin) yin bara’a (daga makiyansu) a fada da aikace, sai dai cikin halin takiyya yayin da suka ji tsoron gallazawar wani azzalumi.

Wannan shi ne kadan daga bayanan malamai da marubuta tarihi dangane da ma’anar kalmar Shi’a. A takaice sun dace a kan siffanta Shi’a da cewa: Su ne wadanda ke gabatar da Imam Ali (AS) a kan sauran Sahabbai bisa dogaro da nassi a kan haka ko saboda wasu siffofi da ya kebanta da su, shi kuma suka fifita shi a kan waninsa.

Abu ne da ya ke sananne cewa kashin bayan Shi’anci shi ne tabbatacciyar yarda da Imamanci da Khalifancin Imam Ali (AS) da wasu kebabbu daga cikin ’ya`yansa tare da gabatar da su a kan wasun su bisa dogaro da nassi a kan haka. Wannan imani na haifar da yarda da wasu muhimman abubuwa kamar haka:

a) Cewa tunda Imamanci ya samo asali ne daga nassi, kuma tunda shi ci-gaban Annabci ne, to dole duk abin da Annabci ke bukata Imamanci ma na bukatarsa, kuma duk abin da aka samu wajen Annabi dole a same shi wajen Imami, wanda shi ke kan kujerar da Annabi ya bari, yake kuma ja-goranci a kan abin da Annabi ya yi; face wahayi wanda ya kebanta da Annabawa kawai.*

b) Cewa Khalifanci reshe ne na Imamanci. Wato tunda ya kasance Imami shi ne ja-goran addini, dole ya zama shugaban siyasa, wanda shi ne Khalifa.

c) Kasancewar Khalifanci shugabanci ne na siyasa kuma reshen Imamanci, to don haka Khalifanci ba ya kasancewa da zabe ko kur’a kamar yadda Annabci ba ya tabbata da hakan; maimakon haka Khalifanci na tabbata ne da wasici daga Annabi ko daga Imami din da ya gabata, wanda kowanne ya samo asali ne daga horon Allah Madaukaki, domin Annabi ba ya magana bisa son zuciya, haka al’amarin ya ke ga Imami kamar yadda zai bayyana nan gaba.

--------------------------------------------------------------------------------

[1] Fairuz Abadi, al-Kamus al-Muhit,, juz’i na 3, shafin na 47.

[2] Ibn al-Athir, al-Nihayah, juzi’ na shafin na

[3] Ibn Munzur, Lisanul-Arab, juz’i na 8, shafi na 188-189.

[4] Na Jauhari, juz’i na 3, shafi na 140

[5] Na Kayyumi, shafi na 329.

[6] Na al-Zabidi, juz’I na 5, shafi na 403.

[7] Kamar surar Maryam, aya ta 69

[8] Duba surorin: al-Hajari, aya ta 10; al-Kamari, aya ta 51 da al-Saba’i, aya ta 54.

[9] Sheikh al-Mufid, cikin littafisa Musi’atul-Utbah, safi na 19.

[10] Al-Milal Wal-Nihalu, sahfi na 102.

* Ya kamata a bambance tsakanin Wahayi da ‘Sadarwa Tsakanin Allah da Kebabbun bayinSa’. Na farkon ne ya kebanta da Annabawa kawai, amma na biyun bai kebanta da su kawai ba. Allah Madaukaki na da sadarwa ta masamman da wasu kebabbun bayinSa ta hanyoyi dabam-daban, irin Ilhama, da Karama, da Mu’inah da wasun wannan. Don haka duk lokacin da muka ce Imamanmu na da sadarwa ta masamman da Allah Madaukaki, wasu masu tsaurin fahimta na tsammanin wahayi muke nufi; alhali ba haka muke bufi ba.

Tarihin Kafuwar Shi'a:
________________________

a) Lokacin Bayyanar Shi’a

Mafi yawan marubuta tarihi (wadanda ba ’yan Shi’a ba) sukan dangana bayyanar Shi’a da zamanin da ya biyo bayan wafatin Annabi (SAWA); sai dai su kansu wadanda suka tafi a kan wannan ra’ayin sun sassaba a tsakaninsu wajen iyakance takamaimen lokacin kafuwar Shi’a din. Wasu daga cikin su sun tafi a kan cewa ta kafu ne a ranar Sakifa, wato ranar da wasu jama’a daga Sahabban Annabi (SAWA) suka gabatar da wanin Imam Ali wajen Khalifanci. Daga masu irin wannan ra’ayi akwai Ustaz Muhammad Abdullahi Anan, dan kasar Masar, kamar yadda ya nuna haka a cikin littafinsa al-Jam’iyyatus-Sirriyyah, inda ya ke cewa:

Babban kuskure ne a fadi cewa Shi’a sun fara bayyana ne yayin da Khwarijawa[1] suka balle, da cewa ana kiran su da wannan suna ne saboda sun saura a bangaren Ali. Gaskiyan al’amarin dai shi ne cewa Shi’ar Ali sun bayyana ne tun lokacin wafatin Annabi (SAWA)…..

Haka nan Ahmad Amin ya dace da wannan ra’ayi a cikin littafinsa Fajrul-Islam.

Wasu kuwa daga cikin marubuta tarihi cewa suka yi bayyanar Shi’a ya kasance ne a ranar kashe Khalifa na uku, Usman bin Affan. Ibin Hazam ya fada, a cikin littafinsa Al-Fisal, cewa:

Lallai Rafidhawa (yana nufin ’yan Shi’a) ba Musulmi ba ne (?) Wato dai wata kungiya ce wadda aka kirkira bayan rasuwar Annabi (SAWA) da kimanin shekaru ashirin da biyar…[2]

Idan aka kasafta shekaru ashirin da biyar daga wafatin Manzo (SAWA), da Ibin Hazam ke magana, za a ga Khalifancin Abubakar ya dauki shekara biyu da wata uku. Khalifancin Umar shekara goma sha biyu da wata shida, wannan ya yi daidai da shekaru goma sha hudu da watanni takwas kenan. Hada wadanan da shekaru goma sha takwas da wata goma na Khalifancin Usman zai ba mu shekaru talatin da biyu da wata shida kenan. Idan aka cire shekaru ashirin da biyar daga talatn da uku da wata shida, zai saura shekaru takwas da wata shida. Wato wannan ra’ayin na ganin cewa Shi’a ta bayyana kimanin shekaru takwas da karewar mulkin Usman bin Affan kenan.

Haka nan a cikin su akwai wadanda ke ganin cewa Shi’a ta kafu ne a ranar Yakin jamal a Basara, kamar yadda Ibin Nadim ya nuna, inda ya ce:

Yayin da Dalhat da Zubair suka sabawa Ali (RA), suka kangare a kan cewa suna neman ramuwar gayyar kashe Usman daga jininsa (Ali din), kuma shi ya daura damarar yakar su har sai sun dawo ga horon Allah Madaukaki; to duk wanda ya bi shi a kan haka shi ake kira da sunan Shi’a.[3]

b) Wanda Ya Kirikiri Shi’a

Banda wadannan maganganu, babban abin da yawa-yawan marubuta tarihi suka fi dogara a kai game da ainihin wanda ya kafa Shi’a shi ne cewa: wani Bayahude, wai shi Abdullahi bin Saba’, shi ne wanda ya fara kafa asasin Shi’a. Muhammad Rashid Ridha ya fada, a cikin littafinsa al-Sunna wal-Shi’a, cewa:

Shi’antar Khalifa na hudu, Ali bin Abi Dalib (RA), ya kasance shi ne mafarin rarrabar wannan al’umma ta Muhammadu a cikin addininta da siyasarta (?) Kuma farkon wanda ya fara kirkirar ta wani Bayahude ne wanda ake kira Abdullahi bin Saba’, wanda ya bayyana Musulunci don yaudara, ya yi kira zuwa wuce-gona-da-iri cikin al’amarin Ali don ya raba kan wannan al’umma ya kuma bata mata addininta da duniyarta.[4]

Ahmad Amin ya ambaci wani abu mai mahimmanci a kan Abdullahi bin Saba’, inda ya fadi cewa:

Ya kasance (wato Abdullahi bin Saba’) yana imani da cewa dukkan mutane an haife su daidai ne, don haka ya wajaba su rayu daidai, kuma abin da ya wajaba a sami daidaita a kansa a tsakanin su shi ne dukiya da mata, domin mafi yawan fadace-fadace suna faruwa ne saboda kudi da mata….

Har zuwa inda yake cewa:

…Mutane sun shiga bin mazahabarsa har bayan wannan lokacin….

Har ila yau ya ci gaba da cewa:-

…. Muna iya lura da kamantuwar akidar Abu Zarri (Sahabin Annabi) da ra’ayin Mazdak (wato akidar mai yada akidar Yahudancin) ta fuskar dukiya kawai (banda mata). Domin hakika Dabari ya ba mu labari cewa: Abu Zarri ya taba tashi a Sham ya ce: `Ya ku mawadata! Ku kiyaye kanku daga (hakkokin) talakawa. Kuma ka yi albishir ga wadanda ke boye zinari da azurfa kuma ba sa ciyar da su a tafarkin Allah da azaba mai radadi. A ranar da za a kona su a kanta (dukiyar) a cikin wutar jahannama…. Sai Mu’awuya ya aika da shi (Abu Zarri) zuwa wajen Usman bin Affan a Madina don kar ya bata mutanen Sham. Yayin da da Usman ya tambaye shi cewa: Me ya sa mutanen Sham ke karar cewa ka dame su? Sai ya ce: ‘Bai kamata mawadata su rika boye dukiya ba.

Daga nan dubi abin da Ahmad Amin ya ci gaba da fada da idon basira:

Daga wannan za ka gane cewa ra’ayin shi (wato Abu Zarri) ya yi kusa kwarai da ra’ayin Mazdak (na Yahudanci) a cikin abin da ya shafi dukiya. Amma abin tambaya a nan shi ne: Daga ina wannan ra’ayi ya zo gare shi? Dabari ne ke ba mu amsar wannan tambaya da cewa: Hakika wannan dan bakar mace (Abdullahi bin Saba’i) ya hadu da Abu Zarri sai ya rudar da shi da wannan akida, kuma wannan dan bakar mace ya je wajen Sahabi Abu Darda’i da Ubaidatu bin Samit, amma ba su saurare shi ba, a nan har Ubaidatu ya tafi da shi wajen Mu’awuya ya ce masa: Wallahi wannan ne ya hada ka da Abu Zarri.

A gain na, inda za a bi hanyar mita da damu da mafi yawan Ahlussunna ke bi a yau wajen zargin Shi’a da zagin Sahabbai, da wannan zance na Ahmad Amin ya zama mafi girman misalign zagin Sahabbai. Wannan zai hafar da yarda da cewa mafi girman nau’in zagin Sahabbai yana littafin Ahlussuna ne.

c) Shin Daga Ina Ibin Saba’ Din Nan Ya Fito Ne?

Kan wannan ne Ahmad Amin ya fadi cewa:

Kuma mun san cewa shi wannan dan bakar mace, wanda ake kira da Abdullahi bin Saba’, ya kasance Byahude ne daga San’a, ya bayyana Musulunci lokacin Khalifancin Usman, kuma ya yi kokarin batawa Musulmi addininsu, ya watsa akidu masu cutarwa a cikin garuruwa da dama a Hijaz, Basra, Kufa, Sham da Masar. Wata kila (?) ya dauko wannan akida ta Shi’a ne daga Mazdakawan (wato Yahudawan) Iraki ko Yaman, sai shi kuma Abu Zarri ya karba da kyakkyawar niyya…

Wadannan su ne maganganunsu a kan tarihin kafuwar Shi’a, da kan Abullahi bin Saba’. Amma shin wadannan maganganu gaskiya ne?

d) Gaskiyar Al’amarin

A gaskiya duk wanda ya iya juriya wajen gabatar da bincike na lura da basira a kan inda masu wadancan maganganu suka dogara, zai fahimci cewa duk al’amarin na su surkulle ne kawai da ba shi da wani tushe. Ta wata fuska kuma, duk wanda ke da ’yar tsinkaya a kan hadisan Annabi (SAWA) zai yi misa sauki ya gane rashin gaskiyar wadancan maganganu. Har ila yau da mutum zai lura da maganganun nasu –su kansu- dangane Abdullahi bin Saba’ da cewa shi ne ya kirkiri Shi’a, da mutum zai gano sabani da karyata-juna cikin zantukansu.

Misali, Muhammad Rashid Ridha, wanda muka fara dauko maganarsa game da kafuwar Shi’a, ya nuna madogarar da ya dogara da ita a kan kissar Abdullahi bin Saba’ da cewa shi ya dogara ne da abin da Ibin Athir ya fitar cikin tarihinsa. Koma cikin littafin nasa ka same shi yana cewa:

Duk wanda ya duba labarin yakin Jamal cikin tarihin Ibin Athir, zai ga iyakar kokarin Saba’iyawa (wato Abdullahi bin Saba’ da mabiyansa) wajen bata tsakanin mutane lokacin kokarin sulhu; ka duba juz’i na 3, shafi na 95, 96 da 103.[5]

Wannan magana ta Rashid tana nuna cewa babban madogarar da ya dogara da ita a kan tarihin da ya bayar na Abdullahi bin Saba’ da kafuwar Shi’a, shi ne littafin al-Kamil na Ibin Athir.

Abul-Fida’i ma ya fitar da wannan kissa gaba dayan ta a cikin littafinsa, al-Mukhtasar fi akhbaril-bashar, bayan ya kammala, shi ma sai ya nuna cewa ya dogara ne da abin da Ibin Athir ya fitar, sai ya ce:

Na zabe shi ne (wato wannan tarihi) na kuma takaita shi ne daga littafin al-Kamil, Tarihin Sheikh Izzuddin, wanda aka fi sani da Ibin Athir al-Jazri….[6]

Idan kuma muka koma cikin tarihin Ibin Athir din –kamar yadda wadancan suka koma- zamu same shi ya ambaci wannan kissa gaba dayan ta a babin abubuwan da suka faru a shekara ta talatin zuwa talatin da shida bayan hijira; amma shi bai fito baro-baro ya bayyana abin da ya dogara da shi a kan wannan kissa ba, sai dai ya ambata a gabatarwar littafin nasa cewa:

Lallai ni cikin wannan littafi nawa na hada abubuwan da ba a hada a wani littafi ba. Duk wanda ya lura zai fahimci ingancin hakan, don na fara ne da littafin Tarikh al-Kabir wanda Imami Abu Ja’afar al-Dabari ya wallafa, don shi ne littafin da duk ake dogara da shi (?) kuma gare shi (duk marubuta tarihi) ke komawa yayin sabani; sai na dauki dukkan bayanansa ban bar bayanin wani mutum ba a cikinsa….

Kenan har da Ibin Saba’. Sai ya ci gaba da cewa:-

Yayin da na gama da shi, sai na dauko waninsa na daga –littafan- tarihi mashaurai, sai na duba su na hada da abin da na dauko daga tarihin Dabari wanda baya cikinsa, sai dai abin da ya shafi Sahabban Annabi (SAWA), shi ban kara wani abu daga abin da na dauko daga Abu Ja’afar (Dabari) ba (?) in ban da abin da ya kunshi karin bayani ko sunan wani mutum ko abin da babu sukan wani daga cikin su (Sahabban) cikin dauko shi. Na kuma dogara ne da shi (tarihin na Dabari) maimakon waninsa na daga littafan tarihi domin shi (wato Dabari) Imami ne mai bin diddigin gaskiya, wanda ya tara ilimi da kyawun kuduri….[7]

Wannan ita ce maganar Ibn Athir, wannan da Ustaz Muhammad Rashid Ridha da Abul-Fida’i suka dogara da shi cikin tarihin da suka rubuta cikin littafansu game da labarin Abdullahi bin Saba’ da kafuwar Shi’a. Ga shi nan, kamar yadda yake bayyane, yana nuna cewa shi ma ya dogara ne da Dabari kan wannan kissa (da wasun ta).

Shi ma Ibn Kathir, bayan ya fitar da wannan kissa a cikin littafinsa, kamar yadda aka bayyana a baya, sai ya nuna inda ya dogara da cewa:

Wannan shi ne abin da Abu ja’afar bin Jarir (Dabari) ya fada a takaice.[8]

Ibin Khaldun ma ya fitar da wannan kissa a cikin littafinsa al-Mubtada wal-Khabar, inada daga baya ya ambaci madogararsa a kanta da cewa:

Wannan shi ne takaitaccen bayanin abin da ya fito daga littafin Abu Ja’afar Dabari, mun dogara da shi ne don yardar mu da shi….[9]

Muhammad Farid wajdi ma ya fitar da ita dai wannan kissa a cikin littafinsa[10], sananna ya bayyana cewa shima ya ciro ta ne daga tarihin Dabari.

A takaice dai kusan dukkan marubuta tarihi wadanda suka fitar da tarihin Abdullahi bin Saba’, Bayahuden San’a; da kuma cewa shi ne wanda ya kafa tubalin farko na ginin Shi’anci a lokacin Khalifancin Usman bin Affan, ko dai sun dauko wannan tarihi ne daga Dabari ko sun dauko daga wajen wanda ya dauko daga wajensa ya kuma dogara da abin da ya dauko dari bisa dari; babu wata hanya sai wannan. Kenan Dabari shi ne muryar farko na wannan kissa.

Duk dai inda aka kai aka komo, wadannan maganganu na Dabari suna nuna abubuwa biyu ne na asasi da ake son mu yarda:

a) Cewa bayyanar Shi’a dai a hannun wani Bayahuden San’ ta kasar Yaman ya kasance. Wanda shi kuma Bayahudem ya bayyana Musulunci don yaudara, ya kuma krikire ta ne don raba kan Musulmi* da bata musu addininsu da siyarsasu.

b) Cewa kirikrar Shi’a ya kasance ne bayan rasuwar Annabi (SAWA) da kimanin shekaru ashirin da biyar, wato karshe karshen Khalifancin Khalifa na uku Usman bin Affan.

Amma idan muka koma tafsirin shi Dabari din –wanda shi ne tushen waccan kissa- za mu same shi yana fassara ayar nan ta cikin surar Bayyinat mai cewa:

Lallai wadanda suka yi imani suka kuma aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafi alherin halitta.

Da cewa:

An karbo daga Abul-Jarud, daga Muhammad dan Ali cewa Manzon Allah (SAWA) ya fada (dangane da fadar Allah mai cewa): “….wadannan su ne mafi alherin halitta” cewa: “Ya Ali! Su ne kai da ’yan Shi’arka.”[11]

Wannan riwaya da Dabari ya fitar cikin tafsirinsa ta karyata labarin da ya bayar –da kansa- dangane da bayyanar Shi’a a lokacin Khalifancin Usman bin Affan; domin riwayarsa ta tafsiri na nuna cewa Manzon Allah ne da kansa ya fara sanya asasin ginin Shi’antar Imam Ali (AS).

Idan muka lura da wadannan riwayoyi biyu masu karyata juna na Dabari, za mu ga cewa riwayar karshen (wadda ke tabbatar da cewa Annabi ne ya fara dasa wanna akida a cikin zukatan Musulmi) ta fi karfi, kuma ita ce gaskiya. Domin kamar yadda muka tabbatar, dukkan wadanda suka rubuta tarihin Ibn Saba’ da cewa Shi’a ta bayyana ne a lokacin Khalifancin Usman bin Affan, (duk) sun dogara ne da riwayar Dabari. Shi kuma Dabari da me ya dogara kan wannan kissa ta sa? A cikin littafin tarihinsa na Tarikh al-Umam Wal-Muluk, isnadin wannan kissa duk ya fito ne ta hanyar wani wai shi Saif bin Umar al-Taimimi, bai kuma riwaito wannan riwaya ta wata hanya daban ba face ta hanyar da ta kare da wannan mutum.

e) Matsayin Riwayoyin Saif Wajen Manazarta

Masu bin diddigi daga Malaman hadisi da masana halayyar masu riwaya, don gane inganci da rashin ingancin hadisi, sun yi nazari kuma sun fadi ra’ayoyinsu a kan riwayoyin Saif bin Umar; kuma da yawa daga cikin wadannan masu bin diddigi sun bayyana rashin ingancin riwayoyin Saif. Daga cikin wadannan akwai:

1- Nasa’i: Ya fadi cewa: “Saif ba amintacce ba ne, don haka hadisansa abin bari ne don rauninsu.”

2- Abu Dauda: Ya ce: “Shi (Saif) ba komai ba ne, makaryaci ne”.

3- Ibin Abi Hatim: Ya ce: “A bar hadisansa (Saif).”

4- Ibin أdi: Ya ce: “(Saif mutum ne) rarrauna, duk da cewa wasu hadisansa mashahurai ne (sai dai) dukkan su ba abin yarda ba ne.”

5- Ibin Haban: Ya ce: “Ya kan riwaito hadisan karya, an kuma tuhume shi da zindikanci.”

6- Ibin Abdu Barr: ya fada, bayan ya fitar da wani hadisin Saif, cewa: “Saif abin gudu ne, mun dai ambaci wannan hadisin shi ne don a san shi.”

7- Hakim al-Naishaburi: Ya ce: “A kiyaye shi (wato Saif), domin an tuhumce shi da zindikanci.”

8- Ibin Hajar: Ya fada, bayan ya ambaci wata riwaya wadda Saif ke cikin jerin isnadinsa (wato wadanda suka riwaito ta) cewa: “A cikin su (masu riwayar) akwai masu rauni, wanda duk ya fi su rauni shi ne Saif.”

Wannan shi ne Saif bin Umar, wanda shi ne tushen kissar Abdullahi bin Saba’ a wajen Dabari, sauran marubuta tarihi kuma suka yada wannan kissa daga shi Dabari din. Ga abin da masu bin diddigin a kan masu riwaya nan suka fada a kansa, ya kuma rage wa hankali ya yi hukunci!!

Amma riwayar Dabari ta biyu, wadda ta zo cikin tafsirinsa, wadda kuma ambatonta ya gabata, a hakika ita ce gaskiya; saboda banda Dabari, wasu masu tafsirai sun fitar da ita ta hanyoyi dabam daban. Daga cikin su akwai:

1-Suyudi: cikin tafsirinsa, inda ya ce:

Ibin Asakir ya fitar daga Jabir bin Abdullahi ya ce: Mun kasance a wajen Annabin Allah (SAWA) sai Ali ya fuskanto inda mu ke, sai Annabi (SAWA) ya ce: ‘Na rantse da wanda raina ke hannunSa, cewa wannan (ya na nufin Ali) da ’yan Shi’arsa su ne masu babban rabo ranar kiyama.’ Sai ayar (Surar Bayyinat aya ta 7-8) ta sauka. Daga nan Sahabban Annabi suka kasance duk lokacin da Ali ya fuskance su sukan ce: Mafi alherin halitta ya zo.[12]

2-Ibin Hajar al-Haithani: cikin littafinsa Sawa’ikul-Muhrikah *, ya ce:

Aya ta goma sha biyar (cikin jerin ayoyin da ke nuna darajojin Ali) ita ce fadar Allah (SWT) mai cewa: ‘Lallai wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafi alherin halitta’ Hafiz Jalaluddin al-Zarandi ya fitar daga Ibn Abbas cewa: Yayin da wannan aya ta sauka, Annabi (SAWA) ya cewa Ali dan Abi Dalibi: ‘(mafi alherin halittu) su ne kai da ’yan Shi’ar ka. Za ka zo kai da ‘yan Shi’ar ka ranar kiyama alhali kuna masu yarda (da abin da za ku gani) kuma wadanda aka yarda da ku, kuma makiyin ka zai zo alhali ana fushi da shi kuma wulakantacce’. Sai Imam Ali (AS) ya ce: Wanene kuma makiyi na? Sai Annabi (SAWA) ya ce: `Wanda ya yi maka bara’a kuma ya la’ance ka.[13]

Wannan shi ne dan takaitaccen bayani a kan riwayar da ke nuna tarihin kafuwar Shi’a, kuma shi ne gaskiya; domin yadda riwayoyin suka bayyana ta hanyoyi dabam daban da bakunan masu riwaya dabam daban, wanda hakan ke nuna gaskiyar fitowarsa daga Annabi (SAWA) kamar yadda masana ilimin hadisi suka tabbatar a muhallinsa.

Amma riwayar farko da ke nuna cewa Abdullahi bin Saba’ ne ya kirkiro Shi’anci a lokacin Khalifancin Usman bin Affan bayan raunin isnadinta, kamar yadda muka tabbatar, tana kuma cikin jerin gwanon hadisan da ake wa lakabi da ‘Hadisan Ahad’*, domin tushen riwayarsa na komawa ne ga Saif bin Umar shi kadai kamar yadda bayani ya gabata.

Wani abin lura a nan shi ne, wasu malaman tarihi biyu ma sun dauko wannan kissa daga Saif kai tsaye. Amma mun kawar da kai daga ambaton haka daga gare su saboda Ahalussunna ba su cika dogara da su a fanning tarihi kamar Dabari ba. Wadannan kuwa su ne Ibin Asakir da Zahabi.

f) Abdullahi bin Saba’: Halittar Tarihi

Amma bincike a kan Abdullahi bin Saba’ ya tabbatar da cewa: Shi dai wani mutum ne da aka kirkire shi aka cusa cikin tunane tunanen mutane, alhali kuwa Allah bai halicci wani taliki irin wannan ba kwata-kwata.

A matsayin mabudin bincike ga mai karatu, za mu iya ambaton abin da mashahurin marubucin nan dan kasar Masar, Dokta Daha Husaini, ya rubuta game da wannan “Gizo” na tarihi, yayin da ya ke bayani a kan yakin Seffin, ya ce:

Mafi karancin abin da kawar da kan malaman tarihi ke nunuwa a kan Saba’iyanci da “dan bakar mace” a yakin Seffin, shi ne cewa al’amarin Saba’iyanci da (Abdullahi bin Saba’) “dan bakar mace” ba komai ba ne face takarkarewa na magudi; an kirkire shi ne daga baya, a sakamakon gardamar dake tsakanin ’yan Shi’a da wasunsu na daga kungiyoyin Musulmi. Sai masu hamayya da Shi’a suka so shigar da wani sanadari na Yahudanci cikin akidun Shi’a don yi musu makirci da munanta su.[14]

Dalilin Dokta Daha Husaini a akan cewa Abdullahi bin Saba’ kirkirarre ne, shi ne cewa:

Da al’amarin “dan bakar mace” ya dogara da wani asasi na gaskiya da ingantaccen tarihi, da a dabi’ance al’amarinsa da makircinsa sun bayyana a lokacin wannan yaki na Seffin mai tattare da tarnaki da rikice-rikice; kuma da a dabi’ance zai bayyana a lokacin da magoya bayan Ali suka sassaba a kan al’amarin hukunci (wat lokacin sulhun Seffin); kuma da masamman ya bayyana a lokacin samuwar sabuwar kungiyar nan (ta Khawarijawa), wadda ta ki sulhu, ta guje masa, ta kuma kafirta duk wanda ya karkata zuwa gare shi ko ya yi tarayya a cikinsa. Amma ba mu ga ambaton “dan bakar mace” a al’amarin Khawarijawa ba. Yaya za a iya kafa dalilin wannan kawar da kai? Ko yaya za a kafa dalilin fakuwar Ibin Saba’ a rikicin Seffin da samuwar kungiyar Khawarijawa?[15]

Daga nan Sai Dokta Daha Husaini ya bayyana ra’ayinsa a kan wannan al’amari da cewa:

Amma ni, na ba wadannan al’amura biyu dalili daya ne kawai, shi ne cewa “dan bakar mace” dai bai kasance ba face rudu. In ma har an yi shi a aikace, to ba shi da matsayin da masu tarihi ke surantawa, da irin yadda suke nuna kai-kawonsa a lokacin Khalifancin Usman da shekarar farko ta Khalifancin Ali. Shi dai wani mutum ne da masu fada da Shi’a suka tanada don Shi’a kawai; ba su tanade shi don Khawarijawa ba.[16]

Don samun cikakken bayani da karin hujjoji a kan tatsuniyar Abdulahi bin Saba’, ana iya komawa littafin nan mai suna Abdullahi bin Saba’, wallafar Shehun malami Sayyid Murtala al-Askari, da littafin Mi’atu Wa Khamsun Sahabiyyil-Mukhtalak, na wannan mawallafi, wanda a cikinsa mawallafin ya kasafto wadansu kirkirarrun Sahabbai dari da hamsin da aka sanya musu sunaye kuma aka kirkiri hadisai aka dangana musu, alhali Allah bai halicce su ba kuma ManzonSa bai san su ba. Wannan ya tabbata bisa hujjoji karfafa da kwararan dalilai wadanda sun ishi duk mai son gaskiya ya san inda aka dosa.

[1] Khawarijawa wasu jama’a ne da suka balle daga rundunar Imam Ali (AS) a lokacin yakin Seffin. Imam ya yake su a yakin Naharwan, kuma daga nan ya hana a yake su, saboda a cewarsa: Wanda ya nemi gaskiya ya kuskure mata baya daidai da wanda ya nemi barna kuma ya same ta.

[2] Ibin Hazam, al-Fisal Fit-tarikh, juz’i na 2, shafi na 75.

[3] Ibin Nadim, al- Fihras, shafi na 249.

[4] Ustaz Rashid Ridha, al-Sunna wal-Shi’a, shafi na 4-5.

[5] Ustaz Rashid Ridha, al-Sunna wal-Shi’a, shafi na 6.

[6] Abul-Fada’i, al-Mukhtasar Fi Akhabaril-Bashar.

[7] Ibin Athir, al-Kamil Fit-Tarikh.

[8] Ibin Kasir, al-Bidayatu wal-Nihayatu, na 7, shafi na 246.

[9] Ibin Khaldun, al-Mubtada’ Wal-Khabar, juz’i na 2, shafi na 425.

[10] Muhammad Farid Wajdi, Da’iratul Ma’arif, juz’i na 7, shafi na 160, 167 da 169.

* Ban sani ba sauran rarrabe-rarraben Musulmi kuma wane Bayahuden ne ya kirkira? kuma ta hanyar kirikrar wace mazahabar? Ina nufin wadannan raebe-rabe da Ahlussunna suka yi zuwa Mazhabobin Furu’a da na akida masu yawa!

[11] Dabari, Ibin Jarir, Tafsirul-Kur’an, juz’i na 30, shafi na 171wajen fassarar wannan aya.

[12] Suyudi, Durrul-mansur Fil-tafsiri bil-Ma’asur, wajen fassarar surar Bayyinat aya ta 7-8.

* Wannan littafi mawallafinsa ya sanya shi ne da nufin ‘yin kaca-kaca’ da shi’anci; ya yi amfani da lafuzza na zage zage da karairayi kamar yadda masu irin wannan aiki suka saba. Sai dai duk da haka ya tabbatar da duk wani dalili da Shi’a ke tabbatarwa game da akidunsu, da darajojin Ahlulbaiti (AS).

[13] Ibin Hajar al-al-Makki, Sawa’kul-Murikati Lir-raddi ala ahlil bida’I wal-Zanikati, shafi na 182

* Hadisin Ahad shi ne duk hadisin da `yan tsiraru suka riwaito shi, sawa’un mutum daya ne ya riwaito shi ko fiye da daya, matukar yawan su bai kai haddin da aka iyakance wa tawatiri ba. To balle kuma wannan riwaya ta Saif da ta takaita da mutum daya. An yi nazarin irin wannan hadisi a fannonin ilimin hadisi da na Usulul-Fikih, inda aka tabbatar da cewa irin wannan hadisi ba hujja ba ne a kashin kan shi, sai idan an sami wani dalili na shari’a da ke mayar da shi hujja. Don haka yardajjen abu ne kan cewa hadisin Ahad ba ya iya tabbatar da akida. Sai a lura da kyau.

[14] Dokta Daha Husaini, al-Fitnatul-Kubrah, shafi na 98.

[15] al-Fitnatul-Kubrah, shafi na 99.

[16] al-Fitnatul-Kubrah, shafi na 99.

'Yan Shi'a Daga Sahabbai:
________________________

Tunda ya tabbata cewa Annabi (SAWA) ne, da kansa, ya dasa tushen asasin Shi’anci kamar yadda bincike ya tabbatar, a dabi’ance zai zama kenan Annabi ya ci gaba yiwa wannan akida ban-ruwa yana karfafa a cikin zukatan Musulmi, masamman Sahabbansa (RA). Wannan shi ne abin da littafinmu na Ahlul-Baiti cikin Alku’ani da Sunna ya kunsa; wato bayani game da yadda Annabi (SAWA) ya yi ta yada akidar Shi’antar Ali (AS) da goma sha daya daga jikokinsa ta bangaren Imam Husaini (AS); da cusa wannan akida a cikin zukatan Musulmi tun farkon bayyanar da’awarsa (a ranar tsawatar da dangi[1]) har da’awarasa ta karshe a kan hanyarsa ta dawowa daga hajjin ban-kwana (a Ghadir), a yayin da ya kara tabbatar da wannan akida a matakin karshe na rayuwarsa. Annabi bai bar duniya ba sai da ya tabbatar da cewa an yi wa Imam Ali (AS) bai’a a gaban idonsa. Haka nan ya bar duniya da sanin wasu kebabbu daga cikin Sahabbansa masu Shi’antar Ali, har ma ana musu lakabi da Shi’ar Ali.

Wadanda suka shahara da Shi’ntar Imam Ali (AS) daga Sahabbai kuma har ake musu lakabi da ’yan Shi’arsa, sun hada da:

1- Salman al-Farisi.

2- Abu Zar al-Gaffari.

3- Mikdad bin Aswad al-Ansi.

4- Ammar bin Yasir.

5- Huzaimatu Zul-Shahadatain.

6- Huzaifatu al-Yamani.

7- Zubair bin Awam.

8- Fadhal bin Abbas.

9- Abdullahi bin Abbas.

10- Hashim bin Ukbatul-Markal.

11- Abu Ayub al-Ansari.

12- Aban bin Sa’ad bin al-As.

13- Khalid bin Sa’ad bin al-As.

14- Ubayyu bin Ka’ab (shugaban masu kira’a).

15- Anas bin Haris.

16- Usman bin Ahnaf.

17- Sahal bin Hanif.

18- Abu Sa’id al-Khudri.

19- Kais bin Sa’ad bin Ubadata.

20- Barra’a bin Malik.

21- Rufa’atu bin Abi Hlata.

22- Bilal bin Rabah al-Habashi.

Da wasun wadannan. Mai son cikakken bayani akan wadanda aka san su da Shi’anci daga Sahabbai, sai ya koma manyan littaffan da suka yi cikakken bayani a kan haka, irin su A’ayanus-Shi’a na Sayyid Muhsin al-Amin; da littafin Darajatur-Rafi’ah Fi Dabakatis-Shi’ah na Sayyid Ali Khan.

Haka wasu littafan Rijal (sanin masu riwayar hadisi) na Ahlussunna, irin su Mizan al-I’itidai, sun tabbatar da Shi’anci wasu Sahabbai, a yayin da suke bin diddigin masu riyawaya daga cukinsu, sai a koma can a duba.

Sa’annan kadan daga cikin maganganun da Ma’iki (SAWA) ya yi ta nanatawa don tabbatar da wanann akida a cikin zukata sun hada da:

ط Matsayin Ali a wuri na kamar matsayin Haruna ne a wurin Musa, illa kawai babu Annabi a baya na[2].

ط Ya kai Ali! Lallai ba bu mai son ka sai Mumini kuma babu mai kin ka sai munafuki[3].

ط Hakika gobe zan bayar da tutar ga wani mutum da ke son Allah da ManzonSa kuma Allah da ManzonSa ke son sa[4] (da aka wayi gari sai ya bayar da ita ga Imam Ali (AS) alhali mashahuran Sahabbai irin Umar dan Khaddabi (RA) sun kwana suna fatan a ba su).

ط Lallai ni mai barin nauyaye biyu ne a cikin ku, Littafin Allah da kebabbun iyalaina (Ahlulbaiti)[5].

ط Ali na tare da gaskiya kuma gaskiya na tare da Ali, tana binsa duk inda ya bi[6].

ط (Annabi ya cewa Dalhat): Da zaka ga duk mutane sun bi wani kwari alhali Ali ya bin wani kwari daban, ka bi inda Ali ya bi[7].

Da sauran irin wadannan masu yawa wadanda ke bayani karara game da yadda Annabi ya bi hanyoyi dabam daban don dasawa da karfafa akidar Shi’antar Ali.

Kamar yadda duk wani mai idon basira ke iya fahimta, wannan ya wuce bayanin falaloli da darajojin Imam Ali (AS), domin kuwa a hadisai da dama da ake riwaitowa (na gaskiya da na karya daga cikin su) game da falolin Sahabbai, duk basa zuwa da irin wadannan sigogi da lafuzza, don haka ne ma Imam Ahmad bin Hambali ya fitar da cewa:

A duk cikin Sahabbai babu wanda riwayoyin darajojinsa suka zo ta hanyar karfafan isnadai irin Ali dan Abi Talib.[8]

[1] Al’amarin kira da tsawatar da makusanta shi ne ke dunkule cikin ayar tsawatarwa mai cewa: و أنذر عشيرتك الأقربيين"” (wato: Kuma ka tsawatar da danginka makusanta).

[2] Sahih al-Bukhari.

[3] Nasa’i, Khsa’isu Amirul-Mu’uminin.

[4] Sahih al-Bukhari.

[5] Sahih Muslim.

[6] Nasa’i, Khasa’isu Amirul-Mu’uminin.

[7] Hakim, al-Mustadrik.

[8] Suyudi, Abdul-Rahman, Tarkh al-Khulafa’i, babin darajojin Ali.

Shi'a Bayan Rasuwar Annabi (s.a.w.a):
________________________

Sheikh Muhammad Hussain Kashiful-Gita’i ya yaye mana shamaki (kamar yadda sunansa ke nunawa) a cikin littafinsa Aslus-Shi’a Wa Usuliha, inda ya bayyana abin da ya biyo bayan wafatin Annabi (SAWA) da cewa:-

“Lokacin da Manzon Allah (SAWA) ya bar wannan gida (na duniya), ya koma zuwa wancan (na lahira), sai wasu jama’a daga Sahabbai suka ga cewa Imam Ali (AS) bai dace da zama ja-goran al’umma (Khalifa) ba, ko dai saboda yarantarsa (kamar yadda wadansu ke gani), ko saboda kasancewar Kuraishawa sun ki haduwar Annabci da Khalifanci ga Banu Hashim (Kamar yadda Umar dan Khattabi ya fada yayin da Abbas ya kebe da shi daga baya, ya tambaye shi dalilin da ya sa aka hana Imam Ali Khalifancin Ma’aiki tare da samuwan nassosi a kan haka); ko don wani al’amari daban wanda ba kansa muke magana ba. Abin da dukkan bangarori biyun –na Shi’a da Ahlul-Sunna- suka dace a kai ne cewa Imam Ali (AS) ya ki yarda ya yi mubaya’a da farko. Kai! a cikin Sahihul-Bukhari, a babin yakin Khaibara –an bayyana cewa- bai yi mubaya’a ba sai bayan watanni shida; haka wasu jama’a daga manyan Sahabbai irin su Zubair, da Ammar, da Mikdad da wasun su sun bi shi a kan haka. Amma yayin da ya ga cewa sabawarsa za ta haifar da wata mummunar baraka ga Musulunci da wani karaya da ba ya doruwa…”

Har zuwa inda ya ce:

“Kuma yayin da ya ga cewa Khalifofi biyun farko –Abubakar da Umar- suna baki kokarin su wajen yada kalmar tauhidi da hada sojoji don bude garuruwa, sai ya yarda ya yi mubaya’a, ya amince da yarjejeniyar zama lafiya, ya kawar da kai daga abin da ya san hakkinsa ne; ba don komai ba sai don kiyaye Musulunci daga barazanar wargajewar hadin kan (mutanen) shi da rarrabuwar kalma; da haka kuwa sai mutane su koma jahiliyyar farko. ‘Yan Shi’arsa kuma suka bi shi a kan haka, suka haskaka da haskensa. To a wannan lokacin –akidar- Shi’anci ba ta da hanyar yaduwa, domin Musulunci ya kasance yana gudana a kan daidaitacciyar hanya[1]”.

A nan Shehin Malamin ya bayyana mana dalilan da suka sa yunkurin Shi’anci ya raunana a lokacin Khalifancin Khalifofi biyun farko (Abubakar da Umar). Kamar yadda ya ke bayyane, dalilan na komawa ne kan wasu al’amurra kamar haka:

1-Rashin tsanantan Canje-canje: domin kamar yadda aka sani, bayan wafatin Manzo (SAWA) Abubakar ya zama Khalifa (ta hanyar da Kashiful-Gita’i ya bayyana) har na tsawon shekaru biyu da watanni uku. A duk tsawon wannan lokaci asasin shugabanci ya kasance yana gudana kamar yadda ya kamata, kuma kasancewar ba a nisanta daga zamanin Manzon Allah (SAWA) ba, ba a manta da karantarwar Musulunci da ya bari ba. Lokacin da ciwon ajali ya kama shi ya yi wasici da Umar dan Khaddabi a matsayin Khalifa na biyu. Umar ya shugabanci Musulmi har na tsawon shekaru goma da watanni shida. A duk wannan tsawon lokacin, duk da an sami ’yan sauye sauyen da ba a rasa ba a Shari’a; kamar: (a) Haramta auren mutu’a da ya kasance halastacce a lokacin Annabi da lokacin Abubakar, (b) cire kalmar (حيُّ على خير العمل) daga kiran sallah, wanda shima ya kasance tabbace a lokacin Annabi (s.a.w.a)da Abubakar. Da shigar da (الصلاة خير من النوم) a kiran sallar asuba, wanda ba a kasance ana yi ba a lokacin Annabi da lokacin Abubakar; (c) shar’anta sallar tarawihi (asham), wadda babu ita a lokacin Annabi da Abubakar; (d) sanya saki uku a lokaci daya ya haramta mace ga mijinta har sai ta yi wani auren kuma ya mutu, alhali kuwa a lokacin Annabi da Abubakar babu saki uku tashi daya, sakin dake wajibta mace sai ta yi wani aure kafin ta koma dakin mijinta shi ne saki tashi uku ana yi ana dawowa; da sauran irin wadannan wadanda Sayyaid Sharfuddin al-Musawi ya kawo su a cikin littafinsa al-Nassu Wal-Ijtihad; sai dai duk da samuwar irin wadannan sauye-sauye, amma ba a sami matsaloli da yawa ta fuskar shugabanci ba; kuma waccan matsala ma Imam Ali (AS) ya iya ya rage kaifin ta da sanya mata takunkumi.

2-Khalifofin biyu sun kasance suna karbar gyara daga Imam Ali (AS). Har ma an riwaito Umar na cewa: “Ba don Ali ba da Umar ya halaka.”

3-Komawar su ga Imam Ali cikin al’amurra da dama. A wancan lokacin sun kasance suna komawa gare shi cikin duk wani al’amari da ya rikice musu; wannan kuwa domin shi aka tanada don aikin fassarar addini da bayyana shi ga mutane yadda ya ke a bayan Annabi. Sanin kowa ne cewa samu cikakken nasarar wannan aiki na bukatar ya zama akalar mulkin jama’a na hannunsa. Ta daya bangaren kuma, idan har wanda ba a tanada da irin nauyin Imam Ali ba ya iya karbar akalar mulkin Musulmi, dole ya sami babbar matsala a irin wancan yanayin. Domin idan aka kira mutum da wannan suna na Khalifan Annabi, to mutane na tsammanin su sami irin abin da suke samu a wajen Annabi daga wurinsa; wannan kuwa shi ne wanin Ali daga Sahabbai ba ya da shi; hakan ya tilasta musu komawa gare shi.

Abul-Aswad al-Du’ali yana kafa dalili a kan Imamancin Ali (AS) da cewa “Dalilin dake nuna cewa shi ne Imamin kowa, shi ne bukatuwar kowa zuwa gare shi, da wadatuwarsa daga kowa.”

Misali an riwaito cewa a lokacin Khalifancin Umar, wasu samari biyu sun taba zuwa wajen wata tsohuwa suka ba ta wasu kididdigaggun kudade ta ajiye musu bisa sharadin kar ta ba kowa sai su biyu tare kamar yadda suka bata su biyu tare. Bayan wani lokaci sai dayan su ya zo mata yana kuka, ya fada mata cewa Allah ya yi wa dan’uwansa rasuwa, daga nan ya yi mata wayo ya karbi kudi ya yi tafiyarsa. Bayan wani lokaci kuma sai ga dayan da aka ce ya mutu, ya zo yana neman kudi a wajen wannan tsohuwa. Al’amari fa ya girmama har ya kai su ga Khalifa, bayan kowa ya fadawa Khalifa matsalarsa sai al’amarin ya fi karfin tunaninsa da iyawarsa; don haka sai ya aikawa Imam Ali (AS) da al’amarin; da ya ji bayanin kowa sai ya ce: “Wane sharadi kuka dace a kai kafin ku ba ta ajiyar kudinku?” Sai saurayin ya ce: Bisa sharadin kar taba dayan mu ba tare da daya ba, amma ga shi nan ta ba shi. Sai Imam ya ce: “To ai wannan mai sauki ne, tafi ka zo da dan’uwanka don ku karbi kudinku tare kamar yadda kuka shardanta.” Daga nan Imam Ali (AS) ya magance wannan mastala

Irin wannan ya faru da yawa a lokacin khalifancin Abubakar da Umar, wanda har hakan ya sa Umar na addu’a da cewa: “Allah kar ka jarabce ni da wani rikitaccen hukunci har sai Abul-Hasan (Ali) na tare da ni[2].” Don samun karin bayani a kan irin wadannan ana iya komawa littafin al-Haka’ik, na Sheikh Habib أli Ibrah.

4-Bude garuruwa: A lokacin wadannan Khalifofi biyu an bude garuruwa da dama, an kuma sami kabilu da suka shiga Musulunci; ta yadda duk wani yunkuri da Imam Ali (AS) zai yi yana iya haifar da cikas ta fuskar ci-gaban bude-buden da ake samu da bakin da suke shiga Musulunci.

5-Manufar kare hadin kai: Wanda shi ne mafi mahimmaci daga abubuwan da suka dakatar da bunkasar yaduwar Shi’anci a lokacin Khalifofi biyun farko. Gaskiya ne cewa Imam Ali (AS) na sane da cewa Khalifanci hakkinsa ne da Manzon Allah (SAWA) ya dora shi a kai, yana kuma iya karba da karfi in ya so –saboda ba a cin Ali da yaki- amma duk da haka ya kame daga hakan saboda gujewa barakar da haka ka iya haifarwa a tsakanin Musulmi. A lura da cewa a wannan lokacin kafiran waje na da tsarin cewa bayan wafatin Annabi za su iya yi wa Musulunci wani aibi; munafukai daga cikin Musulmi sun yi bakam suna jiran wata dama; ga kuma wadanda dama tilasta musu shiga Musulunci aka yi bayan bude Makka irin su Abu Sufyan. Domin tarihi ya hakaito cewa yayin da Abu Sufyan ya ga Imam Ali da ’yan Shi’arsa sun ki yin mubaya’a ga Abubakar, sai ya lababo ya zo ya sami Imam yana nuna masa yiwuwar yakar Khalifa da nuna shirinsa na taimakawa a kan haka. Amma da ya ke Imam ya san kudurinsa sai ya amsa masa cewa: “Kama kanka! Ka dade kana nufin Musulunci da sharri.”

Wadannan su ne dalilan da manzarta suka gano cewa su suka tilastawa Imam Ali (AS) yin hakuri a kan abin da ya ke ganin hakkinsa ne. Shi da kansa ya dunkule wadannan dalilai cikin hudubarsa ta Shakshakiyya, inda ya ce:

“Sai na kame hannuna har sai da na ga inda mutane suka dosa, sun kauce daga Musulunci. Ana kiran su zuwa danne addinin Muhammadu (SAWA). Sai na ji tsoron in har ban taimaki Musulunci da mutanensa ba, zan ga baraka ko gibi a cikin shi, (wanda) musifar haka a kaina za ta fi tsanani fiye da kufcewar shugabancin ku, wanda bai kasance ba face jin dadin kwanaki kadan, abin da ya kasance daga gare shi zai wuce kamar rairayi, ko kamar yadda girgije ke yayewa. Don haka sai na yunkura a cikin wadannan rikice-rikice, har sai da barna ta kau, addini ya natsu ya zauna da gindinsa[3]”.

Wannan shi ne al’amarin Shi’anci a lokacin khalifancin Abubakar da Umar (RA). Amma al’amarin ba haka ya kasance a lokacin khalifancin Usman bin Affan ba. Allama Tabataba’i ya takaita mana yadda Khalifancin Usman ya kasance a cikin fadarsa:

“Bayan wani saurayi Bafarise ya kashe Khalifa na biyu, an tabbatar da khalifancin Khalifa na uku bisa dogara da ra’ayin ma’abuta Shura wadanda adadinsu ya kai shida, wanda kuma ya tabbata ne bisa tsarin da Khalifa na biyu ya tsara, sai –shi Khalifa na uku- ya tabbatarwa da danginsa na daga Umayyawa shugabancin rassa. Ya nada su gwamnoni a Hijaz, da Iraki, da Masar da sauran garuruwan Musulmi. Ga su sun kasance azzaluman gaske cikin hukunce hukuncensu, an san su da shashanci, da zalunci, da fasikanci da ja’ircinsu. Sun gurbata dokokin Musulunci wadanda suka kasance suna gudana. Wannan ya sa kararrakin jama’a suka yawaita a ofishin Khalifa, amma shi Khlaifa na uku ya kasance ’yan’uwantaka na yi misa tasiri masamman a kan Marwanu bin Hakam; don haka bai ba wadannan kararraki mahimmanci ba, a wasu lokuta ma ya kan hukunta wadanda suka kawo kararrakin. A karshe sai mutane suka yi misa bore a shekara ta 25 bayan hijra; bayan kewaye gidansa da tsananin tashin hankali sai suka kashe shi[4]”.

Wannan shi ne takaitaccen bayanin yadda Khalifa na uku ya zama Khalifa da yadda ya gina mulkinsa da irin tashin hankalin da siyasarsa ta haifar masa, wadda a karshe ta sa ya rasa ransa. To a wannan lokacin, a dabi’ance, dole Shi’anci ya bunkasa, domin kuwa a lokacin mafi yawan Musulmi sun gujewa Khalifa na uku saboda yadda ya saba alkawarin da ya dauka na yin aiki da Littafin Allah da sunnar Manzo da tafarkin Abubakar da Umar*. A nan sai zukatan mutane suka raja’a ga Imam Ali (AS), daga lokacin ne ma wasu suka fadaka da cewa ai tun farko ma Imam Ali ne ya kamata ya zama Khalifa bisa nassi da cancanta.

Bayyanar Mu’awuya Dan Abu Sufyanu

Bayan an kashe Khalifa na uku, Musulmi sun dunfari Imam Ali (AS), suka yo misa ca a kan su yi mubaya’a gare shi. Imam ya kau da kai daga gare su ya ce: “Ku nemi wani na” don ya cika hujja a kan su, yayin da suka nace misa sai ya gindaya musu sharuddan cewa duk wanda ya amince ya yi misa bai’a a masalaci kowa na gani, suka amince da haka, suka yi masa mubaya’a ta wannan fuska. Da haka ya zama Khalifa (AS).

Sai dai hukumarsa ta fuskanci nau’o’in matsalolin siyasa masu yawa, wadanda da daya daga cikin wadanda suka gabace shi ya fuskanta da ba inda zai kai. Matsalar da ta fi kowacce ita ce matsalar Mu’awuya dan Abu Sufyan. Ya kasance gwamna a Sham a karkashin Umar, wanda ya kasance yana kaunarsa kwarai. Da Usman ya zo sai ya tabbatar da shi a kan wannan. Labarin mutuwar Usman da zaben Imam Ali (AS) na isa gare shi sai ya tayar da fitinarsa*, ya bayyana kiyayya a fili ga Imam, ya yake shi da iyaka karfinsa, ya tilasta wa Imam Ali (AS) yunkurawa don kariyar kai da kare addini; a sakamakon haka aka yi hasarar rayuka da dama a cikin Musulmi, Musulmi suka rabu kashi biyu; bangaren farko karkashin ja-gorancin Imam Ali, daya bangaren karkashin ja-gorancin Mu’awuya, a karshen yakin Seffin (yayin da suka ga alamar Imam zai kawar da su), sai aka yi wata kumbiya-kumbiya da aka kira da ‘sulhu’, aka cutar da Imam Ali (AS) a wannan wurin; to a lokacin ne aka sami wasu masu gajeren hange suka dauka cewa an sami hadin kai kenan da wannan yaudara, har suka kira wannan shekara da عام الجماعة (wato shekarar hadin kai), kuma masu irin wannan fahimta aka yi musu suna da Ahlus-sunnati wal-Jama’ah. To wannan shi ne ya kara bunkasa shi’antar Imam Ali (AS), ya kara kafa tushen da Annabi (SAWA) ya yi tun farko sai Shi’a ta shahara daga lokacin. Kai! Idan mutum ya yarda da cewa dama wannan yanayi Manzo (SAWA) ya hangowa Imam Ali (AS) kuma don wadannan matsaloli ne Manzo ya fadi irin abubuwan da ya fada a kansa, don su samawa Ali (AS) magoya baya, da mutum bai yi kuskure ba. Don ba don wadannan maganganu na Manzo ba, ba shakka da Ali ya saura shi kadai a wadannan yakoki. Kuma wadannan zantuka na Manzo (SAWA) ne suka sa hatta Ahlussunna suka ba Ali gaskiya a yakinsa da rundunar Dalhat, da Zubair, da A’isha da ta Mu’awuya, balle kuma yakar Khawarijawa da ya yi.

Sakamako

Daga abin da ya gabata, za a fahimci cewa: ta kowace fuska aka kalli tarihin bayyanar Shi’a za a ga cewa kafin wani ya amsa sunan Ahlus-sunna, wasu sun riga sun amsa sunan Shi’a tuni.

Haka daga bayanan da suka gabata, muna iya hangen cewa babban abin da ya kara bunkasa Shi’a a bayan Annabi (SAWA) shi ne wahalhalu da kuntatawa da suka raka rayuwar kebabbun jikokin Annabi (SAWA) da duk wanda ya bi su a kan shiriyar da suke kai, daga makiyansu na daga mahassada, da makiya addinin kakansu da kuma jahilai, wadanda ake amfani da kwakwalensu. Alhali kuwa su ne Imamai masu shiryarwa wadanda kaunarsu (wadda ke jone da wajabcin bin su) wajibi ne daga cikin wajiban addini, kamar yadda Imam Shafi’i, Shugaban mazahabar Shafi’iyya, ya fada a cikin wasu baitocin wake na shi da suka shahara:-

يا أهل بيت رسول الله حبّكمُ فرضٌ من الله في القرآن أنزلهُ

كفاكمُ من عظيم الشأن أنّكمُ منْ لم يصلِّ عليكم لا صلاة لهُ

Ma’ana:

Ya Ahlin gidan Manzon Allah kaunarku

Farali ne da Allah Ya saukar cikin AlKur’ani

Ya ishe ku babbar daraja cewa lallai ku

Duk wanda bai yi muku salati ba ba shi da sallah

Da wannan za mu iya shiga tarihinsu yanzu don mu ga abin da ya sa suka cancanci irin wannan matsayi daga Allah madaukaki.

[1] Kashiful-Gida’i, Asalus-Shi’a Wa Usuliha, shafi na 114-115.

[2] Abdur-Rahman Suyudi, Tarikh al-Khulafa’I, babin darajojin Ali

[3] Nahjul-Balagha, tsarin Subhi Saleh, shafi na 451.

[4] Allama Muhammad Hussaini Tabata’i, al-Shi’atu Fil-Islam, shafi na 26.

* Wadanan su ne Sharuddan da aka tanada ga duk wanda zai zama Khalifa na uku, Umar bin Khaddab ne ya tsara wannan kafin ya bar duniya, kuma ya dora Abdurrahman bin Auf ya aiwatar. Da farko Abdurrahman ya fara tuntubar Imam Ali (AS) ne da wadanna sharudda, Imam ya amsa masa da cewa aiki da Littafin Allah da Sunnar Manzo wannan ba wani abin tantama ba ne, amma bin tafarkin Abubakar da Umar ba karbabbe ba ne a wurinsa saboda ba wani dalili a kan haka.

* Wasu hikayoyin tarihi sun bayyana cewa a lokacin da aka kewaye gidan Usman, kafin a kashe shi ya aikawa Mu’awuya yana neman taimakonsa, kuma Mu’awuya ya jinkirta aikawa da sojoji, ko ya aika amma ya hore su da dakatawa a wani wuri a wajen gari, da cewa kar su shiga sai bayan sun tabbatar an kashe Khalifa. Haka kuwa abin ya faru.

Takaitaccen Tarihin Shugabannin Shi'a

’Yan Shi’a sun dogara ne, cikin samuwarsu da ci-gaba da wanzuwarsu, da Ma’asumai goma sha hudu na wannan al’umma; wato Manzon Allah (SAWA), da ’yarsa Fadima (AS), da dan baffansa kuma surukinsa Imam Ali (AS), da jikokinsa Hasan da Husaini (AS) da wasu tara daga jikokinsa ta bangaren Imam Husaini (AS). Don bayar da haske a kan majinginar ’yan Shi’a a duk fannonin karantarwar Musulunci, za mu dan yi sassarfa cikin tarihin wadannan kebabbun bayi na Allah zababbu kamar haka:

1-MUHAMMADU MANZON ALLAH (SAWA)

2-IMAM ALI BIN ABI TALIB (AS)

3-FATIMA ‘YAR MANZON ALLAH (AS)

4-IMAM HASAN BIN ALI (AS)

- Muhammadu Manzon Allah (s.a.w.a):
________________________

An ambaci wannan suna (Muhammad) mai albarka sau hudu a cikin Alkur’ani mai girma. Sannan an ambace shi da wasu sunaye da siffofi irin su Daha, da Yasin, da Nuun, da al-Muzammil, da al-Mudathir, da al-Bashir, da an-Nazeer da wasun wadannan.

Danganensa

Shi ne Abul-Kasimi, Muhammadu dan Abdullahi, dan Abdul-Mudallibi, dan Shaibatul-Hamd, dan Hashim, dan Abudu Manaf, dan Kusayyu, dan Kilab, dan Murrata, dan Ka’ab, dan Lu’ayyu, dan Galib, dan Fihir, dan Malik, dan Nadhar, dan Khazimata, dan Madrakatu, dan Ilyas, dan Madhar, dan Nazar, dan Ma’ad, dan Adnan. Wannan shi ne gwargwadon inda aka dace a kan nasabarsa ta wajen mahaifi, abin da ya wuce wannan haddi kuwa ana da sabani a kai; illa dai tabbas ne cewa nasabar Adnan na karewa ne da Annabi Isma’il dan Annabi Ibrahim (AS). Har ma riwaya ta zo (ta hanyoyinmu) cewa shi (SAWA) ya ce: “Idan danganena ya kare da Adnan ku kame.”[1]

Mahaifyarsa kuwa ita ce: Aminatu ‘yar Saidi Bani Zuhrah (wanda shi ne) Wahbu dan Abdu-manaf, dan Zaharata, dan Kilab, wanda aka ambata cikin cikin jerin kakanninsa wadanda kuma suka kare da Annabi Ibrahim (AS). Kenan mahaifiyarsa ta hada dangi da mahaifinsa ta wajen kakansu Kilab dan Marrata.

Haihuwarsa (SAWA)

Akwai sabani tsakanin Musulmi game da ranar haihuwar Annabi (SAWA), wasu sun tafi a kan cewa ranar 17 ga watan Rabi’ul-Awwal ne (wannan shi ne abin da ya shahara ta riwayoyin Ahlulbaiti (AS)). Yayin da wasu duka tafi a kan cewa ranar 12 ne ga wannan wata na Rabi’ul-Awwal (wannan shi ne abin da ya shahara ta riwayoyin Ahlussunna).[2] Ko ta halin kaka dai, an haife shi (SAWA) bayan alfijirin wata rana daga cikin watan na Rabi’ul-Awwal, kuma an hafe shi maraya, a sasan da ake kira da Shi’ibu Abi Dalib dake wani gida da aka fi sani da Gidan Muhammad dan Yusuf dake garin Makka (Wahabiyawa sun rushe wannan gida a halin yanzu).

Abin da ya shahara a tarihi shi ne cewa bayan haihuwarsa da dan lokaci kadan sai aka bayar da shi shayarwa! Kai wasu riwayoyi ma sun nuna cewa mahaifiyarsa ba ta shayar da shi ba sai na kwanaki biyu ko uku kawai!! Daga nan sai Suwaiba, kuyangar Abu Lahabi, ta shayar da shi[3]; daga nan kuma sai wata mata mai daraja da ake kira da Halimatus-Sa’adiyya ta zo birnin Makka tare da wasu abokan tafiyarta don neman jariran da za su shayar don samun abin kalaci da haka. Da cewa Halimah da farko ba ta karbe shi ba da ta ji cewa maraya ne, amma da ba ta sami waninsa ba sai ta dawo ta amshe shi, da wannan ta ga alhairai da albarkatu masu yawa.

Wannan shi ne takaitaccen abin da ya shahara game da shayar da shi (SAWA), abin da babu littafin tarhin Annabi da ke rasa shi, sawa’un na Ahlussunna ne ko na Shi’a. Sai dai wasu malaman mu sun yi raddi a kan wasu sassa na wannan bangare, kamar yadda Aribeli ya yi bayani[4]; kai! wasu daga masu bin diddigi ma sun yi inkarin kissar shayarwar daga tushenta, kamar yadda malami mai bin diddigi, Sayyid Ja’afar Murtala al-Amili ya yi cikakken bayani[5]

Bayan ya cika shekaru shida da haihuwa ne mahaifiyarsa Amina ta dauke shi zuwa Madina don su ziyarci kabarin mahaifinsa. Suna dawowa sai ciwon ajali ya kamata a hanya, sai ta rasu a wani wuri da ake kira da suna al-Abwa’. Annabi ya yi matukar bakin ciki da rabuwa da mahaifiyarsa, ya kuma yi kuka mai tsananin gaske.

Bayan rasuwar mahaifiyarsa sai kakansa Abdul Mudallabi ya dauki nauyin rike shi. Abdul Mudallabi ya kasance kamilin dattijo, wanda ya siffantu da dukkan siffofin madalla, wannan ya sa shi ya cancanci shugabanci, don haka ya kasance shugaban Kuraishawa. Ya kasance yana bin addinin kakansa Annabi Ibrahim (AS) tare da daukacin iyalansa.

Bayan Annabi (SAWA) ya cika shekaru takwas da haihuwa sai Allah Ya yiwa kakansa Abdul Mudallabi rasuwa. Daga nan sai baffansa Abu Dalib ya dauki dawainiyar rikonsa bisa horon mahaifinsa Abdul Mudallabi. Yayin da ya kai munzilin koyon sana’a sai ya shiga koya masa kasuwanci.

Bayan ya cika shekaru ashirin da biyar da haihuwa, sai Allah Ya hada shi da wata kamilar mace, wadda Allah Ya hada mata kyawayan dabi’u da dukiya, ana kiranta da suna Khadijah bint Khuwailid. Irin yadda labarin gaskiya da rikon amanar Annabi (SAWA) ya yadu a ko’ina ne ya kai har kunnenta. Sai ta bukaci da su hada gwiwar yin kasuwanci tare. Annabi kuwa ya yarda, bayan dan lokaci kadan sai wannan hulda ta yi albarka, a karshe ta haifar da yin aurensu, a lokacin yana da shekaru ashirin da biyar, ita kuma tana da shekaru ashirin da bakwai*

Hakika wannan aure ya kasance abin koyi ta fuskokin da yawa, inda a cikinsa matar da mijin suka kasance sassa biyu masu karfafa juna da taimakekeniya; kauna da tausayin juna suka kasance tubalin da rayuwarsa ta ginu a kai. Wannan ya sa Annabi (SAWA) bai yi tunanin auren wata mace a tare da ita ba, duk da tayin da aka yi ta yi gare shi kuwa. Wane aure zai yi tunanin yi kuwa alhali yana da mace irin Khadijah? Wadda ta riga ta toshe kowace kafa da kywawan halayenta da imaninta.

Bayan kimanin shekaru ashirin da hudu da yin aurensa da Khadijah, sai Allah Ya yi mata rasuwa bayan ta sadukar da dukkan dukiyarta a kan hanyar Allah.

Abin da ya shahara shi ne cewa Khadija ta rasu ta bar ’ya’ya Shida, amma nazari na tabbatar da sabanin haka, inda tabbacin ’ya’ya biyar ya inganta, sauran kuwa suna nan a fagen kila-wa-kala.*

Halayen Annabi Kafin Aiko Shi

An shaidi Annabi (SAWA) da adalci, da gaskiya, da rikon amana, da kwazo, da rashin kasala, da tsari a rayuwa, da iya gudanar da abubuwa, da saukin kai da sauran wadannan; ta yadda ba shi da abokin kwatantawa a wadannan dabi’u. Wannan ya sa duk mutanen Makka na sauraronsa, suna komawa gare shi cikin sabaninsu, kuma suna amincewa da duk abin da ya hukunta ba tare da jayayya ba. Kamar yadda suka kasance suna bayar da ajiyar kadarori da dukiyoyinsu a hannunsa.

Ya Zama Annabi

Bayan ya cika shekaru arba’in da haihuwa sai Allah Ya yi masa wahayin farko. Wannan ne ya sanar da abin da aka dade ana ganin alamu daga gare shi, wato cewa Allah Ya zabe shi a matsayin AnnabinSa na karshe zuwa ga duniya baki daya. Saukan wahayin farko gare shi ya kasance ne a ranar 27 ga watan Rajab mai alfarma. ’Yan Shi’a na matukar girmama wannan rana, inda suka sanya ta cikin jerin manyan ranakun da suke rayawa da murna don nuna godiya ga Allah Madaukaki.

A lokacin saukar wahayin farko Imam Ali na wajen. Yana ganin Annabi a lokacin da ya ke karbar wahayi; kuma shi ne farkon wanda ya fara ba da gaskiya da sakon Musulunci a maza, Khadijah kuma a mata; wannan wata daraja ce da Allah Ya kebance su da ita, ba wata kumbiya-kumbiyar tarihi da neman kutso da wasu wannan sahun da zai iya canza ta!

Duniya gaba dayanta ta kasance cikin wani yanayi na duhun jahilci da wata irin rayuwa ta dabbanci, da rashin kan-gado, rayuwar da ba ta kunshi komai ba sai jahilci, da fadace-fadace, da sakarci; mai karfi na danne mai rauni; tatsar jinin juna, da sabawa ingantaccen tafarkin rayuwa suka zama rowan-dare. Wannan ne ma ya sa akewa wannan zamani lakabi da zamanin Jahiliyya.* Tsibirin Larabawa ba a cewa komai a wannan lokacin! domin duhun jahilci ya kai su da har suna bautawa gumakan da suka sassaka da hannuwansu. Su na cin mushe, su sha giya su yi ta hauka. Da kan gaji matar ubansa idan ya mutu, koda kuwa uwarsa ce. Kamar sauran kabilun duniya, ba sa ba mace wata kima; kai! na su jahilcin ma har ya kai su ga suna bisne ’ya’ya mata da ransu bisa wani dalili da ya fi ta’asar ban haushi.

A wannan hali ne duniya da tsibirin Larabawa suka kasance har Allah ya aiko da Annabi (SAWA) a matsayin haske da rahama ga duniya baki daya. Sai dai babban abin takaicin da suka aikata shi ne irin adawa da suka nuna ga sakon Musulunci da matsanancin cutar da Manzo (SAWA) da suka yi. Bai tambaye su wani lada kan abin yake kiran su akai ba. Bai dora musu wani nauyi ba, illa kawai su bar wadancan miyagun dabi’u dake harde rayuwarsu da hana su ci-gaba. Hakika Kuraishawa sun cutar da Manzo (SAWA) matuka; in banda baffansa Abu Dalib da ya kasance yana ba shi kariya.

Zuwa Isra’i

Bayan shekaru takwas da aiko shi ne Allah Ya yi Isr’ai da shi, wato tafiyar nan ta dare daya daga Makka zuwa Kudus, daga can kuma zuwa Sama, inda ya shaida ayoyin Allah masu yawan gaske. Wannan Isra’i ya kasance da ruhi da jikin Annabi, kuma yana farke ba cikin barci ba, kuma yana sane ba rafkane ba. Daga Kudus din ne ma aka ba shi wannan sallar da mu ke yi a halin yanzu. Nassosin tarihi sun ce daga lokacin ne aka fara kiran wannan wajen da Masallacin Kudus.*

Shekarar Bakin-Ciki

Bayan shekaru goma da aiko shi kofar matsaloli ta kara budewa ga Annabi da sauran Musulmi ’yan tsiraru a lokacin; yayin da Khadijah bint Khuwailid ta rasu kenan. Kwanaki uku kacal da wannan sai Abu Dalib ma ya rasu. Habawa! Ai Mushrikai sai suka daura sabon damara da yaki da Musulumci da Manzo (SAWA).

Manzo ya yi matukar bakin ciki da rasuwar wadannan gwarazan Musulunci biyu, wanda wannan ya sa ya sawa wannan shekara suna Shekarar Bakin-ciki. Na farko dai duk sun kasance sassan rayuwarsa, kuma sassa masu tasiri cikin aikinsa na isar da Sakon Allah. Rasuwarsu na nufin cewa Musulunci ya shiga wani sabon mayuyacin yanayi kenan[6].

Abu Dalib ya rasu yana mai imani da Annabi (SAWA), har ma ya sha wasu wahalhalu saboda musuluntarsa; sabanini abin da wasu marubta tarihi ke kokarin nunawa na cewa bai musulunta ba.

Hijira Zuwa Habasha
Ganin shiga tsananin da sabuwar al’ummar Musulmi ta yi daga bangare mushrikan Makka bayan rasuwar Abu Dalib, ya sa Annabi ya hori wasu Musulmi da yin hijra zuwa Habasha garin sarki Najjashi, wanda ba a zaluntar wani a gabansa.* Wannan hijra ta kasance karkashin ja-gorancin Ja’afar dan Abu Dalib.
Duk da kokarin da Mushrikan Makka suka yi na kokarin shiga tsakanin sarki Najjashi da Musulmi, amma abin ya ci tura; domin bayan sarkin ya yi musu tambayoyi, kuma Ja’afar ya ba shi amsa a kan abin da ya hada su da mutanensu, da irin abin da sakonsu ya kunsa, sai ya amince ya ba su mafaka, kuma ya kori wakilan da kafiran Kuraishawa suka turo da kyautar da suka kawowa sarki don kwadaitar da shi a kan kin karbar Musulmi. Sai suka koma suna wulakantattu masu hasara. Najjashi dai ya sanar da Musuluncinsa daga baya, shi da mutanen kasarsa gaba daya.
Hijra Zuwa Madina

Bayan cika sheru goma sha uku da aiko shi sai ya yi hijra zuwa Yathrib bisa horon Allah; saboda wani shiri da mutanen Makka suka shirya na kashe shi. Allah Ya tserar da shi ta hanyar sadaukar da kai da Imam Ali (AS) ya yi, ya kwana a kan gadonsa don dauke hankalin wadanda ke labe suna jiran duhu ya shiga don aiwatar da mummunan nufinsu. Sai Manzo (SAWA) ya fita ba tare da sun gan shi ba, ya kama hanyar Madina shi da Abokinsa Abubakar da wani yaronsa dake yi musu hidima a hanya. Bayan dawainiya da wahalhalu masu yawa sai Allah Ya sa suka isa wani wuri da ake kira Kubah dake ’yan mila-milai kadan daga Yathrib, a nan Manzo ya yi zango ya jira har sai da Imam Ali (AS) ya iso tare da Fatima mahaifiyarsa, da Fatima ’yar Manzon Allah, da wasu Musulmi marasa karfi. Daga nan suka dunguma suka shiga Madina baki daya. Al’ummar Yathrib, wadanda suka cimma yarjejeniya da Annabi tun tuni kan cewa ya yi hijra zuwa gare su, sun yi matukar maraba da zuwan Annabi (SAWA).

Hijira zuwa Yathrib, wadda saboda hijrar Annabi aka canza mata suna zuwa Madinatun-Nabi, ta bude wani shafi mai mahimmanci a tarihinmu na Musulunci; domin a nan ne Manzo (SAWA) ya kafa gwamnatin Musulunci ta farko da zata nunuwa duniya irin karfin da Musulunci ke da shi wajen iya tafiyar da rayuwar mutane. Ikon da Musulunci ke da shi ta fuskokin siyasa, da tattalin arziki, da tsarin zamantakewa, da diplomasiyya da aikin soji sun bayyana a shekaru goma da Manzon Allah (SAWA) ya yi a rayuwar Madina; wadanda ke kunshe da yakoki, da yarjeniyoyi, da shari’anta hukunce hukuncen dukiya, da haddodi, da kisasi, da tsarin tsaron kasa da sauran su.

Wani abu mai mahimmanci da ba zai kufce mana ba a nan shi ne cewa: Wannan bangare na tarihin Musulunci na kunshe da abubuwa masu ban sha’awa da kowane Musulmi ke alfahari da su. Musulmi sun nuna bajinta matuka da sadaukar da kai. Musulmin Makka (Muhajirun) sun baro dukiyoyinsu, da danginsu, da kasarsu da sana’o’insu; ba don komai ba sai don su tsira da addininsu. Su kuma mutanen Madina (Ansar) sun nuna dattaku da halin ya kamata, yayin da suka karbi baki masu yawa ba tare da nuna kyashi ba, suka raba dukiyoyinsu da gidajensu tare, wasu suka saki matansu masu kyawawan halaye don bakinsu su aura su sami kwanciyar hankail da natsuwa a sabon yanayin da suka sami kansu a ciki. Kai! babu wata al’umma a tarihi da ta taba gabatar da irin wannan bajinta; kuma babu wani shugaba da iya sana’anta al’umma mai irin wannan hali in ba Muhammadu dan Abdullahi ba. Allah Ya saka masa da alheri, Ya kuma kara masa tsira da aminci. AlKur’ani, a cikin wasu ayoyinsa, ya yabi wannan bajinta yadda ya kamata, don wannan ya zama jinjinawa daga gare shi da kwadaitarwa ga masu zuwa da dabi’antuwa da irin wannan dabi’a.

Malaman Shi’a na yabon wannan bajinta ta Muhajirun da Ansar, suna tinkaho da ita a duk lokacin da suke bayani a wannan fagen, suna kwadaitar da mutane da yin koyi da haka. Kai! A aikace ma yau babu masu dabi’antuwa da wannan dabi’a kamar su; ga su nan saboda takura musu da ake yi a kasashensu suna hijra zuwa inda duk za su sami sassauci, kuma ’yan’uwansu na wadancan garuruwa na kwatanta abin da Ansar din farko suka yi. Wannan wata karyatawa ce ga abin da wasu suka takarkare suna yadawa, na cewa ’yan Shi’a ba su da aiki sai zagin Sahabbai, magana a kan haka na zuwa a mahallinsa in Allah Ya yarda.

Mu’ujizozin Annabi

Mu’ujiza wata tagazawa ce daga Allah Madaukaki ga bayinSa, don su sami saukin fahimtar gaskiyar Annabi su bi shi. Ba kwalliya ba ce ga Annabi kamar yadda wasu ke dauka, rashin ta a kowane lokaci kuma ba gazawa ba ne, kamar yadda wasu limaman Kirista ke nunawa.

Mu’ujiza ita ce duk abin da zai bayyana a hannun wani Annabi a lokacin da ya yi ikrarin Annabta. Dole ta fi karfin tunani mutane da iyawarsu, tana da ban mamaki kuma ba mai iya zuwa da irin ta. Tana bayyana ne kawai a wasu lokuta da ake bukatar bayyanar ta wajen tabbatar da wani abu ga wasu ko kore wata barna da aka jarabci wasu da ita. Mu’ujizar kowane Annabi na dacewa da abin da ya shahara a zamaninsa ne a galibi.

To Annabinmu Muhammadu ma ba abar shi a baya ba a wannan, yana da Mu’ujizozin da suka ma ketare na Annabawan da suka gabace shi. Wasu daga Mu’ujizozinsa sun hada da:

1. AlKur’ani: Mu’ujizancin AlKur’ani ya wuce Mu’ujizar kowane Annabi. Da wata maganar muna iya cewa, babu Annabin da ya zo da Mu’ujizar da ta kama hanyar AlKur’ani. Mu’ujizar AlKur’ani ta hadu ne a jerin ayoyinsa, zabin kalmomi da haruffansa da irin tarin ma’anoninsa. Shi ba waka ko wake ba, amma in ana karanta shi yana ratsa jiki fiye da yadda duk wata waka ke ratsa jikin mai son ta. Shi ba rubuntun zube ba ne, amma baya ginsarwa kamar sauran littaffai. Tun saukarsa ya kalubalanci masu ja da shi da su zo da koda sura daya karama [kamar surar Tawhid ko Takwir] amma suka kasa. Dalilin kashin su kuwa shi ne yadda suka koma suka zabi yakarsa da takobi maimakon harshe, alhali a da can –kafin zuwansa- sun kasance masu takama da hikima da iya tsara magana. Har yau kuma Musulmi na nan a kan wannan kalubale, suna cewa: ‘Idan akwai wanda ya iya kawo mana irin AlKur’ani muna shirye mu bar addninmu.’ Amma muna sane da cewa babu wanda zai iya haka, in kuma mutum zai kwatanta ga fili nan ga mai doki.

2. Saukin Haihuwa: Mahaifiyar Manzo (SAWA) bata sha wahala wajen daukar cikinsa da haihuwarsa ba. Ta kuma haife shi ita kadai, kuma cikin saukin da ba a saba ganin irinsa ba.

3. Lokacin haihuwarsa an shaida wani haske da ya rika fitowa daga dakin.

4. Ana haihuwarsa katangun fadar Kisra (sarkin babban daular Roma mai karfi) ta wargaje; alhali a da sun kasance masu karfin da ba a suranta abin da zai iya rushe su cikin sauki.

5. Tun yana karaminsa girgije ke masa inuwa a wasu lokutan tsananin rana, yana kuma binsa duk inda ya tafi.

6. Ya kasance yana gani ta baya kamar yadda ya ke gani ta gaba.

7. Ya kasance yana ji idan yana barci kamar yadda ya ke ji idan yana farke.

8. Ya kasance yana magana da dabbobi da harshen su.

9. Akwai hatimi (stamp) na cikan Annabci a kafadarsa, wanda aka rubuta kalmar Shahada a kai.

10. A kan ji tasbihin tsakuwa daga tafin hannusa.[7]

11. Ruwa na bubbbugowa daga tsakanin ’yan yatsun hannunsa.

12. Ya bayar da labaran abubuwa kafin su faru, kuma sun zo ba tare da sabani da yadda ya fada ba.

Wannan kadan kenan daga Mu’ujizozinsa (SAWA) wadanda wasu malamai sun kididdigo har 4,440.[8]

Sai dai ya zama dole a nan mu yi ishara da wata ‘yar fadakarwa mai mahimmancin gaske dandagane da mu’ujizar Annabawa (AS). Ya kamata a lura da cewa Annabawa ba su dogara da mu’ujiza a koda yaushe. Ba sa aiki da ita sai a lokutan da bukatar haka ta taso. Bikatuwar haka kan tashi ne kuwa yayin da da’awarsu ke fuskantar barazanar kawo rudu ga gama-garin mutane daga masu kawo rudani. Da wani zance muna iya cewa: irin nau’in mutanen da Annabawa (AS) kan fuskanta yayin kiransu nau’i biyu ne; akwai wadanda hujjoji da dalilai kan wadace su a ko wane irin yanayi, irin wadannan na iya zama su yi nazari da amfani da hankulansu a duk lokacin da aka so wasa da hankulansu ko jefa su cikin rudani. Sai kuma wadanda suke sabanin wadancan, su saboda tsaurin tunaninsu, suna iya fadawa cikin rudu cikin sauki, don haka suna bukatar tantancewa ko “gani-da-ido” na kowane abu. To Annabawa na gabatarwa kowane bangare da abin da zai taimaka masa wajen fahimta da gane sakon Allah Madaukaki, wannan kuwa cikan tausayin Allah ne.

Wani abu karkashin wannan kuma shi ne al’amarin masu neman kawo cikas wajen isar da sakon Annabawa ta hanyar yin amfani da sihiri ko wata harkalla da dabaru, a irin nan ma Annabawa na amfani da mu’ujiza don tonawa irin wadancan asiri, da kunyata su da nuna karyarsu kowa ya gani.

Matan Annabi (SAWA)

Annabi ya auri matan da adadinsu ya kai tara ko goma sha uku (a wasu riwayoyin). Mafificiyarsu ita ce Khadijah al-Kubra, uwar dukkan ’ya’yansa in banda Ibrahim, wanda Mariya ta Haifa. Babu wanda Allah Ya halattawa auren wannan adadin na mata sai shi. An halatta masa ne kuwa saboda wadansu maslahohi da amfaninsu ke komawa ga Musulunci; sabanin yadda masu sukar Musulunci ke kokarin nunawa na zargin son mata da sauran surkullensu.

Hakika malamai daga dukkan bangarorin Musulmi na Shi’a da Ahlussunna sun yi kyawawan bayanai game da wannan mas’ala, sun kuma yi rubuce-rubuce da harsuna dabam daban a kan wannan. Allah Ya saka musu da alheri.

’Yan Shi’a na mutunta matan Annabi (SAWA) saboda darajar zama da shi. Suna kara girmamawa ga wadanda suka dake, kuma suka ci-gaba a kan abin da Annabi ya dora su a kai na taribiyya da kamun kai, a lokacin rayuwrsa da bayan rasuwarsa. Sai dai ba sa ganin zama matar Annabi na nufin kariya daga laifi ko aminta daga kaucewa hanya da bata.

’Ya’yan Annabi (SAWA)

Bin diddigin tarihi na tabbatar da cewa Annabi na da ’ya’ya biyar kamar haka:

1. Kasim: A kan kira shi da Tahir. Shi ne babban dansa kuma ya rasu arayuwar Makkah. Da shi akewa Annabi lakabi da Abul-Kasim. Khadijah ce ta haife shi.

2. Abdullahi: Shi ma ya rasu a rayuwar Makka, Khadijah ce ta haife shi.

3. Ibrahim: An haife shi a Madina, bayan hijra, ya rasu yana karami, mahaifiyarsa ita ce Mariya al-Kibdiyyah.

4. Zainab: An haife ta a rayuwar Makka, kuma ta rasu tana karama a rayuwar Makka din dai. Khadiha ce ta haife ta.

5. Fatima: An haife ta a rayuwar Makka. Ita Allah ya zaba don yada tsatson Annabi. Khadijah ce ta haife ta.

Amma an riwaito cewa ’ya’ya bakwai ke gare shi da karin: Rukayya da Ummu Kulthum. Sai dai wannan ba tabbatacce ba ne ta fuskar nazarin tarihi da kyau.[9]

Rasuwar Annabi (SAWA)

Lokacin da ciwon ajali ya kama shi, ya yi wa Imam Ali (A) wasici da cewa idan ya cika ya yi masa wanka shi kadai. Ya tabbatar masa da cewa Mala’iku za su taimaka masa. Ya kuma yi wasici da cewa idan ya cika a rufe shi a dakin da ya cika (wato dakinsa), kuma a yi masa likkafani da suturu uku. Daga nan sai aka ga ya kai bakinsa kunnen Imam (AS) ya yi masa wata doguwar magana da babu wanda ya ji, alamu dai sun nuna cewa tana da matukar muhimmanci, domin an ga fuskar Imam ta canza kuma zufa na karyo masa.

Yayin da lokacin sallah ya yi, Bilal ya kira sallah, sai Annabi ya bukaci Imam Ali (AS) da baffansa Abbas dan Abdul-Mudallibi da su rike kafadunsa su kai shi masallaci. Bayan ya ja-goranci jama’a sallah sai ya yi musu hudubar karshe, wadda a cikin ta ya jaddada musu wasu daga wasiyyoyin da ya yi musu tun tuni; ya kuma kara karfafa wasiyyarsa a kan riko da nauyayen nan biyu da ba a bata matukar an yi riko da su; wato Littafin Allah da Ahlulbaiti (AS). Yayin da Musulmi suka ga halin da ya ke ciki duk sai suka rude da kuka, suna kururuwa sun fadar Inna Lillah Wa Inna Ilaihi Raji’un.

Bayan ya gama hudubarsa, sai Imam Ali (AS) da Abbas (RA) suka kama shi suka shiga da shi gida ya ci gaba da jinya, har lokacin da Allah Madaukaki Ya karbi ransa a bayan sallar la’asariyar ranar litinin, 17 ga watan Safar, shekaru goma cur bayan hijirarsa. Amincin Allah Ya tabbata gare shi a duk fadin rayuwarsa da bayan mutuwarsa.

Bayan rasuwar Manzo (SAWA), sai Imam Ali (AS) ya yi masa wanka, kamar yadda ya yi wasici, sannan a daren talata da laraba aka yi ta masa sallah. Imam Ali da zuriyyarsa da wasu Sahabbai (irin su Salman, da Abu Zar da Ammar) ne suka fara yi masa salla, daga baya sai sauran Musulmi suka rika shiga jama’a bayan jama’a suna yi masa sallah har suka kare.

Sai dai kuma wani abin takaici shi ne, mafi yawan Musulmin wannan lokacin ba su sami daman halartar bisne shi ba saboda shagaltuwa da suka yi da rikicin Khalifanci da mulki.

[1] Za a iya samun wannan riwaya a cikin littafin Kashful-Gummah, na Arbili, juz’i na 1, shafi na 15; kamar yadda Allama Ja’afar Murtadha al-أmili ya fitar a shafi na 63, juz’i na 2 na littafinsa al-Sahih min Siratin-Nabiyyil-A’azam; bugun Darus-Sirah

[2] A kokarin da suka nace a kai na hadin kan Musulmi, masamman tsakanin Shi’a da Ahlussuna, malaman Shi’a, bisa tsarin Imam Khumaini (RA), sun fitar da shirin shagaltuwar Musulmi da tattuna matsalolinsu da hanyoyin magance su a kwanakin dake tsakanin 12 zuwa 17 ga watan Rabi’ul Awwal na kowace shekara. Suka yiwa makon da ranakun suka fada cikinsa suna da makon hadin kai. Ya zama hakki a kan malaman Musulmi da shugabanninsu da su himmatu da raya wannan ingantaccen shiri da duk iyawarsu, wajen kusantar juna da kulla zumunci tsakanin juna, tare da yiwa juna uzuri da afuwa kan abubuwan da aka saba. Kamar yadda ya zama wajibi ga al’ummar Musulmi da su godewa Imam Khumaini bisa wannan dogon hange na shi.

[3]An fitar da wannan a littafin Kamusur-Rijal na Balaziri, wajen tarihin Suwaiba, juz’i na 10, shafi na 427.

[4]A cikin Kasaful-Gummah, juz’i na 1, shafi na 16.

[5] A cikin littafinsa na tarihin Annabi mai tarin kima, wato al-Sahih Min Siratir-Rasulil-Akram, juz’i na 2, shafi na 68, bugun Darus-Sirah dake Lebanon.

* Wannan shi ne abin da nazarin tarhi da bin diddigi ya tabbatar. Abin da ya shahara na cewa ya aure ta a lokacin tana da shekaru arba’in ya sabawa abin da shi, da kansa, ya karantar da Musulmi na mustahabbancin saurayi ya auri budurwa. Manzo kuwa bai kasance yana aikata abin da zai zo ya karhanta shi daga baya ba. Kara da cewa tarihi ya tabbatar da cewa ita ce ta haifi dukkan ’ya’yan Annabi banda Ibrahim; a ilmance kuwa zai yi wuya tsohuwa mai irin wadancan shekarun ta haifi irin wadannan ’ya’yan cikin shekaru goma sha uku kacal. Ga kuma wata riwaya ta Ibin Abbas dake karyata wancan zance, take kuma tabbatar da abin da muke fada (Duba littafin al-Fatima wal-Fadimiyyun, na Abbas al-Akkad don karin bayani).

* Biyun da tarihi ya kasa tabbatar da ingancin samuwarsu su ne Rukayya da Zainab, wadanda aka ce ’ya’yan Abu Lahabi biyu (Abdullahi da Ubaidullahi) sun aure su a lokacin Jahiliyya, bayan zuwan Musulunci (wai) sai aka raba su Usman ya aure su daya bayan daya ta rasu a hannun shi. Wa ya sani, ko wannan na cikin abin da aka kirkira don samun wata daraja ga Usman, ko don wani abin daban. Uhum! dama haka tarihin na mu ya ke gunin takaici!!

* Idan mutumin yau na so ya fahimci mummunan yanayin da duniya ta kasance kafin aiko Annabi (SAWA), sai ya dubi yadda duniya ta ke a yau, da halin da take ciki na rashin gaskiya kiri-kiri da zalunci da barna da rashin tsari. Don haka a yanzu ma muna raye ne a zamanin Jahiliyya.

* Abin takaici da ban kunya ga Musulmi shi ne, suna cikin halin gafala da sabawa addininsu Yahudawa, bisa goyon bayan wasu kasashen Turai, suka zo suka mamaye wannan wuri mai tsarki. Sabani, da kace-na-ce, batanci ga juna da kafirta juna sun hana su yin katabus a kan wannan. Wasa-wasa al’amari ya cabe musu, suna kallo ana kashe ’yan’uwansu alhali ba sa komai sai surutan da ba sa da wani amfani. Wallahi kuwa ba su da wata mafita a kan wannan sai sun koma bisa karantarwar addininsu, sun kiyayi rarraba da kafirce-kafircen juna. Allah Ya nuna mana wannan lokaci.

[6] Sakayyar tarihin Musulunci ga Abu Dalib kan wannan babbar gudunmawa shi ne kafirta shi da cewa ya mutu Mushriki. Ban sani ba wane irin shirka ne wannan mai kariya ga Musulunci. Kuma me yasa Annabi ya yi bakin-ciki da mutuwarsa har ya sawa shekarar suna Shekarar bakin-ciki?

* Wani abu mai jan hakali shi ne cewa Sarki Najjashi, a wannan lokacin, Kirista ne shi da mutanensa. Kuma da haka ya karbi Musulmi ya ba su mafaka a kasarsa. Don haka mu ke cewa: a cikin wadanda suka ba addinin Musulunci gudunmwa akwai Kirista. Wannan wani babban kalubale ne ga Musumi da Kirista, a bangaren zamantakewa. Wane Muslmi ne zai fito ya ce Annabi bai yi daidai ba da ya tura Musulmi kasar Kirista hutu? Ko wane Kirista ne zai ce Najjashi ya yi kuskuren karabar Musulmi? Sai dai mai son zuciya. A cikin wannan akwai darasi na zamantakewa tsakanin mabiya addinan biyu.

[7] Wannan shi ya fi kyau a kan yadda yawa-yawan malamai da marubuta tarihi ke fada, na cewa “tsakuwa na tasbihi a hannun Annabi”. Domin tsakuwa na tasbihi a hannun kowa ma, kamar yadda AlKur’ani ke cewa: Babu wani abu face yana tasbihi da gode maSa (Allah), sai dai ku ba ku jin tasibihinsu. Amma ana ji a hannun Manzo.

[8] Wani abin lura da ya wajaba a fadaka da shi, shi ne cewa Musulmi ba sa shakka a kan dukkan Mu’ujizozin Annabi (SAWA). illa dai daga baya an sami wasu Wahabiyawa (da duk bangarorinsu) suna musanta Mu’jizozin; kai! Wasu na yi musu izgili ne ma, suna cewa: ya ya za a yi mutum ya ga bayansa? Ko ya ya za a yi mutum ya ji magana a lokacin da yake barci? Wani ma ya taba ce min wai surkulle ne a ce ana ganin alamun kafar Annabi in ya yi tafiya a kan dutse, alhali ba a gani in yana tafiya a bisa yashi. Wannan ba abin mamaki ba ne, domin su ne suka haramta raya ranar haihuwarsa, da ranar aiko shi da ranar rasuwarsa. Kai sun ma hana Musulmi ziyarar kabarinsa, bisa dogaro da wasu riwayoyin karya da makiya Musulunci suka dasa a littafan Musulmi don raba su da Annabinsu (SAWA).

[9] Sayyid Murtdha al-Amili, al-Sahihu min Siratil-Rasulil-Akram.

2- Imam Ali bn Abi Talib (a.s):
________________________

Shi ne Amirul-Mu’uminina Ali dan Abi Talib, abin wasicin Manzo, gwarzon Musulunci, kofar ilimin Annabi, majin Batul, baban Hasan da Husaini kuma kanin Annabi.

Babu shakka kan cewa shi ne farkon wanda ya fara karbar Musulunci, ba farkon wanda ya Musulunta (kamar yadda masu tarihi ke rubutawa) ba. Domin ba a cewa ’wane ya Musulunta’ har sai ya taba yin kafirci. Imam Ali kuwa bai taba yin kafirci ba (bisa dacewar dukkan Musulmi). Af, ba ka ga ba wanda ke cewa ‘Manzon Allah (SAWA) ya musulunta ba’? Ai saboda bai yi kafirci ba ne.

Idan wannan ya tabbata, to kar ma masu kokarin tawili (irin su Ibin Kathir) su wahalar da kansu wajen cewa:

Ana cewa shi ne farkon wanda ya musulunta. Amma abin da ke ingatacce shi ne cewa shi ne farkon wanda ya musulunta daga yara![1]

Wannan rabe-raben musulunta an yi shi ne don a sakaya baiwar da Allah Ya kebance shi da ita na gabatar da shi a kan wasu (dake da galihu a tarihi). Kana ganin da daya daga cikin ‘yan gatan ne ke da wannan fifikon da za a yi wannan kasau din? In ba haka ba, me ke fa’idar kasau din? A fito mana a fadi wanda ya gabaci kowa a Musulunci, ba tare da la’akari da yaranta, matanta ko manyanta ba!

Wani abu dake kara tabbatar da wannan hasashe shi ne fadarsu cewa:

Dalilin musuluntar Ali yana yaro shi ne cewa ya kasance karkashin renon Annabi (SAWA); domin a shekarar da yunwa ta same su, sai ya dauke shi daga wajen mahaifinsa, ya kasance tare da shi. Lokacin da Allah Ya aiko shi da gaskiya sai Khadija ta yi imani da shi, sai mutan gida a cikin su har da Ali…

Ka ji ciwon zuciyar ko? Su waye wadannan mutan gidan? Bari ma ka ji fiye da haka:

Imani mai amfani da mutane za su iya dogara da amfaninsa shi ne imanin Saddik (yana nufin Abubakar)[2].

Aha! Ka ji inda aka dosa tun farko! Amma sai aka fake da rabe-raben musulunta!!

Matsayinsa (AS)

Hakika a Musuluncin nan banda Annabi (SAWA) babu wanda ya sami abin da Imam Ali (AS) ya samu na yabo da girmamawa daga Allah Madaukaki. Yana cikin wadanda ayar tsarkakewa[3] ta sauka a kan su, haka ayar ciyarwa[4] da ayar Mubahala[5]; ayar Wilaya[6] kuwa a kansa shi kadai ta sauka. Kai a takaice ma dai malamai sun ce babu ayar da Allah zai ce: “Ya ku Muminai” face Ali ne shugabansu (Muminan).[7]

Wancan dangane da ayoyi kenan. Hadisai kuwa a kan haka sun yawaita, don ta’kidi da karin bayani a kan matsayisa a wannan addini. Manzo (SAWA) ya fada yana mai magana da shi cewa:

Ya Ali, ba mai son ka sai Mumini kuma ba mai kin ka sai munafuki.[8]

Har ila yau Manzo ya yi magana da shi da cewa:

Kai dan’uwana ne kuma ni dan’uwanka ne. duk wanda ya ce maka wani abu ka ce: ‘Ni bawan Allah ne kuma dan’uwan ManzonSa’. Ba mai ikrari da haka banda kai sai makaryaci.[9]

Haka na ya fada game da shi cewa:

Ali na tare da gaskiya, kuma gaskiya na tare da Ali; ba za su rabu ba har su same ni a bakin tafki.[10]

Imam Ali (AS) ya shaida dukkan yakoki tare da Manzon Allah (SAWA), kuma bai taba gazawa ko kasala a cikin su ba, balle kuma gudu da juya baya.

Haihuwarsa (AS)

An haife shi a ranar juma’a, sha uku ga watan Rajab shekaru sha biyu kafin aiko Annabi (SAWA). An haife shi a cikin dakin Ka’aba; shi ne farkon wanda aka Haifa a cikinsa (Ka’aba), ba a kuma kara haihuawar wani a ciki bayansa ba; wannan kuwa girmamawa ce gare shi daga Allah Madaukaki.[11]

Mahaifinsa shi ne Abu Talib, da ga Abdul-Mudallibi kuma baffa ga Annabi (SAWA); wannan da ya bayar da kariya ga Annabi, ta yadda har rasuwarsa (tare da Khadijah) ta sa Manzo ya yi hijra daga Makkah zuwa Madina, ya kuma kira shekarar da ya rasu da shekarar bakin-ciki. Ya mutu yana mai imani da sakon Annabi (SAWA).

Mahaifiyarsa kuwa ita ce Fadimatu ’yar Asad dan Hashim. Tushenta daya da mahaifin Annabi. Don haka ne ma aka ce: Ita ce farkon Bahashimiyar da ta haifi Bahashime.[12]

Albishrin haihuwarsa na isa ga Manzon Allah (SAWA) sai ya bayyana murna da tsananin farin-cikinsa.

Tun daga haihuwarsa Manzo (SAWA) ya rinka kaiwa da komowa tsakanin gidansa da gidan Abu Talib, don kewaye wannan abin haihuwa da lurarsa ta masamman da kaunarsa. Ya kasance yana daukarsa a kirjinsa, yana girgiza shi har ya yi barci da sauran wadannan na daga alamomin kauna. Haka ya ci gaba har na tsawon lokacin da abin haihuwa ya share tare da mahaifansa.

Karkashin Tarbiyyar Annabi (SAWA)

Bayan abin haihuwa ya cika shekaru shida da haihuwa, sai Allah Ya zaba masa makarantar farko a gidan mafi alherin malami. Domin kuwa Kuraishawa ne suka fuskanci matsanancin matsin tattalin arziki, wanda tsananinsa ya kuntatawa Abu Talib, domin da ma shi mutum ne mai yawan iyali kuma “wani kogo ne da mabukata da talakawa kan dogara da shi”, wannan kuwa saboda irin matsayinsa ne a tsakanin mutanen Makka.

Wannan ya sa Manzo (SAWA) ya je wajen baffansa Abbas dan Abdul-Mudallib, ya ba shi shawarar su ragewa Abu Talib nauyin iyali. Abbas ya yi maraba da wannan shawara, sai suka nufi wajen Abu Talib suka gaya masa abin da ke tafe da su; sai shi kuwa ya amnice musu. Sai Abbas ya dauki Ja’afar, Manzo kuma ya dauki Ali (AS), a lokacin yana da shekaru shida.

Wannan ya sa Imam Ali (AS) ya tashi a gidan Annabci tun yana dan karaminsa, yana sha daga bubbugen wahayi, ya dace da kulawar Annabi da tausayinsa. Manzo ya karantar da shi daga abin da Allah Ya sanar da shi. Bai taba rabuwa da shi ba tun daga wannan lokacin har Manzo ya koma ga Allah Madaukaki. Imam Ali na tunawa da wadannan ranaku da fadarsa:

Hakika [Manzo] ya kasance yana zuwa [kogon] hira a kowace shekara, sai ni ke ganinsa alhali wanina ba ya iya ganinsa. A lokacin gidan bai hada kowa ba a Musulunci banda Manzon Allah (SAWA) da Khadija ni ne na ukun su. Ina ganin hasken wahayi da sako, ina shakar kamshin Annabci.[13]

Sai daga baya za a fahimci cewa ashe duk wannan wani shiri ne daga Allah Madaukaki, na tanajin wanda zai gaji ma’aiki a wannan aiki na isar da sakon Allah. Shi yasa Allah Ya sabbaba kara kusanta shi da Ma’aiki (SAWA) fiye da yadda ya kasance kafin komawarsa gidansa.

Ali (AS) ya kasance Musulmi a fidira. Jahiliyya ba ta bata shi da dattinta ba, bai tasirantu da komai daga rayuwarta ba. Bai taba yin sujjada ga gunki ba, don haka ne ma suke ce masa Karramallahu Wajhahu (wato: wanda Allah Ya karrama fuskarsa).

Lokacin da Allah Ya hori Annabi da ya kira danginsa makusanta, kuma Manzo ya hada su ya isar da sakon gare su, sannan ya tambaye su wanene zai amsa masa ya zama mataimakinsa, Ali ne ya mike ya ce: “Ni ne Ya Manzon Allah, zan zama mataimakinka a kan shi.” A kan haka ne Manzon Allah ya ce:

Zauna, kai dan’uwana ne, abin wasicina, mataimakina, kuma Khalifana a baya na.[14]

Imam Ali (AS) ya shiga cikin duk harkokin da’awa daga farkonta har zuwa rasuwar Annabi (SAWA), kuma duk wahalhalun da Annabi ya sha a wannan hanya tare suka sha da Ali (AS).

Lokacin da Abu Talib ya bar duniya kafin horo da hijira, Imam Ali (AS) ya yi matukar bakin cikin rabuwa da mahaifinsa, kamar yadda Annabi (SAWA) ya yi.

Imam Ali Ya yi Hijira

Lokacin da da’awar Musulunci ta dauki sabon salo, yayin da kafirai suka taru a Darul-nudwah, suka dace a kan cewa su kashe Annabi (SAWA), kuma Allah Ya hori Annabi da yin hijira zuwa Yathrib, manzo ya hori Imam Ali da ya kwana a gadonsa, ya kuma rufa da mayafinsa. Haka kuwa aka yi. Da arna suka kai samame a gidan Annabi da goshin asuba sai suka yi kacibir da zakin-Allah; nan take ya daka musu tsawa da cewa: “Me kuke nema?” suka tambaye shi ina Muhammadu; ya ba su amsa da cewa: “Kun ba ni ajiyarsa ne? Ashe ba ku kuka ce ‘mu fitar da shi daga garinmu ba’? To ya fita daga gare ku.” Sai suka juya suna masu hasara. Da haka Imam Ali ya sadaukar da rayuwarsa don Manzon (SAWA), inda ya misalta gwarzontaka da sadaukarwa, har AlKur’ani mai girma ya zo yana yabon wannan matsayi da cewa:

Daga mutane akwai wanda ke sayar (sadaukar) da kansa don neman yardar Allah; Allah kuwa Mai tausayi ne ga bayi.[15] (al-Bakara:207)

Annabi (SAWA) ya bar shi ne don ya sadar da amanonin dake hannunsa (Annabi din) zuwa ga masu su, sannan daga baya ya dauko Fadima al-Zahra (AS), da Fadima mahaifiyarsa da sauran ’yan gidan Annabi (SAWA).

Manzon Allah (SAWA) bai shiga Madina ba sai da Ali (AS) ya zo ya same shi a Kubah, inda ya yi zango don jiransa.

Kamar yadda muka bayyana a baya, farkon abin da Annabi (SAWA) ya fara aiwatarwa bayan isarsa Madina shi ne hada ’yan’uwantaka tsakanin bangarorin Musulmi biyu; mutanen Makka da suka yo hijira (Muhajirun) da mutanen Madina da suka karbi baki (Ansar). A wannan lokacin, da ma lokacin da ya gabaci wannan, Manzon Allah Ya hada tashi ’yan’uwantakar ne da Imam Ali (AS).*

A rayuwar Madina ne kusan duk yakokin Musulunci da makiya suka faru. A duk yakokin da aka aiwatar tsakanin rundunar Manzon Allah (SAWA) da ta Mushrikai, ba kawai Imam Ali ya kasance gaba-gaba ba ne, bugu-da-kari ya gabatar da jarunta da sadaukar kai irin wadanda tarihi (da duk gurbata shi da aka yi don a zalunci wannan bawan Allah) ya kasa boye su daga gare shi. Wala’lla yaki daya ne bai halarce shi ba, shi ne yakin tabuka, kuma shi ma ba a yi shi ba. Dalilin rashin halartarsa kuwa, kamar yadda Ibin Sa’ad ya fitar, shi ne cewa:

Lokacin da aka shirya rundunar da za ta yakin Usrah, shi ne Tabuka, Manzo (SAWA) ya ce wa Ali (AS): ba makawa ko ni in saura ko kai ka saura. Sai ya Khlifantar da shi. Yayin da Manzo ya tafi don yaki, sai wasu mutane suka ce: ‘Bai khalifantar da Ali ba sai don wani abin kyama da ya gani daga gare shi.’ Sai wannan labari ya je kunnen Ali, sai ya bi Manzo (SAWA) har ya kai gare shi, (sai Manzo) ya ce mishi: Me ya zo da kai ya Ali? Sai (Imam Ali) ya ce: Ba komai ya Manzon Allah, illa dai na ji wasu mutane ne na cewa ka khalifantar da ni ne kawai don wani abin kyama da ka gain daga gare ni. Sai Manzo ya yi murmushi ya ce: Ya Ali, ba ka yarda ka zama a gare ni kamar yadda Haruna ya kasance a wajen Musa ba, banda kawai cewa kai ba Annabi ba ne? sai (Imam Ali) ya ce: ‘E ya Manzon Allah (na yarda). Sai Annabi ya ce: To lallai haka ne.[16]

Imam Ali A Zamanin Khalifofi

Ran Manzon Allah (SAWA) ya fita daga jikinsa a lokacin yana kwance a cinyar Imam Ali (AS). Ya bar duniya cikin damuwa kan yadda sakon Musulunci zai kasance. Domin a karshen rayuwarsa ne ya nemi a ba shi tawada don ya rubuta wa al’umma abin da in ta yi riko da shi ba za ta taba bata bayansa ba. Amma sai wasu suka yi karan-tsaye aka hana hakan[17], don haka sai ya yiwa Ahlulbaiti wasici da alheri.

A daidai lokacin da Imam Ali da sauran zuriyyar Manzon Allah (SAWA) ke shagalce da shirya shi don bisne jikinsa mai daraja, sai Ansar suka hada taro a Sakifatu Bani Sa’idah, don nasabta wanda zai khalifanci Annabi wajen ja-gorancin Musulmi.

Wasu daga cikin Muhajirun sai suka gaggauta halartar taron (bayan an je an tsegunta musu). Nan ne fa aka yi ta muhawarori masu kaifi da tsanani, abin da ya samar da wani yanayi na rsahin kwanciyar hankali da sabani da gardandami. Nan take Umar bin Khaddab ya gaggauta yiwa Abubkar Mubaya’a da khalifanci, ya kuma nemi sauran wadanda ke nan da su yi haka. Sai wasu suka yi mubaya’a wasu kuwa suka ki.

Har zuwa wannan lokacin Ahlulbaiti ba su gushe ba cikin jana’izar Manzon Allah (SAWA); domin jikinsa mai tsarki ya yi kwanaki kafin a bisne shi, don Musulmi su sami daman yin sallama da shi da yi msa sallah.

Saboda rashin amincewar Imam Ali (AS) da abin da ya gudana, da imanin da ya ke da shi na cewa Khalifanci hakkinsa ne, ya janye wa mutane ya bar su da abin da suke ciki har na tsawon watanni shida, ba a jin komai daga gare shi. Bai shiga cikin yakin da suka kira ‎yakin masu ridda ba, bai kuma shiga wasun wannan na daga harkokinsu ba.[18]

Wannan sauyi ya haifar da wasu abubuwa da suka kasance barazana ga Musulunci da al’ummarsa. Domin al’amarin masu da’awar annabcin karya ya karfafa bayan rasuwar Annabi (SAWA), haka nan Munafukai sun kara samun kaimi, hadarinsu ya kara girma a tsibirin harabawa baki daya, masamman kuma a Madina. Ga Romawa da Farisawa na jiran Musulmi a gefe daya. Banda kuma rikicin siyasa da ya addabi al’ummar Musulmi a sakamakon abin da ya faru a Sakifah.

Wannan ya sa Imam Ali (AS) ya yi mu’amala da Khalifofi daidai da yadda maslahar Musulunci ta hukunta, alahli yana mai kariya ga Musulunci daga wargajewa da bacewa, don kuma ya cimma babbar manufar Musulunci da ya yi ta yaki don ita. Ya yi bayanin haka a fadarsa:

Sai na kame hannuna har sai da na ga akalar mutane an karkatar da ita daga Musulunci, ana kiran su zuwa gurje addinin Muhammadu (SAWA). Sai na ji tsoron cewa in ban taimaki Musulunci da mutanensa ba, zan ga wani gibi da baraka, damuwa da haka kuwa ya fi girma gare ni a kan kufcewan mulkin ku, wanda ba komai ba ne illa jin dadi na ’yan kwanaki kadan; (daga nan) abin da ya kasance daga gare shi (mulkin) zai gushe kamar yadda rairayin sahara ke tashi ko kamar yadda girgije ke washewa. Don haka sai na yunkura a irin wannan yanayi har sai da barna ta kau kuma ta tuke, addini ya natsu kuma ya sarara.[19]

An kasance ana jin muryar Imam Ali (AS) a duk lokacin da aka tambaye shi ko aka nemi shawararsa; wannan kuwa don ya fuskantar da rayuwar al’umma ne daidai da yadda sakon Musulunci ke hukuntawa.

A duk wannan tsawon lokaci na rasuwar Annabi (SAWA) da zaman shi Khalifa, Imam Ali (AS) ya aiwatar da manyan ayyukan addini masu girman gaske. Don haka ne ma duk mai bin diddigin tarihi zai sami Imam (AS) a wannan lokacin yana magance wasu mas’aloli da hukunce hukunce da babu mai iya warware su sai shi. Ya bayyana hukunce hukuncen Allah Madaukaki ya kuma kare Sunnar ManzonSa (SAWA).

Imam Ali Shugaba

Bayan wani abin takaici da ya haifar da yiwa Khalifa na uku (Usman bin Affan) bore, wanda kuma ya sabbaba kashe shi a hannun wasu Musulmi (daga Sahabbai), al’umma ta yiwa Imam Ali (AS) kawanya kan sai ta yi masa mubaya’a a matsayin Khalifa; sai dai shi (a matsayin cika hujja gare su) ya ki amsa musu da farko, ya ce musu:

Ku kyale ni, ku je ku kama kafa da wanina (ku yi masa bai’ar)[20]

A ganina, Imam (AS) na son ne a nan ya ja hankalin al’umma a kan kuskurenta. Kamar dai yana cewa: “Ba kun riga kun gabatar da wanina a kaina tun farko ba? To yanzu ma kuje ku nemi wanin nawa kamar yadda kuka saba”. Kukan kurciya ai jawabi ne!

Har ila yau Imam Ali (AS) na so ya tabbatar musu da cewa shi ba ya cikin irin mutanen da shugabanci ke rufewa ido. Ya sha bayyanawa a hudubobinsa cewa shugabanci bai yi daidai da fiffiken sauro a idonsa ba. Kuma mulki ba bakin komai ya ke ba matukar bai zama hanyar tsayar da gaskiya da kawar da barna ba.

Yayin da al’ummar ta nace kuma hujja ta tabbata a kanta, sai Imam Ali (AS) ya amsa bisa sharuddan da ya yada kowa ya ji, na cewa:

Ku sani cewa ni idan na amsa muku zan ja ku ne da abin da na sani, ba kuma zan saurari zancen mai zance ko sukan mai suka ba.[21]

A nan Imam (AS) na so ne ya sanar da su cewa: sabanin yadda suka saba, shi zai ja su a kan abin da ya sani daga Musulunci, na irin abin da zai saba da son zukatan wasu mutane. Kan haka ne ya ke cewa[22]:

Yayin da aka ba ni –gwamnati- sai na duba Littafin Allah da abin da aka tanadar mana kuma aka hore mu –da shi- na hukunci, sai na bi shi; haka abin da Annabi ya sunnanta sai na yi koyi da shi.[23]

Nan da nan al’umma ta gaggauta karbar sharuddansa, ta mika masa hannunta na mubaya’a don ya ja-gorance ta a fagagen tunani da ayyukan yau da kullum.

Imam Ali (AS) ya yi cikakken bayanin dalilin da ya sa ya amsa bukatun mutane ya karbi wannan shugabanci, inda ya ce:

Ya Allah Kai Ka san cewa abin da ya kasance daga gare mu bai kasance rige-rigen neman mulki ba, ba kuma hadaman wani abu da aka ci aka rage ba ne. Sai dai don mu dawo da dokokin addininKa, mu kawo gyara a garuruwanKa; ta yadda wadanda ake zalunta daga bayinKa za su aminta, kuma a tsayar da dokokinKa da aka daina aiki da su.[24]

Wannan ka’ida da Imam ya ginu a kanta ne ta sa ya rungumi aikin kawo gyara ba ji ba gani, a dukkan fagagen siyasa, da tattalin arziki da zamantakewa.

Ya yi matukar kiyayewa wajen zabar gwamnonin da zai yi aiki da su. Ya kawar da duk wani nau’i na bambanci tsakanin mutane wajen rabon tattalin arzikin kasa; inda ya tabbatar da cewa takawa da gabata a Musulunci, da jihadi da sahibantar Manzon Allah (SAWA) wasu al’amurra ne da ba sa bambanta masu da sauran mutane a duniya; sai dai su suna da ladaddakinsu ne wajen Allah a gobe kiyama. Don haka duk wanda ya zama ya dace da samun wani abu daga wadancan darajoji, to Allah ne zai dauki nauyin saka masa. Amma a duniya mutane duk daya suke wajen cancantar hakkoki na dukiya, haka a gaban shari’ar Musulunci da wajibai da takalifofi.[25]

Imam Ali (AS) ya kwana da sanin cewa abin da ya ke son aiwatarwa na Adalcin Musulunci a kan mutne ba zai yiwa wasu mutane dadi ba; masamman irin wadanda suka kasance suna amfana da kusancin da suke da shi da gidan mulki ko wani abin dabam, wajen wawure kudaden mutane a lokacin mulkin da yagabata.

Ilai kuwa, abin da Imam ke tsamani ne ya kasance. Domin wadanda suka saba da rayuwar jin dadi sun kasa jurewa adalcin Ali (AS), wanda ya daidaita da da bawa, Balarabe da wanda ba Balarabe ba, ya sanya mutane suka zama daya kamar kan mashaci, tun da ai shi shugabansu ne ba tare da wani bambanci ba.

Zubairu bin Awam da Dalhatu bin Ubaidullah sun yi inkarin wannan siyasa ta Imam Ali, sun ga hakan a matsayin abin da ya saba da abin da mutane suka saba da shi. Imam ya tambaye su dalilin hammayarsu da shi. Su kuma suka amsa masa da cewa: “ai kai ne ka sanya hakkinmu kamar hakkokin sauran mutane, ka kuma daidaita tsakaninmu da wasu da ba su kai mu ba”. Sai Imam ya ba su amsa da cewa:

Amma abin da kuka fada na daidaitawa, hakika wannan wani al’amari ne da ban yi hukunci a kan shi da ra’ayina ba, ba kuma wani son zuciya na sa a ciki ba; ni da ku mun same shi daga abin da Manzon Allah (SAWA) ya zo da shi, ya kuma gama da shi. Ba zan ja da ku a kan abin da Allah Ya riga Ya raba shi Ya kuma aiwatar da hukuncinsa ba. Wallahi a kan haka ba ku da wani zargi a kaina haka wanin ku. Allah Ya yi riko da zukatanmu da naku zuwa gaskiya, Ya kuma yi mana, da ku, ilhamar hakuri. Allah Ya ji-kan mutumin da ya ga gaskiya ya yi taimako a kanta, ko ya ga zalunci ya kawar da shi, ya kuma zama mai taimako ga gaskiya da mai bin ta.[26]

Yakin (Basara) Jamal

Zubair da Dalha ba su wadatu da bayanin da Imam ya yi musu ba; don haka sai suka fara shirin yakarsa, suna tunzura Musulmi a kan fitowa tare da su. Wannan ya sa al’umma cikin matsanancin tashin hankali, saboda sun ja hankalin A’isha matar Annabi tare da su zuwa Basara don yakar Ali (AS).

A Basara din ma, Imam ya yi ta kokarin jan hankulansu da yi musu nasiha amma abin ya faskara.

Imam ya hadu da Zubair ya tuna masa wani zance da Manzon Allah ya fada masa na cewa:

Wata rana za ka yake shi –Ali- alhali kana mai zaluntarsa.

Zubair ya bayyana cewa shi ya manta ne, amma yanzu ya tuna. Don haka ya yi amazar komawa, amma sai dansa Abdullahi ya nuna masa cewa tsoro ne ya kama shi.[27]

Haka dai yaki ya balle tsakanin rundunonin biyu (na gaskiya da na bata). A karshe, bisa al’ada, Imam ya yi nasara a kansu; ya kuma yi yekuwar yin afuwa ga kowa, ya koma da Ummul-Muminina A’isha zuwa Madina, ya tunatar da ita horon Allah gare ta na cewa:

Ku zauna a cikin gidajenku, kuma kar ku rika fita irin fitar jahiliyyar farko. (al-Ahzab: 33).

Yakin Siffen

Tarihi ya tabbatar da cewa babbar matsalar da Imam Ali (AS) ya fuskanta a lokacin Khalifancinsa ita ce matsalar gwamnonin da suka shugabanci kasashen Musulmi a karkashin Khalifofin da suka gabace shi. Mafi yawan su sun kasance, ba kawai ba su da siffofin shugabanci ba ne, a’a wasun su ma fasikai ne na gaske.

Wasu daga cikin su suna bakar adawa da Manzo (SAWA); kuma sun cutar da shi, kamar Hakam bin al-أs, wanda ya kasance yana matukar cutar da Annabi, har ma sai da Manzo ya kore shi daga Madina.

Daga cikin irin wadancan akwai Walid bin Ukbata bin Abi Mu’id, gwamnan Usman a Kufah, wannan ya kasance “mazinaci kuma mai yawan shan giya. Har ma yana da wani abokin shan giya Banasare.”[28]

Har ma ya taba yi wa mutane sallar asuba raka’a hudu a lokacin yana cikin halin maye.

Daga cikin su akwai Abdullahi bin Sa’ad bin al-أdi; wanda ya taba zama sakataren Manzon Allah (SAWA), sai ya ha’ince shi wajen rubutu, sai Manzo ya kore shi; shi kuma sai ya yi ridda daga Musulunci. A karshe Usman ya nada shi gwamnansa a Masar.

Daga cikin su akwai Mu’awuya dan Abu Sufyan, gwamanan Sham tun lokacin Umar bin Khaddab, Usman kuma ya tabbatar da shi.

Ahmad bin Hambali ya fitar, daga Abdullahi bin Baridah, ya ce:

Ni da babana mun taba shiga wajen Mu’awuya, sai ya zaunar da mu a kan shimfida, sannan ya kawo mana abinci muka ci, sai ya kawo mana abin sha –giya-, sai Mu’awuya ya sha, sai babana ma ya taba, sai ya ce: ‘Rabo na da shan ta tun da Annabi (SAWA) ya haramta’.[29]

Mu’awuya ya kasance mai bakar adawa da kiyayya ga Ali (AS), saboda ya kashe masa dan’uwansa Hanzalah daga Mushrikai a lokacin yakin Badar, da kawunsa Walid bin Utbah da wasun wadannan masu yawa daga wadanda suka kasance cikin rundunar Kafiran Kuraishawa.

Tsananin adawarsa ga Imam Ali (AS) har ta kai ga ya sa a rika zagin Imam Ali a mumbarorin masallatai da kowace hudubar juma’a.[30]

Yayin da ya kasance babu makawa Imam Ali (AS) ya sauke irin wadannan gwmanoni ya musanya su da wadanda suka fi su dacewa, sai sauyin ya sa suka yi wa Imam bore. Sai suka sami Mu’awuya a matsayin mafakar da ta dace wajen yakar Imam Ali. Don haka sai suka hadu da Mu’awuya, shi kuma ya bayyana kangarewarsa ga Imam (AS), ya janye da’arsa daga Imamin zamaninsa.

Ya zama dole ga Imam ya yaki Kungiyar Azzalumai karkashin ja-gorancin Mu’awuya bin Abi Sufyan. Haka kuwa ya faru, domin bangarorin biyu sun hadu a daidai kogin Furat (a Seffin).

Imam ya yi bakin kokarinsa wajen hana zubar da jini da kiyaye hadin kan Musulmi, sai dai Mu’awuya, bisa shawarar Amr bin al-أs, ya dage sai da ya ga hakan ya faru. A karshe an zubar da jinin dubban mutane cikin yakin da ya sharare makonni biyu.

Karshen al’amarin, a sakamakon wani makirci da Amr bin al-أs ya shirya, sai yakin ya kare da abin da suka kira da hukunci. Suka ruda masu saukin fahimta daga sojin Imam Ali, suka yi murda-murda aka watse ba tare da an cimma wata matsaya ba.

Makirce-Makircen Mu’awuya

Bayan yakin Siffen, sai Mu’awuya ya koma ya fara tasarrufi kamar shi ne cikakken mai hukunci a kan mutane:

Ya shiga tara dukiyar Zakka da haraji. Yana aikawa da rundunoni zuwa garuruwa don tsorata mutane da shimfida mulkinsa.[31]

Mu’awuya, ba kawai ya zabi miyagun ma’aikata da sojoji ba ne, bugu-da-kari sai da ya darje masu mummunar adawa da mugun kulli da Musulunci. An ce:

A shekara ta 40 bayan hijira, Mu’awuya ya aika da Busir bin Abi Arda’ah, a matsayin kwamandan wata runduna mai mayaka dubu uku; ya hore shi da kama hanyar Hijaz, da Madina da Makka, har sai ya kare da Yaman. Ya ce masai: ‘Kar ka bar garin da ka sauka a cikinsa alhali mutanensa na da wilaya ga Ali har sai ka shimfida musu harshsenka –da barazana-; har sai sun ga cewa ba su da wata mafita daga gare ka, da cewa ka na kewaye da su; sannan sai ka kira su zuwa ga mika min bai’a, duk wanda ya ki ka kashe shi. Ka kashe ’yan Shi’ar Ali a duk inda suke.[32]

Haka kuwa aka yi. Domin Busira ya kashe sama da mutum dubu talatin daga ‘yan Shi’ar Ali (AS):

Ya shiga bin duk wanda ke da wilaya ga Ali ko ya kasance cikin Sahabbansa da duk wanda ya jinkirta yin bai’a ga Mu’awuya; sai ya shiga kona gidajensu yana rushe su yana kwace dukiyoyinsu. A tsakainin zuwansa da dawowansa ya kashe mutum dubu talatin, ya kuma kona wasu da wuta.[33]

Haka nan Mu’awuya ya hori Sufyan bin Auf al-Gمmiri da ya shiga Iraki ya aikata duk ta’asar da zai iya na kisa, da kona mutane da kwace dukiyoyinsu. Ya ce masa:

Ka rushe duk kauyen da ya shiga hanyarka, kuma ka kashe duk wanda ka hadu da shi daga wanda ba ya kan abin da kake kai, ka kwace dukiyoyi, domin wannan ya yi kama da kisa, ya ma fi cutar da zuciya.[34]

Duk wannan ta’asa da Mu’awuya ya yi ta tafkawa da rashin tausayi bai alakanta shi da addini ba. Domin ya fadi cewa:

Wallahi ni ban yake ku don ku yi sallah ko azumi ko hajji ko zakka ba, domin ai kuna yin haka; na dai yake ku ne don in mulke ku.[35]

Wannan ne ya sa nake mamakin wadanda suka takarkare daga baya suna dangana barnace-barnacen Mu’awuya da addini; da haka sai suka fi shi zama azzalumai!!

A gefe daya kuma dubi siyasar Imam Ali (AS). A duk lokacin da ya aika da wata runduna ya kan yi wasici ga kwamandanta da cewa:

Ku ji tsoron Allah Wanda gare Shi za ku koma. Kar ku wulakanta Musulmi da Kafirin amana. Kar ku kwace dukiya ko ’ya’ya ko zuriya ko da za ku tafi a kafa ne kuwa. Kuma ku kiyaye sallah a kan lokacinta.[36]

Duba wane irin bambanci dake tsakanin bangarorin biyu. Abin da ke cikin akushi ne buso kamshinsa ko warinsa. Mai yabo ya fadi cewa:

فحسبكمُ هذا التفاوت بيننا فكلّ إناءٍ بالذي فيه ينضحُ

Ma’ana:

Wannan ya ishi nuna muku bambancin dake tsakaninmu

Da ma kowane akushi abin da ke cikin shi ya ke hurowa

Don haka fito-na-fito tsakanin Imam Ali (AS) da Mu’awuya fito-na-fito ne tsakanin karya da gaskiya, tsakanin zalunci da adalci. Ba ta fuskar da za su taba haduwa kuwa.

Imam Ali Ya Koma Ga Allah

Imam Ali (AS) na shirin hutar da al’umma daga kungiyar zalunci ta Mu’awuya, sai wata kungiyar ta ‘yan hamayya ta yi mishi gaggawa. Yayin da ta aiwatar da tsohon shirinta na kashe Amirul-Mu’uminin (AS).

Imam na cikin hada runduna mai karfi don yakar Mu’awuya da tsige tushen barnar shi; a daidai lokacin kuma Abdul-Rahman bin Muljam al-Muradi –babban mujrimi- ya shigo Kufah don aiwatar da mummunan shirinsu a cikin wani yanayi da Musulmi ke matukar bukata ga Imam Ali (AS).

Da asubahin ranar sha tara ga watan Ramalana mai albarka na shekara ta 40 bayan hijira; Ibin Muljam ya sara wa Imam takobinsa mai lullube da guba. A lokacin Imam na limancin sallar asuba, cikin halin sujjada (a lokacin da ya dago daga gare shi).

Khawarijawa sun yi taronsu a garin Makka, inda suka dace a kan su kashe kowane daya daga: Imam Ali (AS), Mu’awuya da Amr bin al-أs. Don haka suka dorawa Baraka bin Abdullah al-Taimimi nauyin kashe Mu’awuya a Sham. Umar bin Abi Bakr al-Taimimi kuma shi zai kashe Amr bin al-أs a Masar. Abdul-Rahman bin Muljam al-Muradi kuma ya tafi Kufa don kashe Imam Ali (SA).

Wanda ya tafi Sham don Mu’awuya bai taki sa’a ba; domin Mu’awuya na da masu gadi dake gadinsa hatta a lokacin salla, don haka da ya kai sara bai iya samun Mu’awuya a makasa ba, nan da nan aka kame shi aka jefa a gidan sarka ana jiran bayani. A lokacin da labarin shahadar Imam Ali ya zo gare shi sai ya sa aka saki fursunanna shi don tsananin murna.

Wanda ya tafi Masar don Amr kuwa ya yi kisa, amma fa na’ibi ya kashe; domin a ran nan Amr bai fito salla ba, don haka sai ya sare na’ibin shi. Shi ma an kashe shi daga baya.

Abdul-Rahman ne kawai ya sami nasarar aiwatar da kudurinsa.

Bayan sararsa da aka yi, Imam Ali (AS) ya yi kwanaki uku yana jinya, a cikin su ba abin da ya ke furtawa sai ambaton Allah Madaukaki da yabonSa, da bayyana yardarsa ga hukuncinSa.

Ya yi wasici da alheri yana mai shiryarwa. Daga cikin wasicin da ya yi ga ‘ya’yansa Hasan da Husain (AS) da sauran dukkan mutane akwai cewa:

Ina yi muku wasci da tsoron Allah da cewa kar ku nemi duniya ko da ta neme ku. Kar ku yi takaicin wani abu da ya kufce muku daga gare ta; kuma ku fadi gaskiya kuma ku yi aiki don lada. Ku zama masu ja da azzalumi kuma masu taimako ga wanda aka zalunta. Ina yi muku wasici, tare da dukkan ‘ya’yana da iyalina da duk wanda wannan sakon nawa ya isa gare shi, da tsoron Allah da tsara al’amurranku da kyautata tsakanin ku. Hakika na ji Kakanku (SAWA) yana cewa: ‘kyautata tsakani ya fi dukkan salla da azumi’. Ku ji tsoron Allah cikin al’marin marayu….kar –ku bari- su bace a gaban idonku. Ku ji tsoron Allah kan –hakkin- makotanku, domin su abin wasicin Annabinku ne, bai gushe ba yana mana wasici da su har sai da mu ka yi tsamannin zai sanya su cikin magada. Ku ji tsoron Allah wajen –riko- da AlKur’ani, kar wanin ku ya riga ku aiki da shi. Ku ji tsoron Allah wajen –kiyaye- sallah, domin ita ginshikin addininku ce. Ku ji tsoron Allah wajen –ziyarar- dakin Ubagijinku, kar ku bar shi matukar kuna raye, don in aka bar shi ba ku da abin tinkaho. Ku ji tsoron Allah kan –yin- jihadi da rayukanku da dukiyoyinku. Ku kiyayi ja da baya da yankewa. Kar ku bar horo da aikin alherin da hani da mummuna, domin –da haka- sai a dora ashararan cikin ku a kan ku sannan ku yi addu’a ba za a amsa muku ba.[37]

Haka dai al’umma na ji na gani ta yi hasarar irin wannan taliki da aka kulle mahafun mata daga hahuwar irinsa. Al’umma ta rasa tsaikonta na babban abin misali a ilimi, kwazo, gwarzontaka da zuhudu (gudun duniya).

Ta bangaren shi kuwa, Imam (AS) ya ci ribar duniya. Ya shigo ta da kafar dama ya fita da kafar dama. A rayuwarsa ta duniya ya aiwatar da duk abin da Allah Ya halicce shi don su, ya kuma yi mutuwar da ta fi daukaka, ita ce shahada, a mafi daukakan lokaci, shi ne watan Ramalana, a mafificin wuri, shi ne dakin Allah, cikin mafi kyaun ayyuka, ita ce sallah, a mafificin yanayi, shi ne sujjada. Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da tsarkakan ‘ya’yansa.

‘Ya’yansa

Imam Ali (AS) ya rasu ya bar ‘ya’ya da yawa. Ga dai Hasan da Husain da Zainab da Ummu kulthum, dukkansu ‘ya’yan Fadima (AS). Ga kuma Abul-Fadhl Abbas, uwarsa ita ce Fadimatu Ummul Banin. Ga kuma Muhammad bin al- Hanafiyya, wadda uwarsa ita ce Khaulah. Da wasun wadannan.

[1] Ibin Kathir, al-Bidayatu wal-Nihayah, juz’i na 7, ahafi na 234, bugun Dar al-takwa, AlKahira ,1999.

[2] Ibin Kathir, al-Bidayatu wal-Nihayah, juz’i na 7, shafi na 234-235.

[3] Surar Ahzab, aya ta 33.

[4] Surar Insan, aya ta 8-11.

[5] Surar أli Imran, aya ta 61.

[6] Suran Ma’idah, aya ta 55.

[7] Ibin Hajar, Sawa’ikul-Muhrikah, babin ambaton Imam Ali (AS).

[8] Sahih na Trimizi, juz’i na 2, shafi na 299; da Masnad na Ahmad bin Hambali, juz’i 6, shafi na 292.

[9] Tirmizi, juz’i na 2, shafi na 299, da Nasa’i, cikin Khasa’is, shafi na 3 da na 18, da Ahmad bin Hambali, cikin Masnad, juz’i na 1, shafi na 159.

[10] Khadib al-Bagdadi, cikin Tarikhu Bagdad, juz’i na 15, shafi na 321, da al-Haithami, cikin majma’al-Kabir, juz’i na 7,shafi na 235.

[11] Shabalanji, cikin Nur al-Absar, shafi na 76; da Tirmizi, cikin Manakibu Amirul-Mu’uminin, kamar yadda Muhsin Amini ya fitar a cikin al-Gadir, juz’i na 6, shafi na 22-37; da Shahabud-din Alusi, cikin Sharh Kharidatul-ghaibiyya Fi sharhi Makasid al-ainiyyah, shafi na 15.

[12]Ibin Kathir, al-Bidayatu wal-Nihayah, juz’i na 7, shafi na 234.

[13] Hudubar da ake yiwa lakabi da al-Kasi’ah, a cikin Nahaj al-Balagha, shafi na 301, tsarin Subhi Saleh.

[14] Nisa’i, Khasa’isu Amirul-Mu’uminin, shafi na 6; da Ibin Athir, al-Kamil Fil-tarikh, juz’i na 2, shafi na 22.

[15] Allamah Muhammad Hussaini Dabadaba’i, al-Mizan fi tafsir al-Kur’an, juz’i na 9, shafi na 70.

* Ya kamata a fadaka da cewa wannan ’yan’uwataka tana da ma’anarta ta masamman da manufarta; don haka wannan bai kore kasancewarsu (Manzo da Imam) ’yan’uwan juna na jini ba. Sai a lura da kyau.

[16] Ibin Sa’ad al-Dabakat, juz’i na 3, sashi na 1, shafi na 15. Haka nan Bukhari, da Muslim, da Tirmizi, da Ibin Majah, da Hakim, da Ibin Hambali da Nasa’i, cikin Khasa’is Amirul-mu’minin, duk sun fitar. A tarihi ma Dabari da Ibin Athir duk sun fitar a littafansu na tarihi wajen tarihin Imam Ali (AS).

[17] Bukhari, juz’i na 1, Kitabul-ilmi, shafi na 21, da Muslim, a karshen littafin al-Wasaya, juz’i na 3, shafi na 259.

[18] Sheikh Muhammad Ridha al-Muzaffar, al-Sakifah, shafi na 16.

[19] Nahjul-Balagha, tsarin Dokta Subhi Saleh, shafi na 451.

[20] Nahajul-balagha, shafi na 136.

[21] Nahajul-balagha, shafi na 136.

[22] Wannan karin takidi ne a kan matsayin da ya dauka tun lokacin da aka bijiro masa da Khalifanci bayan mutuwar Umar bin Khaddab. Domin kafin shugaban kwamitin mutum shida da Umar ya nada ya yi tallan Khalifanci ga Usman, sai da ya yi ga Imam Ali (AS) amma bisa sharadin aiki da AlKur’ani da Sunnar Annabi da bin hanyar Abubakar da Umar; nan take Imam Ali ya ki amincewa da sharuddan biyun karshe, ya tabbatar masa da aikata abin da ya sani daga AlKur’ani da Sunna. A nan ma Imam ya kara tabbatar da wannan matsayi na shi ne.

[23] Nahjul-balagha, wasika ta 205.

[24] Nahjul-balagha, wasika ta 131.

[25] Misali saboda wani Sahabi ne ko saboda ya halarci yakin Badar ko wani daga cikin yakokin Musulunci; ko saboda shi yana da wani kusanci na masamman da Allah ta fuskar takawa, duk wadannan ba sa canja komai daga takalifofi da wajiban dake kansa, kamar Salla, da azumi, da jihadi da sauransu. A’a, yadda suke kan kowa haka suke kansa daidai wa daida. Haka wadancan ba su hana a hukunta shi da hukuncin Musulunci ba idan ya yi laifi. To a bangare rabon dukiya ma haka ne. Duba karshen fahimta da adalci irin na Musulunci da Imam ke aikatawa.

[26] Nahjul-Balagha, nassi na 205.

[27] Ibin Sabbag, cikin al-Fusul al-muhimmah, shafi na 62.

[28] Umar ibn Abi Shibh, a cikin Tarikh al-Madinah, juz’i na 3, shafi na 37.

[29] Ahmad bin Hambali, cikin Masnad, juz’i na 5, shafi na 347.

[30] Al’amarin zagin Imam Ali ba boyayye ba ne a tarihi.

[31] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 66.

[32] Al-Thakafi, cikin al-Garat, shafi na 598; kamar yadda aka fitar cikin Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 67.

[33]Al-Thakafi, al-Garat, shafi na 653.

[34] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 68.

[35] Inda aka ambata a sama

[36]Nafakhat Min al-Sirah

[37] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 70.

3- Fatima Al-Zahra (a.s):
________________________

Diyar Ma’aiki, Fatima, Siddikah, Mubarakah, Dahirah, Zakiyyah, Radhiyah, Mardhiyyah; wadda take ma’asumiya.

Fatima ce shugabar matan duniya na farkonsu da na karshensu (hadisi). Ita ce halittar da Manzo ya fi kauna (hadisi). Matsayinta a wajen Annabi kamar matsayin zuciya ne ga mutum (hadisi). Manzon Allah (SAWA) ya kasance yana matukar daraja ta da girmama ta.

Tana daga cikin wadanda ayar tsarkakewa ta sauka a kansu (Ahzab:23). Haka tana cikin wadanda Allah Ya wajabta a so su (Shura:23). Har yau tana cikin wadanda Allah Ya sa a tafi Mubahala da Kiristan Najran da su (أli Imran:61), haka tana cikin wadanda Allah Ya yabi halayyarsu (Insan:7-18).

Babban matsayin da take da shi, wanda ko shi kadai ya ishe ta zama mafificiya, shi ne kasancewar ta ‘ya ga shugaban Manzanni (SAWA), mata ga Aliyu (AS) wasiyyin Manzo, gwarzon Muslunci, zakin Allah, kuma uwa ga Hasan da Husain (AS) shugabannin samarin gidan Aljanna; kuma kaka ga zababbun wannan al’umma da Sharifai baki daya. Ga ta kuma cikin mata hudu da Allah Ya zaba ya fifita su a duniya bisa fadar Manzo (SAWA):

Mafifta matan Aljanna (su ne): Khadija ‘yar Khuwailid (matar Annabi kuma uwar Fatima), da Fatima ‘yar Muhammad, da Asiya ‘yar Mazahim (matar Fir’auna) da Maryam ‘yar Imrana (mahaifiyar Annabi Isa (AS).[1]

Fakhruddin al-Razi, daga malaman Ahlulsunna, ya fada a yayin da yake fassara ayar Mubahala, wajen fadar Allah Madaukai:

و نساءنا و نساءكم

Ma’ana: da matanmu da matanku. Inda Musulmi suka dace a kan cewa (daga matanmu), da Fatima kawai Manzo (SAWA) ya fita zuwa Mubahala. Sai malamin ya ce:

Wannan na nuna cewa Fatima ta fi duk matan duniya. Idan ka ce: to ai Allah Ya ce (a cikin Surar Maryam) ya sanya maryam ta fi matan duniya; sai in ce maka: Ai na lokacinta ne. Af! Ashe ba ka ga cewa kowane Annabi shi ne mafificin lokacinsa ba, alhali Manzon Allah shi ne shugabansu duka baki daya?[2]

Bugu da kari, ga ta kuma ‘ya ga Khadija bint Khuwailid, ummul-mu’minina.

Wannan, a dabi’ance, ya sa dole ta tasirantu da irin halin gidan da ta tashi; wato ta tasirantu da mahaifanta, ta kuma yi koyi da mafi alherin halitta. Wannan ne ya sa ta zama mafificiyar matan duniya na farko da na karshe, kuma abin koyi ga mace Musulma.

Haihuwarta (AS)

An haifi Fatima (AS) a Makka, a ranar juma’a 20 ga watan Jimada al-Akhir, shekara biyar bayan aiko Annabi (SAWA), wato kafin hijra kenan da shekaru takwas. Manzo ya karbi wannan abin haihuwa cikin farin ciki da murna da ba su da iyaka. Nan take ya sa mata suna FATIMA.

Ta tashi kuma ta tarbiyyantu a gidan Annabci da wahayi, tana sha daga tsarkakakken gulbin nan na shi na Imani, tarbiyya da kyawawan dabi’u.

Fatima ta dauko dabi’un Annabi da kamanninsa. A kan haka ne ma A’isha, ummul-Mu’uminina, ke cewa:

Ban ga wanda ya yi kama da Annabi a shiru da kyauta, da tsayuwarta da zamanta kamar Fatima ba. Ta kasance idan ta shigo wajen Annabi (SAWA) ya kan mike mata, ya sumbace ta, ya zaunar da ita a wajen zamansa. Haka idan Annabi (SAWA) ya shiga gidanta ta kan mike daga inda take zaune, ta sumbace shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta.[3]

Fatima ta fara yarantarta ne a daidai lokacin da sakon Musulunci ke cikin mawuyacin halin da ya shiga. Don haka iyayenta sun kasance cikin kuntatawa da cutarwa matsananta, ta yadda har sai da Kuraishawa suka tilasta musu takunkumin tattalin arziki da na zamantakewa tare da sauran Banu Hashim. Don haka Fatima na nan cikin wadanda suka shiga Shi’ibi Abi Dalib.

Mahaifiyarta, Khadija, ta rasu a gaban idonta, a sakamakon dukar da ita da tsananin takunkumin ya yi. Wayyo! Hakika Fatima ta yi tsananin rashin wannan uwa mai tausayi, ta kuma yi kuka kwarai.

Manzo ya yi matukar tasirantuwa da ganin halin da Fatima ta shiga na bakin cikin rabuwa da mahafiyarta, wannan ya sa ya kara lullube ta da kaunarsa don ya musanya mata rashin da ta yi da kaunarsa da tausayinsa.

Hakika Manzo (SAWA) ya so Fatima kuma ita ma ta so shi, ta kuma tausaya masa; har ma an ce babu wanda zuciyarsa ta fi so kuma ya fi kusa da zuciyarsa kamar Fatima. Ya tabbatar da wannan a hadisansa masu yawa; inda ya ke bayyana matsayinta a cikin wannan al’umma. Ga shi nan (SAWA) yana tabbatarwa da Musulmi cewa:

Fatima wani yanki ne daga gare ni, wanda ya fusata ta ya fusata ni.[4]

A wani wuri ya kara bayyana haka da wani lafazin:

Fatima wani yanki ne daga gare ni, abin da yake cutar da ita na cutar da ni.[5]

Fatima ta kasance tana ji da Manzon Allah (SAWA) irin son iyaye mata ga ‘ya’yansu; don haka ne ma ya yi mata lakabi da: Uwa a wajen babanta (Ummu Abiha). Irin wannan alaka ta zama babban abin koyi ga ‘ya Musulma wajen lura da kiyaye iyayenta.

An riwato cewa wata rana daya daga cikin wawayen Mushrikan Makka ya watsawa Manzon Allah (SAWA) kazanta; Manzo ya hakura ya tafi gida a haka alhali kansa da fuskarsa masu daraja na lalace da kura. Lokacin da Fatima ta ga halin da babanta ke ciki sai ta tafi tana kakkabe masa kurar, ta debo ruwa tana wanke kansa da fuskarsa tana kuka saboda bakin ciki da jin zafi; wannan ya yi wa Manzo (SAWA) tasiri kawarai, sai ya sa hannusa ya shafa kanta yana lallashin ta yana cewa:

Kar ki yi kuka ‘yata, lallai Allah mai kariya ne ga babanki, kuma mai taimako gare shi a kan makiya addininSa da sakonSa.[6]

Fatima Ta Yi Hijra

Mun ji, a tarhin Manzo, cewa a sakamakon tsanantar cutarwar Kuraishawa ga Annabi (SAWA), wanda ya sa har sai da suka yi yunkurin kashe shi, Allah Ya hore shi da yin hijira zuwa Madina. Kuma ya yi. Haka nan an ji cewa Manzo ya bar Imam Ali (AS) don aiwatar da wasu ayyuka kafin, daga baya, ya zo ya same shi a gidan hijira. To daya daga cikin wadannan abubuwa da aka bar Ali ya aiwatar shi ne sayen abin hawa don daukar mata, da hada iyalin Annabi don zuwa da su.

Daga daga wadanda Imam Ali (AS) ya dauko ya taho da su Madina akwai Fadimomin nan na Banu Hashim, wato: Fatima ‘yar Manzo (SAWA), da Fatima bint Asad, mahaifiyar Imam Ali (AS), da Fatima bint Zubair bin Abdul-Mudallib, da Fatima bint Hamza bin Abdul-Mudallibi.

An ce Imam Ali (AS) ya tafi tare da su a kafa ba tare da ya hau abin hawa ba, wannan ya sa kafafunsa suka kumbura saboda tsananin tafiya.

Da suka isa Kubah, inda Annabi ya tsaya ya yana jiran isowar Imam Ali (AS) don su shiga Madina tare, sai Annabi (SAWA) ya yi matukar farin ciki. Da ya ga halin da Ali ya shiga, sai ya rungume shi har ya zubar da hawaye saboda tausayin yadda kafafunsa suka kumbura, sannan ya yi addu’a ya tofa a hannunsa ya shafa kafafun biyu da hannun na sa, nan take suka warke bai kara jin ciwonsu ba har aka kashe shi.[7]

Fatima Ta Isa Aure

Sai Fatima ta girma. Kullun daukakarta, darajarta da kyawunta sai karuwa suke yi. Ga ta da kokari. Wannan ya sa hankulan mutane ya koma kanta. Wasu Sahabbai suka fara tunanin neman auren ta don samun darajar kusanci da dangane.

Abubakar ne ya fara gabata don neman auren ta; sai Umar ya biyo bayan shi; haka wasunsu ma sun zo, amma duk Manzo (SAWA) ya nemi uzurin rashin amsa bukatunsu yana ce musu:

Hukunci bai sauko ba tukuna.[8]

Allah Ya yi ilhama ga Ali (AS) da ya je ya nemi auren Fatima (AS), don haka sai ya yi alwala ya yafa mayafinsa, ya yi sallah raka’a biyu, sannan ya tafi wajen Annabi (SAWA), a lokacin Annabi na dakin Ummu Salma. Bayan sun gaisa sai Imam ya dukar da kai yana kallon kasa, sai Manzo (SAWA) ya ce mishi: kana da wata bukata ne? Sai Imam ya ce: “na’am, na zo ne don in nemi auren ‘yarka Fatima”.

Ummu Salma (RA) ta ce: sai na ga fuskar Manzon Allah (SAWA) ta cika da annuri na farin ciki, sannan sai ya yi wa Ali murmushi. Sai ya tashi ya shiga wajen Fatima (AS) ya ce mata:

Ali bin Abi Dalib, wannan da kika san kusancinsa da darajarsa a Musulunci, ya zo yana zance a kan al’amarinki (wato yana neman auren ki). Hakika kuwa da ma ni na roki Ubangijina da ya aurar da ke ga mafi alherin talikanSa kuma wanda Ya fi so daga cikin su. To me kike gani?

Sai ta yi shiru. Sai Manzo (SAWA) ya fita yana cewa:

Allahu Akbar! Shirunta yardarta.

Sannan ya cewa Imam Ali (AS):

Ya Ali, shin kana da wani abu da zan daura maka aure da shi?

Sai Imam Ali (AS) ya ce:

Sai takobina da garkuwata, sai kuma rakumina na ban ruwa (a wata riwayar an ce doki ne maimakon rakumin).

Sai Manzo (SAWA) ya ce:

Amma takobinka kana da bukatar sa, kana yaki da shi a tafarkin Allah kuma kana kashe makiya Allah da shi. Rakuminka kuma kana shayar da (gonar) dabinonka da shi, haka kana daukar kaya da shi, kuma yana daukar ka a tafiye-tafiyenka. Don haka je ka yi yadda za ka yi da garkuwarka.

Sai Imam Ali (AS) ya je ya sayarwa Usman bin Affan da garkuwarsa a kan farashin dirhami 480, sai ya kawo wa Manzo.[9]

Daga nan Manzon Allah (SAWA) ya sanar da Musulmi zancen auren, ya kuma cewa Ali (AS):

Allah Ya hore ni da in aurar maka Fatima a bisa nauyin miskali dari hudu na azurfa in ka yarda da haka.

Sai Imam ya amsa da cewa ya yarda, don haka sai Annabi ya yi masu addu’a da cewa:

Allah Ya hada kan ku, kuma Ya ba ku sa’a, Ya kuma albarkace ku, Ya fitar da tsarkaka masu yawa daga gare ku.

Anas bin Malik Ya kasance yana cewa:

Hakika kuwa Allah Ya fitar da tsarkaka da yawa daga gare ku.”[10]

Da haka auren Ali da Fatima ya cika, bisa madaidaicin sadaki, aka kuma sanya mata kayan gidan da bai wuce kudin sadakin ba, don a karantar da masu zuwa nan gaba cewa abin duniya ba komai ba ne a gaban daraja da mutuncin ‘yan Adamtaka.

Fatima Uwar-gida

Bayan Fatima ta tare ne Imam Ali (AS) ya shirya walimar da ya tara Muhajirun da Ansar.

Fatima ta zauna a gidan mijinta, Ali, cikin jin dadi da farin ciki masu yawan gaske. Wahalhalun yau da kullum na rayuwa ba su taba raba ta da farin cikinta ba; ina! Alhali ita mata ce a gidan Ali, gwarzon Musulunci, ma’abucin sadaukar da kai kuma mai dauke da tutar nasara da jihadi!!

Mata da mijin gaba daya sun rayu karkashin sa-idon Annabi (SAWA), kuma ya ci gaba da nuna mata kaunar nan ta shi, sai ma abin da ya karu. Karuwar kusancin shi da ita har ta kai ga idan zai yi tafiya ita ce karshen wadda ya ke gani; kuma idan ya dawo ita ce farkon wadda ya ke fara gani.

A takaice dai zan iya cewa auren Fatima (AS) da Ali (AS) wani abin koyi ne da Allah Ya tanaje shi ga duk wanda aka rubautawa samun dacewa a wannan bangare mai mahimmanci na rayuwa. Domin ita Ma’asumiya ce ‘yar Ma’asumi, sai aka aurar da ita ga Ma’asumi; wannan ya sa auren ma ya zama ma’asumin aure (da ba wani kuskure a cikin shi). Ka ga kenan zaman mata da miji a cikin shi dole ya zama ma’asumiya zama, wanda daga baya zai haifar da samun Ma’asuman ‘ya’ya! Kai! Mabiya ku kuka dace da mafi kyawun abin koyi cikin rayuwar aure!!

Fatima Uwa

Itaciyar Annabci ta sami yaduwa, yayin da aka haifi Hasan sannan Husaini. Wadanda zancen kowannen su ke zuwa nan gaba.

Bayan su kuma aka haifi Zainab al-Kubrah, gwarzuwar Karbala kuma abokiyar tarayyar Imam Husaini (AS) a jihadinsa. Haihuwarta ta kasance a ranar 17 ga watan Rajab na shekara ta biyar bayan hijira. Manzon Allah ya yi matukar farin ciki da wannan abin haihuwa kwarai da gaske.

Wasu riwayoyin tarihi sun zo da zancen haihuwar wata ‘ya mai suna Zainab al-Sugrah, wadda ake wa lakabi da Ummu Kulthum, wadda da alamun ta rasu tana karama. Ba ni da cikakkiyar masaniya na bin diddigi a kanta da ya wuce wannan.

Amma zancen wata abar haihuwa mai suna Rukayya, wadda har ta girma ta yi aure; wannan wani abu ne da bai tabbata ba bisa bincike da nazari.

Abin da na tabbatar a karshen babin sama na iya ba da surar irin tarbiyyar da Fatima za ta yi wa ‘ya’yanta, wannan kuwa ita ce ma’asumiyar tarbiyya, don ta zama abin koyi ga masu babban rabo a wannan rayuwa ta duniya da gobe lahira.

Halayen Fatima (AS)

Ba zai zama boyayyen abu ba cewa Fatima, wannan da ta tashi a mafi tsarkin gida na Annabci, ta zama ta siffanta da dabi’un wannan gida mai albarka. Ta sha daga marmaro na wahayi, kuma ta raka rayuwar isar da sako tun tana karamar ta har ta kawo karfi.

Don haka Fatima (AS) ta kasance mai yawan ibada, mai kaunar mutane da taimaka musu, mai hakuri da sauran duk wani halin kirki da mutum ke iya tunani. Yaya fa ba haka ba, alhali kuwa wadannan dabi’u daga gidansu suka fita zuwa sauran mutane!

Danta Imam Hasan (AS) ya shaida ibadarta da cewa:

Na taba ganin uwata Fatima a tsaye a wajen sallarta a wani daren juma’a, ba ta gushe ba tsakanin ruku’u da sujjada har sai da asuba ta fara kunno kai. Na ji ta tana ta addu’a ga Muminai maza da mata, tana kiran su da sunansu tana yawaita addu’a gare su; ba ta yi wa kanta addu’a da komai ba. Sai na ce mata: “Ummana, mai ya sa ba ki yi addu’ar ga kan ki kamar yadda ki ke yi ga wasun ki ba?” Sai ta ce: Ya kai dana, makoci kafin gida![11]

Fatima Marainiya

Bayan Manzo (SAWA) ya kammala aikinsa na isar da sako a wannan doron kasa, sai lokacin komawarsa ga Ubangiji ya yi, inda zai tafi ya rayu madauwamiyar rayuwa cikin ni’ima da natsuwa.

Wannan ya sa ciwon ajali ya kama Manzo (SAWA), a hankali ya rika tsananta alhali Fatima na gani tana bakin ciki da damuwa.

Fatima ta zo duba jikin mahaifinta (SAWA) cikin halin rashin jin dadi, sai ya zaunar da ita a gefen shi ya yi mata marhabin. Bayan nan sai ya ba ta labarin cewa ita ce farkon mutan gidan shi da za ta hadu da shi, sai ta yi dariya tana mai farin ciki da haka. Wannan ya nuna tsananin ta’allakuwar ta ne da shi.

A karshe dai Manzo ya koma zuwa ga Ubangijinsa. Fatima ta yi tsananin rashi da bakin ciki mai yawa; a karshe ta dangana tana mai sauraron haduwa da shi nan ba da dadewa ba.

Fatima (AS) ba ta yi tsawon rai bayan Annabi (SAWA) ba, ta tafi ta hadu da shi kamar yadda ya yi mata alkawari. Malaman tarihi sun yi sabani a kan tsawon lokacin da ta rayu bayan shi; wasu sun ce ta rayu na tsawon kwanaki hamsin da bakwai ne; yayin da wasu suka ce watanni uku; kai! wasu ma sun ce ta kai har watanni shida bayan shi.

Fatima ta rayu na wadannan takaitattun ranaku cikin bakin ciki da hakuri, ta share su cikin Ibada da yankewa zuwa ga Allah Madaukaki. Haka ta yi matukar taimakawa cikin harkokin al’umma kamar al’amarin Sakifa, wanda ta taka mahimmiyar rawa a kai. Domin hakika ta tsaya kyam a gefen mijinta Imam Ali (AS) da neman hakkinsa na Khalifancin Manzo (SAWA). Ta kasance tana haduwa da Muhajirun da Ansar tana tattaunawa da su a kan haka, tana neman su da su tuna da alkawarin Allah a kansu.

Babu shakka Zahra ta rayu a wadannan ranaku cikin wahala da tsanantar al’amurra, wadanda sun yi matukar gurbata jin dadin rayuwarta da lafiyarta; domin a gaban idonta tana ganin hakkin mijinta na kaucewa daga wajensa, tana gani an manta da wasicin Manzo (SAWA) a kan Ahlulbait dinsa. Zahra ta bar wannan duniya cikin wannan takaici da yanke kauna.

Sabani ya gudana tsakanin ta da Abubakar kan Fadak, wanda wani fili ne na noma cike da dabino da Manzon Allah ya ba ta kyautar sa a lokacin rayuwarsa. A yayin da Manzo ya bar duniya sai Abubakar ya hana ta, ya ki karbar shedar Imam Ali (AS) kan cewa mallakarta ne. Wannan ya sa Zahra ta yi tsananin jayayya da shi, ta kuma yi maganganu masu zafi da ke kunshe a cikin shafukan tarihi.

Allahu Akbar, Fatima ce kawai ‘yar Annabin da ba ta gaji mahaifinta ba, alahli baban nata ne ya zo da tsarin gado mafi cika!

Mallakan wannan fili bai koma ga Ahlulbait ba sai a lokacin mulkin Umar bin Abdul-Aziz, wanda ya koma da shi ga ‘ya’yan Zahara; amma shi ma bayan ya mutu Umayyawa sun sake kwacewa.

Fatima Ta Bar Duniya

Abubuwan da suka faru bayan Annabi (SAWA), da suka hada da cutar da Zahra (AS) sun kara zafafa mata ciwo. Ta yi jinya har tsawon kwanaki arba’in.

Duk da haka, a karshen rayuwarta ta nuna alamun kamar ta warke, domin ta tashi ta sa ‘ya’yanta Hasan da Husaini (AS) suka yi wanka, ta sa musu mafi kyawun tufafinsu, sannan ta bukace su da su je su ziyarci kabarin Kakansu Manzo Allah (SAWA).

Duk da wannan alama na samun sauki, ashe ita shiri take yi na haduwa da mahaifinta; domin ta bukaci Asma’u bint Umais da ta debo mata ruwan wanka, sai ta yi wanka ta sa mafi kyawun tufafinta.

Yayin da ta ji kusantowar ajali sai ta bukaci Asma’u da ta yi mata shimfida a tsakar gida, sai ta kwanta tana mai fuskantar alkibla. Sannan sai ta sa Asma’u da Ummu Aiman da su kira mata Imam Ali (AS). Da ya zo sai ta ce mishi:

Ya kai dan baffa, ina jin cewa kuma ni na zo karshe. Ba na jin wani abu face cewa ni zan hadu da babana a ‘yan sa’o’in nan. Ina so in yi maka wasici da abin da ke cikin zuciyata.

Sai Imam ya zauna daidai kanta, ya ce mata ta yi wasicinta. Ita kuwa sai ta ce masa:

Ya dan baffa, ba ka taba samu na da karya ko cin amana ba, kuma ban taba saba maka ba tun da ka zauna da ni.

Sai Imam (AS) ya ce:

Allah Ya sauwaka, ai ke ma kin sani, kin fi biyayya, kin fi takawa, kin fi karimci kuma kin fi tsoron Allah a kan in zarge ki da saba min. Hakika rabuwa da ke da rashinki sun tsananta gare ni. Sai dai haka wani abu ne da ba makawa a kan shi. Wallahi kuma kin sabunta min musifar rabuwa da Manzon Allah (SAWA), kuma hakika wafatin ki da rashin ki sun girmama Inna Lillah Wa Inna Ilaihi Raji’un! Wannan musifa me ya fi ta daga hankali da zafafa rai da bakin ciki!! Wallahi musifa ce da ba ta da makoki, kuma bakin ciki ne da ba shi da masauyi.

Sai duk suka yi ta kuka na wani lokaci, sannan sai Imam Ali (AS) ya kama kanta ya kai kirjinsa ya rungume ta ya ce:

Fadi wasiyyar da kika so, lallai za ki same ni mai cika ta, zan aiwatar da duk abin da ki ka hore ni da shi…

Sai Fatima (AS) ta ce:

Allah Ya saka maka da alehri. Ya kai dan baffa, da farko ina maka wasici da ka auri ‘yar ‘yar’uwata Umamah* a baya na, domin ita za ta kasance ga ‘ya’yana kamar ni; domin mata dole ne ga maza.

Haka yana daga abin da ta yi masa wasici da shi cewa:

Ina yi maka wasici da kar [ka bar] daya daga cikin wadannan da suka zalunce ni ya shaida jana’izata, kar ka bar wanin su ya yi sallah a gare ni. Ka bisne ni da daddare, lokacin da idanuwa suka natsu kuma gannai suka yi barci…[12]

Fatimatul-Zahra (AS) ta yi sallama da Ali (AS) da ‘yan gidanta, aka dauke ruhinta mai tsarki zuwa gidan dauwama.

Madina ta dauki zafi, zukatan Muminai sun buga saboda rasuwar reshen Annabci.

Mutane sun yi dandazo suna jira su ga an fito da Zahra zuwa makabarta; sai dai Imam Ali (AS) ya hori Salman -ko Abu Zarri – da ya sallami mutane, ya ce musu Fatima ta hana mutane su shaida jana’izarta. Haka gawarta mai tsarki ta saura har sai da idanuwa suka dauke sannan Imam Ali, Hasan, Husain, Ammar, Mikdad, Akil, Zubair, Abu Zarri, Salman, Baridah da wasu mutane daga Banu Hashim suka raka gawar zuwa Baki’a suka bisne ta a can, suka kuma boye duk wata alamar kabarin don kar mutane su sani.

Amincin Allah sun tabbata gare ta a ranar haihuwarta da ranar rasuwarta da ranar da za ta tashi a raye.

[1] Sahih al-Bukhari, juz’i na 5, shafi 48.

[2] Fakhruddin al-Razi, Tafsir al-Kabir. Wajen fassarar ayar Mubahala, sura ta 3 aya ta 61.

[3] Sahih al-Tirmizi, juzi’ na 2, shafi na 319; da Sunanu Abi Dauda, juz’i na 2, shafi na354; da Mustadrik al-Sahihain, na Hakim, juz’i na 4, shafi na 272.

[4] Bukhari, juz’i na 2, shafi na 185; da Masnad na Ahmad bin Hambali, juz’i na 4, shafi na 332.

[5] Nasa’i, cikin Khasa’isu Amirul-mu’minin. A ga ba kadan ne ma ya zo cewa: “Wanda ya cutar da Manzon Allah (SAWA) kuwa aikinsa ya baci.”

[6] Sayyid al-Husainy, cikin Siratul-Musdafah, bugu na 3, shafi na 205.

[7] Siratul-Mustafa, bugu na 3, shafi na 258.

[8] Dabari, cikin Zaha’irul-Ukbah, shafi na 30

[9] Sayyid Muhsin al-Amin, cikin al-Majalis al-Siniyyah, juz’i na 3, shafi na 83-84.

[10] Dabari, cikin Zakha’irul-Ukbah, shafi na 30 da na 31.

[11] Sayyid Abdul-Razak Kamonah, a cikin al-Nafahat al-Kudusiyyah fi al-anwar al-Fadimiyyah, fasali na 13, shafi na 45.

* Ita ce Fadima Ummul-Banin, mahafiyar Abul-Fadhal Abbas (AS). Ita ta nemi Imam Ali (AS) ya sauya mata suna daga “Fadima” da wani sunan daban; saboda ta lura duk lokacin da Imam ya kira sunanta, sai ta ga sauyi a fuskokin Hasan da Husaini, saboda sun tuna mahaifyarsu. Sai Imam ya sa mata Ummul-Banin (wato: Uwar ‘ya’ya).

[12] Sayyid Muhsin Amin, cikin al-Majalis al-Siniyyah, juz’i na 1, shafi na 123.

4- Imam Hasan Al-Mujtaba (a.s):
________________________

Shi ne babban jika, al-Hasan bin Ali bin Abi Talib. Mahaifiyarsa ce Fatima al-Zahra da tarihinta ya gabata. Daga abubuwan da muka ji na tarihin mahaifin shi (Imam Ali) da mahaifiyarsa (Zahra) nasabarsa da wannan madaukakin dangane ta gama bayyana.

Matsayinsa (AS)

Kamar sauran kebabbun ‘yan-gidan Manzo (SAWA), Imam Hasan (AS) na da madaukakiyar daraja a wannan addini. Musulmi ba sa sabani a kan cewa ayar tsakakewa ta kunshe shi, haka ayar ciyarwa, ayar kauna da ayar Mubahala; wadanda duk ambatonsu ya gabata.

A bakin Annabi (SAWA) kuwa an ji zantukan kauna, girmamawa da daukakar matsayin Imam Hasan daga gare shi. Bukhari da Muslim sun riwaito daga Barra’u bin أzib, ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya kasance yana dauke da Hasan bin Ali a kafadarsa alhali yana cewa:

Ya Allah ina sonsa, don haka Kai ma Ka so shi.[1]

Anas bin Malik ya ce: An taba tambayar Manzo (SAWA) cewa daga mutanen gidanka wa ka fi so? Sai yace: “Hasan da Husaini”.

Ummul-Mu’uminin A’isha ta ce: Manzon Allah (SAWA) ya kasance yana daukar Hasan ya rungeme shi sannan yakan ce:

Ya Allah wannan dana ne, kuma ni ina sonsa, to Kai ma Ka so shi, Ka kuma so mai sonsa.

Jabir bin Abdullah al-Ansari ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya ce:

Wanda ke son ya kalli shugaban matasan Aljanna sai ya kalli Hassan bin Ali.

Imam al-Ghazzali ya fitar da cewa: Manzon Allah (SAWA) ya cewa Hasan (AS):

Ka kamantu da ni a halitta da dabi’u.[2]

A wani wajen an riwato Annabi na cewa:

Hasan da Husaini Imamai ne sun mike (sun yi yaki don tabbatar da haka) ko sun zauna (ba su yi yaki ba).[3]

Haihuwarsa (AS)

An haifi Imam Hasan (AS) a ranar sha biyar ga watan Ramalan mai albarka, shekara ta uku bayan hijira. Farin ciki mai yawa ya lullube gidan Fatima da samun wannan abin haihuwa mai albarka. Nan da nan aka je aka yi albishir ga Manzo (SAWA).

Manzo ya yi matukar farin ciki da wannan abin haihuwa, nan da nan ya zo ya dauke shi ya rungume shi sannan ya yi kiran sallah a kunnen shi na dama, ya yi ikama a na hagu. Sannan ya dubi Imam Ali (AS) ya tambaye shi ko wane suna ya zaba masa. Imam ya ce: ‘Ai bai kamata in gabace ka ba ya Manzon Allah’. Sai Manzo ya ce: haka ni ma ba na gabaci Allah ba’. Wannan muhawara ba a dade da gama ta ba sai ga wahayi daga Allah na saukowa inda ake sanar da Annabi cewa: ‘Hakika Allah Ya yiwa abin haihuwa mai albarka suna Hasan’.[4]

Bayan kewayowar kwana bakwai da haihuwa:

Sai Manzo ya yi masa akika da babban rago, ya ba unguwar zoma cinya daya da dinari daya don godewa kokarinta.[5]

Dabi’u Da Halayensa (AS)

Jikansa Imam al-Sadik (AS) ya bayyana halayen Imam Hasan (AS) da cewa:

Hasan bin Ali ya kasance ya fi duk mutanen zamaninsa ibada, kuma ya fi su gudun duniya kuma shi ne mafificin su.[6]

Har ila yau Imam al-Sadik (AS) ya ce:

Hasan bin Ali (AS) ya tafi aikin hajji sau ashirin da daya a kafa…[7]

Ya kasance idan yana alwala sai a ga launinsa ya canza kuma gabubbansa na kakkarwa, sai aka tambaye shi dalilin haka, shi kuwa ya ba da amsa da cewa:

Hakki ne a kan duk wanda ya tsaya a gaban Ubangijin Al’arshi launinsa ya canza, kuma gabubbansa su kada.[8]

Ya kasance mai yawan taimakon mutane, ta yadda babu wanda zai tambaye shi wani abu face ya ba shi. Wata rana aka tambaye shi mai yasa koda yaushe aka tambaye shi abu sai ya bayar, sai ya amsa da cewa:

Hakika ni ma mai rokon Allah ne, kuma mai kwadayi gare Shi; don haka ina kunyar in zama mai roko alhali kuma ina hana mai roko. Kuma Shi (Allah) Ya sabar da ni da bayar da ni’imarSa gare ni, haka ni ma na sabar da Shi in bayar da ni’marSa (da Ya ba ni) ga mutane; to ina tsoron in na yanke al’adata Shima Ya yanke al’adarSa.[9]

Imami Dan Imami

A lokacin rayuwar mahaifinsa, Imam Hasan ya kasance, ba kawai da mai biyayya ba ne, har ma jami’i ne mai da’a. Ya halarci dukkan yakokin da mahaifinsa ya yi da azzalumai a Basra, Seffin da Naharwan; ya kuma taka muhummiyar rawa wajen kashe wutar fitina; ba don komai ba sai don kare Musulunci da mutanensa. Ya kuma wakilci mahafinsa a wurare da daman gaske.

Kafin Imam Ali (AS) ya bar duniya ya yi wasici a Imam Hasan (AS) a matsayin Imam. Ga abin da ya fada a lokacin da bakinsa:

Ya kai dana, hakika Manzon Allah (SAWA) ya hore ni da in yi wasici da kai kuma in ba ka littafaina da makamaina kamar yadda shi ya yi wasici da ni kuma ya ba ni littafansa da makamansa. Haka ya hore ni da in hore ka da cewa idan mutuwa ta zo maka ka bayar da su ga dan’uwanka Husaini.

Sannan ya waiwaya ya dubi Husaini (AS) ya ce:

Manzon Allah (SAWA) ya hore ka da ka bayar da su ga wannan dan naka…

Sai ya kama hannun Imam Ali Zainul-Abidin (AS) ya ce:

Kai kuma Manzon Allah (SAWA) ya hore ka da ka bayar da su ga danka Muhammad; ka isar da gaisuwa gare shi daga Manzon Allah da ni.[10]

Bayan shahadar Imam Ali (AS), a lokacin da Imam Hasan (AS) ya fito yana yiwa mutane huduba, yana sanar da su babbar masifa (ta rashin Imam); bai ko gama ba sai Ibin Abbas ya fara kiran mutane da su mika masa bai’arsu. Haka kuwa abin ya kasance, aka yi wa Imam Hasan Mubaya’a a matsayin Khalifa.

Labarin bai’ar da aka yiwa Imam Hasan ta girgiza Mu’awuya kwarai da gaske, don haka ne ma ya kira taron gaggawa tare da masu ba shi shawara a kan harkokin siyasa don samo hanyar da za a fuskanci sabon yanayin da aka shiga.

Masu taron sun dace a kan a dauki matakin watsa ‘yan leken asiri cikin garuruwan dake karkashin shugabancin Imam Hasan (AS), don cusa tsoro da yada karairayi don yin bakin fyanti ga hukumar Ahlulbaiti (AS). Haka taron ya bukaci da jam’iyyar Umayyawa ta fadada aikin jan hankulan shugabannin kabilu a Iraki, ta hanyar watsa rashawa da alkawuran karya da kyaututtuka da barazanoni da wasun wadannan.[11]

Sai dai kafofin tsaron gwamnatin Imam Hasan sun iya gano wannan makirci tun bai je ko’ina ba. Wannan ne ya haifar da musayar wasiku tsakanin Imam da Mu’awuya, amma hakan bai yi amfani ba; domin Mu’awuya ya dage a kan ci gaba da hamayya.

A karshe dai ya zama dole ga Imam Hasan (AS) ya shirya yaki da Mu’awuya; don haka ya fitar da bayanin da aka watsa mai cewa:

Bayan haka, lallai Allah Ya wajabta jihadi a kan bayinSa Ya kira shi da abin da ba a so. Sannan Ya cewa Ma’abuta jihadi daga Muminai: Ku yi hakuri, lallai Allah na tare da masu hakuri. Ya ku mutane, ba za ku iya samun abin da kuke so ba sai da hakuri da abin da ba ku so. Ku fita –Allah Ya yi muku rahma- zuwa rundunarku a Nakhila….[12]

Sai dai kunnuwan da wannan sako na Imam ya shige su sun riga sun fara tasirantuwa da kage-kagen Mu’awuya, don haka ba su yi kazar-kazar wajen amsa kiran jihadi ba.

Duk da haka wasu Muminai sun amsa wa Imam, suka tafi Nakhila –wani wuri dake wajen Kufah a kan hanyar zuwa Sham- don kama hanya zuwa arangama da miyagu.

A kan hanya ne, ana shirin yak,i sai irin tasirin aikin Mu’awuya ya fara bayyana cikin rundunar Imam Hasan (AS), wanda daga baya ma har ya gane akwai wadanda ke jira a fara yaki su kama shi su kai wa Mu’awuya cikin sauki ya san yadda zai yi da shi. Don haka sai ga sanarwar dakatar da yaki daga Imam Hasan (AS).

Wannan yanayin ne ya sa Imam Hasan ya amsa shirin sulhun da Mu’awuya ya yi kira da shi cikin wani mummunan yanayi. Yanayin da yaki ba zai taimaka wajen gyara shi ba sai ma dai kara gurbata al’amurra. Imam ya fadi dalilin karbar sulhun da ya yi da cewa:

Wallahi da na yaki Mu’awiya da sun riki wuyana har sun mika ni zuwa gare shi cikin ruwan sanyi. Wallahi in yi sulhu da shi ina madaukaki* ya fi min a kan ya kashe ni ina fursunan yaki; ko ya yi min gori, (hakan) ya zama abin zagi ga Banu Hashim.[13]

Ya kara da cewa:

Ban zama mai kaskantar da Muminai ba; sai dai ni mai daukaka su ne. Ba wani abu na yi nufi da sulhuna ba face kau da kisa daga gare ku yayin da na ga sandar Sahabbaina da nokewarsu daga yaki.[14]

Har ila yau ya taba fadawa Abu Sa’id cewa:

Ya kaiAbu Sa’id, dalilin sulhuna da Mu’awuya shi ne (irin) dalilin sulhun Manzon Allah da Bani Dhamrah da Bani Ashaja’a da mutanen Makka, a lokacin da ya koma daga Hudaibiyya.[15]

Sulhun Imam Hasan Da Mu’awuya

Abin da wannan yarjejeniya ta kunsa shi ne cewa shi Mu’awuya ya yi aiki da Littafin Allah da Sunnar ManzonSa. Haka sulhun ya tanadi cewa kar Mu’awuya ya nada kowa a matsayin mai jiran gadonsa. Kuma Mu’awuya ya dauki alkawari tsakanin shi da Allah cewa ‘yan Shi’ar Ali za su zama cikin aminci na rayukansu da dukiyoyinsu, matansu da ‘ya’yansu.

Sai dai tun farko Imam Hasan (AS) na so ne ya fitar da hakikanin Mu’awuya kowa ya gan shi ta hanyar wannan sulhu. Wannan kuwa shi ne abin da ya faru; domin Mu’awuya ya sabawa duk tanaje-tanajen sulhun. Bai yi aiki da Littafin Allah da Sunnar Manzo ba, kuma ya rika kashe bayin Allah da zababbun wannan al’umma, ya rika zaluntarsu da kwace dukiyoyinsu, ya watsa fasadi mai yawa a doron kasa.

A Kufah ne Mu’awuya ya mike ya yi hudubar nan tasa da ya bayyanawa duniya ko shi wanene; yayin da ya ce:

Wallahi ni ban yake ku don ku yi sallah ko azumi ko hajji ko zakka ba, domin ai kuna yin haka; na dai yake ku ne don in mulke ku, hakika kuma Allah Ya ba ni hakan alhali ku ba ku so. To ku saurara duk wani jini da aka zubar a wannan fitina ya tafi a banza, kuma duk wani alkawari da na dauka yana karkashin kafafuwan nan nawa guda biyu[16]

Bayan sulhun ne Imam Hasan ya kuduri aniyar komawa Madina gefen Kakan shi (SAWA), ya koma can ya ci gaba da aikin shi na Imamanci (wanda ba ya kwatuwa). Inda ya koma ya shiga ja-gorancin tunani. Hakika kuwa zamansa na Madina bayan sulhun ya haifar da manyan masana Musulunci da gawurtattun masu riwayar hadisi.

Zuwa Mihrabin Allah

Mahukuntan Umayyawa ba su zama cikin jahilcin ma’anar komawar Imam Hasan Madina ba. Suna sane da cewa zai koma ne wajen yada addini. Wannan ma babbar matsala ce gare su. Don haka sai suka fara makiricin raba shi da duniya. Amma sai suka fara daukar matakan siyasa kafin aiwatar da wancan mummunan kuduri na su na karshe.

Matakin farko shi ne kuntatawa ‘yan Shi’ar Ali (AS), suna Koran su, suna toshe hanyoyin abincinsu, rushe giajensu da sauran irin wadannan. A kan haka gwamnatin Umayyawa ta sami taimakon miyagun gwamanoninta da jam’ianta irin su Mugirah bin Shu’ubah, Samrata bin Jundubi da Zaiyad bin Abihi.

Ziyad ya kasance dan zina ne, don haka ne ma ake kiran shi Ibin Abihi (dan babansa), kuma shi ne gwamnan Umayyawa a Iraki. Mugu ne na karshe, tarihi ya hakaito cewa:

Ziyad ya rika bin ‘yan Shi’ar Ali bin Abi Talib yana kashe su ko’aina har sai da ya kashe talikai masu yawa daga cikin su. Ya shiga yanke hannuwansu da kafafunsu, yana tsire idanuwansu. Ya zama yana rudin Mu’ayuwa da –samun kusanci da shi- da kashe su.[17]

Haka Mu’awuya ya yi amfani da wasu masu wa’azozi masu mika wilaya ga masu mulki, wajen gurbata tarihin Ahlulbaiti masamman Imam Ali (AS). Abu Huraira –mashhurin mai riwayar hadisan nan- ya yi matukar taimaka musu a wannan fagen.

Mu’awuya ya sa zagin Imam Ali (AS) ya zama al’ada a bisa mumbarorin Musulmi da hudubobin juma’a. Banda hadisan karya da ya sa aka yi ta cusawa kasashen Musulmi masu batanci ga addini da wadanda za su mara masa baya. Wadannan hadisai na Mu’awuya har yanzu suna nan cike da littafan Musulmi, masamman Ahlulsunna, suna aiki da su a matsayin hadisan gaskiya, alhali mafi yawan su ba su sani ba.

Karshe shirin su shi ne kashe Imam Hasan (AS) da guba da Mu’awuya ya shayar da shi ta hanyar matarsa (Imam din) wadda ake kira Ja’adatu. Wadda kuma Mu’awuya ya rude ta, ya hure mata kunne, bisa alkawarin cewa daga baya zai aurar mata da dansa Yazidu.*

Imam Hasan ya sha gubar ne cikin madarar da ya yi bude baki da ita bayan ya kai azumi. Ya rika yin tari har hantarsa na fitowa ta bakisa. Inna lillah Wa inna Ilaihi raji’un.

Shahadarsa ta kasance a ranar bakwai ga watan Safar, shekaru hamsin bayan hijirar Kakansa (SAWA).

Imam Hasan ya yi wasici da a bisne shi a kusa da Kakan shi Annabi. Sai dai Umayyawa, karkashi ja-gorancin Marwan bin Hakam, sun hana a bisne jika a kusa da Kakansa kuma masoyinsa, shugaban samarin gidan Aljanna. Don haka sai aka bisne shi a Baki’a kusa da kabarin kakarsa Fatimatu bint Asad, mahaifiyar Imam Ali (AS).

Amincin Allah ya tabbata gare ka a raye da mace, ya kai Abu Muhammad wanda aka zlunta.

Imam Hasan ya rasu ya bar ‘ya’ya da dama; kuma wasu daga cikin su sun yi shahada tare da baffansu Imam Husaini (AS) a Karbala.

[1] Bukhari da Muslim da Tirmizi, wajen ambaton Imam Hasan (AS).

[2] Ghazzali, cikin Ihya’u Ulum al-Din.

[3] Don neman karin bayani kan wadannan nassosi da wasun su masu kama da su, ana iya komawa: Kashful-Gummah, juz’i na 2; al-Majalis al-Siniyyah da Tazkiratul-Khawas. Da wasun su masu yawa.

[4] Taufik Abu Ilm, cikin Ahlul-bait, shafi na 264.

[5] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 98.

[6] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 100.

[7] Inada aka ambata a sama, shafi na 98.

[8] Inada aka ambata a sama.

[9] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assasar al-Balagh, shafi na 101.

[10] Sheikh al-Dabrisi, cikin I’ilam al-Wara, shafi na 206; da Kashf al-Gummah fi Ma’arifatul-A’immah, juz’i na 2, shafi na 155.

[11] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 105.

[12] Ibin Abil-Hadid, cikin Sharh Nahjul-balagha, juz’i na 6, shafi na 38.

* Zancen daukaka (Izza) ya saura tsaikon yunkurin Ahlulbaiti (AS). Imam Husaini ya yaki Umayyawa don Izza haka Imam Hasan ya yi sulhu da su don wannan. Manufar yunkurin wadannan Imamai biyu na kore duk wani sabani a tsakaninsu. Manufarsu daya, hanyarsu daya kuma makiyansu daya. Zamunanu ne suka sassaba, wanda haka ya tilasta daukar matakin da ya dace da kowane yanayi. To ai Imam Husaini na nan a lokacin sulhun, kuma ya taimaka wajen ganin manufofin sulhun sun tabbata.

[13] Al-Karashi, cikin Hayat Imam Hassan, juz’i na 2, shafi na 281.

[14] Al-Karashi, cikin Hayat Imam Hassan, juz’i na 2, shafi na 281

[15] Inda aka ambata a sama.

[16] A’atham al-Kufi, a cikin, al-Futuh, juz’i na 4, shafi na 161.

[17] Inda aka ambata a sama, shafi na 203.

* Sai dai bayan Ja’adatu ta aiwatar da bukatar Mu’awuya, daga baya da ta nemi cika alkawari Mu’awiya bai cika mata ba. Ya kafa mata hujja da cewa: ‘Mai hankali ba ya auren wadda ta kashe mijinta’. Haka wannan ja’ira ta ga tabewa tun a duniya.

5- Imam Husain Shahidin Karbala (a.s):
________________________

Sanin cewa Imam Husaini (AS) kane yake ga Imam Hasan ya isa ya sanar da mutum danganensa. Domin tushensu daya da Imam Hasan (AS). Uwa Fatima ‘yar Manzon Allah, Uba Ali dan Abi Dalib kuma Kaka Manzon Allah (SAWA). Magana ta kare.

Haihuwarsa (AS)

An haifi Imam Husaini a ranar uku ga watan Sha’aban na shekarar hijra ta hudu. Haihuwarsa ta karo haske da farin ciki a gidan Annabi (SAWA), domin albishirin haihuwarsa na isa wajen Manzo ya gaggauta zuwa gidan Fatima (AS), ya cewa Asma’u bint Umais: “Ya Asma’u kawo min dana”. Da Asma’u ta kai shi ga Manzo (SAWA), sai aka ga albishir a fuskarsa. Sai ya yi masa huduba, bayan ya gama sai ya dora shi a cinyarsa, sai aka ga (Manzo) na kuka. Sai Asma’u ta tambaye shi dalilin kukansa sai ya ce mata: “saboda wannan dan nawa”. Sai Asma’u ta yi mamaki, ta ce: “dazun nan fa aka haife shi!” A nan ne Manzo (SAWA) ya habarta mata cewa:

Ya ke Asma’u, kungiyar nan ta azzalumai za ta kashe shi a baya na. Allah ba zai hada su da cetona ba.

Daga nan sai ya ja kunnen Asma’u a kan yada wannan labari, ya ce:

Ya Asama’u, kar ki ba Fatima wannan labarin, domin ba ta dade da haihuwarsa ba.[1]

Daga nan sai Manzon Allah ya hori Imam Ali (AS) da ya sa masa suna Husaini, bisa horon Allah.

Matsayinsa (AS)

Wasu daga cikin darajojin da muka ambata a baya ga Fatima, Imam Ali da Hasan duk Husaini na da su; wannan ya hada da shigarsa cikin wadanda Ayar Tasarkaewa ta sauka a kansu; haka nan Ayoyin Ciyarwa, Mubahala da sauransu.

Haka wasu daga darajojin da muka ambata dangane da wansa Imam Hasan a darussan da suka gabata, shi ma yana da su, kamar hadisin da ya siffanta su da ShugabanninSamarin Aljanna.

Kari a kan wadannan, Salman al-Farisi ya ce: na ji Manzon Allah (SAWA) na cewa:

Hasan da Husaini ‘ya’yana ne, wanda ya so su ya so ni, wanda kuma ya so Allah zai so shi, wanda kuwa Allah Ya so zai shigar da shi Aljanna. Kuma wanda ya fusata su ya fusata ni, wanda kuma ya fusata ni Allah zai yi fushi da shi, wanda kuwa Allah Ya yi fushi da shi zai shigar da shi wuta.[2]

Imam Zainul-Abidin (AS) ya riwaito daga mahafinsa, daga kakansa ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya taba kama hannun Hasan da Husaini ya ce:

Wanda ya so ni ya kuma so wadannan biyun da babansu da mamansu, zai kasance tare da ni ranar kiyama.[3]

A wani wuri kuma ya ce:

Husaini daga gare ni ya ke ni kuma daga gre shi nake. Allah Ya so wanda ya so Hussaini.[4]

Dabi’unsa (AS)

Wanda ya kasance karkashin tarbiyyar kakansa (SAWA) da mahafansa (Ali da Fatima AS); ya kuma tashi tare da wa irin Imam Hasan (AS), wane irin hali za ka samu daga gare shi! Ya kasance wajen misalta sakon Allah madaukaki a tunani, aiki da dabi’u. Shu’aib bin Abdul-Rahman ya riwaito cewa:

An ga wani tabo a bayan Imam Husaini (AS) a Karbala; sai aka tambayi Imam Zainul-Abidin game da shi, sai ya amsa da cewa: “wannan ya sabo asali ne daga buhunan abinci da yake dauka a bayansa yana kaiwa gidajen matan da mazansu suka mutu da marayu da miskinai.[5]

A daren goma ga watan Muharram din da ya yi shahada, Imam Husaini (AS) ya bukaci rundunar Umayyawa ‘yan hamayya da su jinkirta masa wannan daren saboda:

Muna so mu yi sallah ga Ubagijinmu a wannan daren, mu kuma nemi gafararSa, Shi kuwa Ya san ina son sallah gare shi da karatun LittafinSa da yawaita addu’a da istigfari.

Husaini Mai Kariya Ga Musulunci

Imam Husaini (AS) na da gudunmwar da ta saura bashi a wuyan wannan al’umma ta ci gaba da gode masa a kai. Domin da wuri ya fara bayar da taimakonsa ga wannan addini, wannan kuwa tun lokacin mahaifinsa Imam Ali, da gefen da’uwansa Imam Hasan.

Bayan shahadar yayansa ne aikinsa na addini ya dauki wani sabon salo daidai da yadda yanayin rayuwar al’umma ya sauya.

Hakika Imam Husaini ya rayu a wani yanayi da ya fi na duk wadanda suka gabace shi da wadanda suka zo bayan shi wuya, wajen kalubalantar makirce-makircen Umayyawa bayan sulhunsu da Imam Hasan (AS). Domin kuwa ta’addaci ya yadu, aka wahalar da duk wanda ya bayyana ‘yar hamayya komai karancinta ga mulkin banu Umayya karkashin mulkin Mu’awuya da dansa Yazid. Shi’ar Ahlulbait (AS) ne suka fi wahala a wannan hali. Imam Al-Bakir (AS) ya siffanta wannan masifa da fadarsa:

Sai aka kashe Shi’armu a kowane gari. Aka yanke hannuwa da kafafu a bisa zato. Ya kasance duk wanda aka ji yana kaunar mu da zuwa wajen mu za a jefa shi a kurkuku ko a kwace dukiyarsa ko a rushe gidansa. Haka al’amarin ya ci gaba da tsananta da karuwa har lokacin Ubaidullahi bin Ziyad, wanda ya kashe Husaini.[6]

Ibin Athir ya ambaci cewa:

Ziyad –gwamnan Mu’awuya a Kufa- ya wakilta Samrata a Basra cikin mafi yawan kashe kashe da aka yi a can. Ibin Sirin ya ce: ‘Samrata ya kashe mutum dubu takwas a bayan idon Ibin Ziyad, sai Ibin Ziyad ya ce mishi: Kana jin tsoron ko wata kila ka kashe wanda bai ji ba bai gani ba? Sai ya ce: da ace na kashe irinsu tare da su da ban ji tsoro ba’. Abul-Siwari al-Adawi ya ce: ‘A dare daya Samrata ya kashe mutum arba’in daga mutanen da dukkan su mahardata AlKur’ani ne’.[7]

Haka nan mahukuntan na Umayyawa sun yi matukar yin amfani da dukiya wajen sayen hankulan mutane, lamirinsu da addininsu; kai har ma sun sayi wasu masu wa’azi da masu riwayar hadisi, wadanda ke da hannu dumu-dumu wajen barranta barnace barnacen Mu’awuya ta hanyar kirkiran hadisan karya da dangana su ga Manzo (SAWA), don girmama shi da cin zarafin jikokin Ma’aiki .

Ga su kuma ba su daina dabi’ar nan ta su da suka kasance suna yi tun lokacin Imam Hasan (AS) ba, na wasa da dukiyar al’umma.

Yanayin zamantakewa ma bai kasa yanayin siyasa da na tattalin arziki wajen tabarbarewa ba. Domin mahukuntan sun rungumi siyasar raba-ka-mulka, yayin da suka daidaita al’umma ta hanyar tayar da kurar kabilanci da bangaranci. An san su da yada dabi’ar nan ta fifita larabawa a kan wadanda ba larabawa ba daga Musulmi ba tare da wani dalili ba.

Ga su, kamar yadda ya gabata, su suka kashe Imam Hasan (AS) wanda shi ne shar’antaccen shugaban ingantaccen bangaren Musulmi a duniyar Musulunci.

Yazidu Dan Mu’awuya

A karshe Mu’awuya ya lankayawa mutane dansa Yazid, fajiri, fasiki, mashayin giya kuma dan caca, a matsayin shugaba gare su. Wannan kuwa ya faru ne ta hanyar nuna fin karfi, kumbiya-kumbiya da yaudara.

Wadannan al’amurra duk sun sa makomar al’ummar Musulmi cikin matsanancin hadari, wanda matukar ba a yi wani abu ba Musulunci zai zama sai sunansa. Domin da an koma jahiliyya danya cakal.

Dabi’un Yazid kawai sun isa su gama da Musulunci daga farkonsa. Dubi abinda tarihi ke fada game da shi:

An riwaito cewa Yazid ya shahara da wasan kade-kade, shan giya, wake-wake, farauta, yawo da matasa da karnuka da birai. Babu ranar da za ta wayi gari face yana cikin giya. Ya kasance yana daure biri a kan doki bisa sirdi ya rika jan shi. Yana kuma sanya wa birai hulunan zinari. Idan biri ya mutu yana yi mishi makoki…[8]

Idan har haka ya zama shi ne halin Khalifa, ya ya halin na kewaye da shi zai kasance? Mas’udi ya fitar da bayanin haka da cewa:

Irin fasikancin da Yazid ke aikatawa ya yi galaba a kan na kusa da shi da gwamnoninsa. A ranakunsa ne wake-wake suka bayyana a Makka, aka yi ta holewa, mutane suka bayyana shan giya (a fili)[9]

Wannan lalataccen Khalifa da Mu’awuya ya tilastawa Musulmi shi a wuyansu, ta hanyar da ta sabawa ka’idojin Musulunci da dokokinsa ya daga hankalin al’ummar Musulmi masamman masu fada-a-ji a cikin mutane. Wannan kuma ya budewa tarihin Musulunci wani sabon sahfi –mawuyaci. Al’umma ta wayi gari ba ta da mafita sai dayan biyu:

1-Ko dai ta mika kai bori ya hau, wannan kuwa zai tilasta mata yin sakwa-sakwa da addininta da yin kunnen-uwar-shegu da sakonta da zubar da mutuncinta da daukakarta a wannan rayuwa.

2-Ko ta dauki matakin hamayya ta daura damarar yaki da fasadin da aka lankaya mata.

Sanannen abu ne cewa Imam Husaini wanda yake tarbiyyar gidan Annabci kuma mai matsayi na Imamanci, a irin wannan yanayi, ba shi da wani uzuri in ba shiga gaba wajen hamayya da kokarin tsige wannan barna daga tushenta ba. Wannan shi ne abin da ya haifar da masufar Karbala.

Ilai kuwa, ba don yunkurin Husaini (AS) ba da yanzu Musulunci na nan cakude da dabi’un Umayyawa.

Ya bayyana manufar yunkurinsa yayin da wasu marasa hangen nesa suka rika neman hana shi. Wadancan sun kasa fuskantar inda Imam Husaini ya sa gaba saboda irin gurbatacciyar fassararsu ga Musulunci. Imam ya ce musu:

Hakika ni ban fito alhali ina mai kangarewa gaskiya ko mai neman barna ko azzalumi ba, na dai fito ne don neman kawo gyara cikin al’ummar kakana (Manzon Allah SAWA). Ina so in yi horo da aikin kirki in yi hani da mummuna in kuma bi hanyar kakana da da babana Ali dan Abi Dalibi

Mafarin Al’amarin

Mu’awuya ya koma makomarsa a tsakiyan watan Rajab na shekara ta sittin bayan hijra ba tare da ya iya karbar bai’ar wasu gwaraza daga Musulmi ba, a gabansu akwai Imam Husaini (AS); illa ya bar tsarin cewa mahukunta su ci gaba da karbar bai’a da karfi ga Yazid.

Cikin gaggawa Yazid ya aikawa gwamnansa na Madina, Walid bin Utbatah, cewa ya karbar masa bai’a daga mutanen Madina masamman Imam Husaini (AS), saboda masaniyar da Umayyawa ke da ita na kasancewarsa tsayayye wanda ba ya girgiza, kamar dai mahaifinsa da wansa.

Kamar kuwa yadda suka yi hasashe, Imam Husaini (AS) ya ki biyan bukatarsu, inda ya fito fili ya bayyana kin bai’a ga Yazid yana mai cewa:

Yazidu mtum ne fasiki, mashayin giya, mai kashe rai ba bisa hakki ba, mai bayyana fasikanci; iri na ba zai yi mubaya’a ga irinsa ba.[10]

Saboda ba kowa ke ja-gora ba, a irin tarbiyyar da Husain (AS) ya samu, illa masu siffofin da ya bayyana a fadarsa da cewa:

Wallahi ba kowa ke shugaba ba face mai hukunci da AlKur’an, mai tsayar da adalci, mai riko da addinin gaskiya mai iyakance kan shi da Zatin Allah[11]

Wannan ne ya shata jan layin da ya haifar da zubar da jinin Imam a Karbala, shi da ‘ya’yan shi, ‘ya’yan dangin shi da Sahabban shi a ranar Ashura. Domin Yazid ya dage kan cewa dole a karbar masa bai’ar Imam Husaini ko a zo masa da kansa, sabanin wasicin da Mu’ayuwa ya yi gare shi na cewa kar ya yi amfani da karfi (a kan Imam Husaini) don ya san kwanan zancen, kamar yadda mai begen Ahlulbaiti ya furta cewa:

In ko kana bidar ka san jarintarsa sanin yakini

Ka tambayi Mu’awuya da dan أsi sui ma bayani

Don su suka ja da Imamu Ali aka fid da raini

A gaida ki-gudu kuma sa-gudu Abbul-Hasanaini.[12]

Wasu riwayoyin tarihi sun bayyana cewa yayin da Walid ya nemi kawo gardama a sakamakon kin mika mubaya’a da Imam Husaini (AS) ya yi, da kyar mutane suka kwace shi a hannun Imam Husaini (AS).

Iraki Da Mutanenta

Bayan abin da ya faru, Imam Husaini (AS) ya hada ‘yan’uwansa da danginsa don zuwa aikin Hajji a ranar 3 ga watan zul-hijjah. A daidai lokacin, mutuwar Mu’awuya da hawan Yazidu kan mulki ya yadu a ko’ina, tare da labarin tarnakin da ya faru tsakanin sababbin azzalumai da Imam Husaini da labarin fitarsa daga Madina zuwa Makka. Wannan ne ya sa Imam ya shiga samun wasiku daga yankuna dabam daban masamman daga Kufah, wadanda ke kawo kukansu gare, shi a matsayin shi na Imami. Imam kuma ya rika aika musu da amsoshin dake kunshe da kiransu zuwa wajibcin yunkurawa da taimakon gaskiya. Yayin da Imam ya ga yawan wasikun mutanen Kufah, wadanda adadinsu ya wuce dubu sha biyu, sai ya aika musu da dan baffansa Muslim bin Akil don ya zama wakilinsa a cikin su kafin ya iso gare su. Muslim bin Akil, bayan ya isa Kufah, ya sami daman karbar bai’ar mutane da dama ga Imam Husaini (AS) na da’a da jurewa wajen yakar zalunci da kawar da fasadi. An ce cikin ‘yan kwanaki kadan ya karbi bai’ar mutane kusan dubu tamanin. Ya kasance yana samun daman sadarwa da Imam Husaini ta hanyar musayar wasiku; don haka ne ma ya gaya wa Imam irin ci-gaban da aka samu.

Da farko Muslim ya sauka a gidan wani dan Shi’a mai suna Mukhtar bin Ubaidullah al-Thakafi.

A bangaren azzalumai kuwa, labarin halin da Kufah ke ciki ya isa ga Yazidu, hangen irin hadarin da kujerarsa ke fuskanta ne yasa har ya canza gwamnansa na Kufah, wanda bai iya yin wani katabus wajen murkushe yunkurin da ke tasowa ba. Sai wani mai ba Yazid shawara ya ba shi shawara da ya aika musu da Ubaidullahi bin Ziyad, wanda ke Basra kuma wanda ya shahara da rashin tausayi, iya kisan kai da bakar kiyayyarsa da jikokin Ma’aiki (SAWA). Sai Khalifa ya yi haka kuwa, ya aika yana ba shi labarin halin da ake ciki, da cewa ya hada masa Kufah da Basra matukar har ya iya kashe Muslim bin Akil.

Cikin gaggawa Ibin Ziyad ya shiga Kufah tare da runduna mai dakaru dari biyar, tare da wasu shugabannin Basra dake da karfin fada-aji a kan wasu mutanen Kufah saboda kusancin dake tsakaninsu.Ya bar shugabancin Basra din a hannun dan’uwasa kafin ya dawo. Yana shiga Kufah sai ya tara mutane ya yi musu bayanin shi na farko dake kunshe da tsoratarwa a kan ukubar da bata kasa kisa ba. Sannan ya hado kan shugabannin kabilu tare da shi, ya sa su kawo masa sunayen duk wadanda suka fita daga yiwa iyalan Abu Sufyan biyayya.

Wannan ya sa Kufah ta shiga wani hali na firgita da rashin tabbas, al’amari ya birkice, mizani ya juya yayin da aka shiga kashe ‘yan Shi’ar Ahlulbaiti (AS) da wadanda suka mika wilaya ga yunkurin Imam Husaini na kawo gyara.

Ta hanyar ‘yan leken asirin da ya cika Kufah da su, Ibin Ziyad ya yada cewa akwai wata babbar rundunar Umayyawa a kofar Kufah*. Wannan farfaganda ta yi matukar yamutsa Kufah, abin da ya sa uwa na hana danta fita, mata na sa mijinta ya gudu, uba na tsawatar da dansa, wa na hana kaninsa.[13]

Kwadayi da tsoro sun yi matukar tasiri wajen janyewar mutanen Ibin Akil, ta yadda babu wanda ya saura tare da shi sai wasu ‘yan tsiraru masu tsarkin niyya da istkama, wadanda suka buya a wani yanki da ake kira al-Kindah da ke Kufah.

A karshe dai al’amarin ya kai ga sai da bangarorin biyu suka hadu, inda aka gwabza, Muslim ya nuna bajintar gidan Annabci a wajen, har zuwa lokacin da raunuka suka yi mishi yawa, abin da ya haifar da kama shi aka kai shi wani dogon gini a Kufah a jeho shi zuwa kasa. Inna lillahi wa inna ilaii raji’un. Haka Muslim ya cika yana shahidi a tafarkin Allah da ManzonSa. A tare da shi an kashe Hani bin Urwa wanda ya kasance cikin manyan Kufah, wanda ya taimaki Muslim suka karfafa shi har zuwa karshen rayuwarsu. Amincin Allah Ya tabbata a gare su baki daya.

Imam Husaini (AS) kuwa ba shi da labarain abin da ke faruwa a Kufah, amma ya san ba lafiya ba, saboda an dauki lokaci bai sami bayani daga wajen Muslim ba.

Da ma shi ma ya yanke aikin hajinsa a lokacin da ya fuskanci cewa Yazid ya turo wasu mutane da su kashe shi koda yana rataye a kyallen Ka’aba, mutanen suna nan cikin harami kamar mahajjata, kunshe da makamai a tare da su. Shi kuma ba ya so a keta hurumin Daki mai alfarma a Wata mai alfarma da jininsa. Ya bar garin Makka cikin sanin yadda al’amaurra za su kare, kamar yadda ya yi ta bayyana haka a cikin hudubobinsa masu yawa.

A ranar 8 ga watan zuj-hijjah na shekara ta 60 bayan hijra Imam ya kama hanyar Iraki. A kan hanya ne ya rika neman karin bayani a kan halin da mutanen Iraki ke ciki, ya rika samun amsar da ke cewa: “Takubba na tare da Umayyawa yayin da zukata ke tare da kai”. Wannan ya sa Imam ya san cewa al’ummar nan ba za ta fadaka ba sai wani babban abu ya girgiza ta! Don haka bari shahadarsa da wadanda ke tare da shi na daga zuriyyar gidan Annabci ta zama na’urar girgizawa.

A Karbala

A ranar 2 ga wata Muharram mai alfarma na shekara ta 61 bayan hijra Imam Husaini (AS) da Sahabbansa da mutanen gidansa suka isa sararin saharar Karbala. Wannan sararin sahara da zai zama ‘tsiako’ ga ‘yantattu kuma ‘take’ ga masu yunkurin kawo gyara a tsawon tarihi.

Mahukuntan Umayyawa kuwa, karkashin Ubaudullahi bin Ziyad a Kufah, sun hada wata runduna mai karfin gaske karkashin ja-gorancin Umar dan Sa’ad bin Abi Wakkas. Da farko Umar bin Sa’ad ya ki amincewa ya shiga cikin wannan ta’asa, saboda masaniyar da yake da ita da matsayin Imam Husaini (AS). Amma daga baya sai zuciya ta galabci hankalinsa, saboda barazanar da ibin Ziyad ya yi na kwace mulkin Rayyu daga hannunsa. An ji Umar bin Sa’ad na fadar irin yakin son-zuciya da hankali da ya shiga ciki a baitocin dake cewa:

Shin zan bar mulkin Rayyu alhali ita nake kwadayi

Ko zan koma abin zargi ne ta hanyar kashe Husaini

A cikin kashe shi akwai wuta wadda a tare da ita

Babu shamaki, alhali ga mulkin Rayyu sanyin ido

Da karshe dai ya mika wuya ga son-zuciya ya karbi aikin, ya ja rundunarsa mai mayaka dubu hudu. Bayan ya isa Karbala ya nemi Imam Husaini (AS) ya mika kai bori ya hau ba tare da yaki ba. Amma Imam Husaini (AS) ya san abin da yake yi kuma don me yake yi, don haka ba ja da baya, wannan ya sa ya watsa bayanin matsayinsa cikin hikima don amfanin ‘yantattu:

Ni ba na ganin mutuwa face dacewa, rayuwa da azzalumai kuwa (ba komai ba ce) sai kunci da tabewa.

Bai gushe ba yana bayyana yakeuwar nan da ya gada daga kakansa (SAWA), yayin da ya yiwa sojojin Umayyawa huduba da cewa:

Manzon Allah (SAWA) ya ce: “Duk wanda ya ga ja’irin mai mulki, mai halatta abin da Allah Ya haramta, mai karya alkawarinSa, mai sabawa sunnar Manzon Allah (SAWA), yana aiki, a cikin bayin Allah, da sabo da kiyayya; sannan [wanda ya ganin] bai canza abin da [mai mulkin]ke kai da aiki ko da magana ba, Allah na da hakkin Ya shigar da shi mashigarsa [azzalumin].[14]

Da mutanen suka ki ji suka kangare, Imam ma sai ya ki sai yakarsu.

Daren Ashura

Imam Husaini (AS) ya bukaci dan’uwansa Abul-Fadhal Abbas da ya yi yarjejeniya da abokan gaba da su ba shi zuwa tsawon daren goma ga watan Muharram kafin ya ba su kudurin shi na karshe a safiyar goma ga wata. Ba ya nemi wannan jinkiri ne don yin tunani ba, domin ya gama wannan tuni, ya yi haka ne don ya yi amfani da wannan dare –wanda shi ne daren shi na karshe a duniya- wajen ibada, addu’a, wasiyya ga dangi da masoya da sallama. Saboda yana sane da abin da ke tafe. Ga nassin abin da ya ce wa Abbas:

Koma gare su, in za ka iya, ka sa su jinkirta mana zuwa gobe. Ka kore mana su zuwa wayewar gari, ko ma samu mu yi sallah ga Ubangijinmu a wannan daren mu kuma roke Shi, mu nemi gafara daga gare Shi; domin kuwa Shi Ya san na kasance mai son sallah da karatun LittafinSa da yawan addu’a da istigfari[15].

Haka kuwa aka yi. A daren nan babu abin da ka ke gani a tsakanin mutanen Imam Husaini (AS) da sauran zuriyyar gidan Annabci da mabiyansu daga mai sallah sai mai addu’a da mai karatun AlKur’ani, istigfari, sai mai yin wasici da sallama da dangi, ‘ya’ya da mata. Suka shiga gyaran makamansu da tanajin haduwa da Ubangijinsu.

A wannan dare Imam Husaini (AS) ya yi sallama da iyalansa, danginsa da masoyansa. Ya ziyarci Imam Sajjad (AS) da Sakina da Laila, da jikansa jariri Muhammad al-Bakir. Ya yi wasiyyoyinsa alhali yana mai mika wuya ga hukuncin Allah da kaddararSa.Ya sayar da kansa ga Allah. Ya kudurta shayar da bishiyar shiriya da imani da jininsa da ransa.

Ranar Ashura

Kamar ina ganin Umar bin Sa’ad yana gyara sojojinsa, wadanda suka rika karuwa kullum a duk tsawon makon da suka yi a sararin Karbala. Yana aje kowa a matsayinsa don yakar dan ‘yar Manzon Allah (SAWA), kuma na biyar daga Ahlulbaiti tsarkaka, wadanda Allah Ya farlanta kaunarsu da mika wilaya gare su a kan wannan al’umma da nassin AlKur’ani mai girma.

Kamar ga ni ga Imam Husaini (AS) yana shirin yaki da ‘yar karamar rundunarsa mai mayaka tsasa’in da wani abu, amma wadda imaninta ke haske rana da abin da ta haska. Ga shi nan (AS) yana kange tantunansa da ya kunshi mata da kananan yara. Ya sa a haka rami a kewaye tantotin. Ya sa a kunna wuta a ramukan don kar makiya su iya samun daman cutar da wadancan raunana.

Ga Imam nan ya fuskance su yana kiransu yana tunatar da su da AlKur’ani da Sunna, yana tuna musu alkawarinsu; amma ina! Sun yi nisa ba sa ji kira!! Imam bai gajiya ba, ga shi nan ya sake daukar AlKur’ani mai girma ya bude shi a hannuwansa biyu ya na ce musu:

Ya ku wadannan mutane, tsakani na da ku akwai littafin Allah da Sunnar kakana (SAWA).

Amma ba wanda ya ce uffan!! Sai ma Umar bin Sa’ad da ya sa mai rike da tutarsa ya gabata. Ya kunna wuta da hannusa a kan kwari ya harba kibiya ta farko ya ce: “Ku yi min shaida a wajen sarki cewa ni ne farkon wanda ya harba kibiya a rundunar Husaini”.

Duk da cewa an kashe masa kusan duk wani mai karfi a rundunarsa. Daga ‘ya’ya irin su Ali al-Akbar da Ali al-Asgar sun fadi. Daga dangi ga gwarzon gidan Annabi nan Abul-Fadhal Abbas babu hannuwa a kwance. Ga Kasim nan, dan Imam Hasan mai shekaru sha biyu da haihuwa, kwance cikin jinin Shahada. Ga jaririnsa nan Abdullahi dan wata shida da haihuwa, wanda kishirwa ya kafar da nonon uwarsa, Imam ya mika musu shi da nufin su shayar da shi ruwa, sai suka yi masa ruwan kibau suka kashe shi a hannun mahaifinsa. Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un!! Daga Sahabbai ga su Muslim bin Ausajah nan sun fadi, su Habibu bin Mazahir na kwance ba rai. Daga wadanda suka tuba suka dawo gaskiya daga rundunar arna akwai Hur bin Ziyad al-Riyahi. Ga su wane…. da su wane… duk ba su.

Kamar gani ina kallon Imamina (alaihi afdhallul-salati wa azkas-salami) ya daga hannu sama yana ganawa da Ubangiji da cewa:

Ya Allah Kai ne amincina ga kowane bakin ciki, kuma Kai ne fatana a cikin kowane tsanani, kuma Kai ne amincina da tanajina cikin kowane al’amari da ya sauka gare ni. So nawa bakin ciki kan raunana zukata, dabaru su karanta a cikin shi, aboki ya gudu a cikin shi kuma makiyi ya daga kai; amma na mika shi gare Ka na kuma kai kara wajen Ka, ina mai wadatuwa da Kai daga waninKa; sai kuwa Ka yaye shi daga gare ni. Domin Kai ne majibincin kowace ni’ima kuma ma’abucin kowane kyakkywan abu kuma karshen kowace bukata[16].

Ga Umar bin Sa’ad nan, da ya ga Imam Husaini na kashe mutanensa ba tare da gajiya ba, yana bayar da oda da a kunna wuta a tantotin da mata da yara ke ciki don a shagalta Imam a dauke hankalinsa daga yaki. Ga Imam nan ya waiwaya yana kallon wannan tashin hankali, ya daga murya yana magana da mu (masu zuwa daga baya) cewa:

Ko akwai mai kariya ga hurumin Manzon Allah? Ko akwai wani da ya kadaita Allah ya ji tsoron Allah cikin al’amarinmu? Shin ko akwai mai agajin dake fatan haduwa da Allah a kanmu?*

Amma ba abin da ka ke ji sai kukan yara da ihun mata. Ba abin da ya rage ga Imam sai ya fuskance su da kan shi. Don haka ya yi harama ya fada musu.

Ga Imam nan dauke da takobin nan ta Annabi (SAWA), sanye da rawaninsa, ya hau dokin shi (Annabi). Wadanda ke kusa da Umar bin Sa’ad sun ga jikin shi ya yi sanyi da ya hangi Imam Husaini a kan dokin, sai suka tambaye shi dalili, shi kuma ya fada musu gaskiya, cewa ya gane wancan farin dokin da Imam Husaini (AS) ke kan shi ne; dokin na cikin kananan dawakin Annabi (SAWA).

Ga Imam nan na magana da su yana ce musu:

Ni ke yaki da ku, mata ba ruwan su, ku kame daga iyalina tunda ga ni a raye a tare da ku.[17]

Amma ina! Masu kunnen-kashi ne!! Sai ga Shimr bin Zil-Jaushin nan da wasu mutane goma daga sojin azzalumai suna fuskantar wajen tantunan; a nan Imam ya daga murya da karfi ya ce musu:

Kaiconku! In har ba ku da addini kuma ba ku tsoron ranar kiyama, to ku zama ‘ya’ya mana masu lissafi! Ku kawar da jahilanku da kangararrunku daga iyalina.

A nan ne Ibin Zil-Jaushan ya ce: “Ka sami haka, dan Fatima”.

Haka Imam Husaini (AS) ya yi ta fama da su, da sun sha wahala sai su koma ga iyalansa, ya je ya koro su daga can. Yara su kawo kukan kishirwa, don rana ta yi tsanani, kuma makiya sun kange su daga kogin Furat har na tsawon kwanaki uku. Don haka a lokuta da dama ya yita kokarin ya ratsa su ya debo ruwa, amma abin ya ci tura.

Yaki ya tsananta. Ga Imam Husaini can a tsakiyar abokan gaba yana yakarsu ba kakkautawa, da ganin shi ka san dan Ali bin Abi Dalib ne. Ganin wannan ne ma Ibin Sa’ad ya daga murya yana tir da mutanensa da cewa: “Kun manta wanda kuke yaki da shi ne? Shi ne dan mai kashe larabawan nan fa! Wallahi in kuka ci gaba a haka sai ya ga bayan mu baki daya!!

Wannan yasa sun bar hanyar yaki suka koma kisa. Sai suka yi masa kawanya. Ga shi nan sun yi masa taron dangi! ga wani nan ya cillo kibiyarsa ta sauka wuyan Imam… Inna lillah! Sun rufar masa baki daya, mai sara da takobi na yi, mai suka da mashi na yi, wani ma da dutse yake dukan sa. Raunuka sai da suka kai sittin da bakwai a jikinsa[18].

Ga Imam nan kwance a saharar Daffi, jikin shi mai tsarki barbaje ta wuyan shi jini na zuba. Sai dai duk da haka hayakin kiyayya da wutar adawa ba ta gushe tana ruruwa a cikin zukatan makiya. Basu wadata da wannan ba, sai da Shimr bin Zil-Jaushan ya dauki takobi, ga shi nan ya doshi jikin Imam! Mai yake nufi? Wayyo!! So ya ke ya cire kan Imam –wanda juz’in kan Annabi ne-, zai taba reshe daga bishiyar Annabci! Shi ke nan!!! Sara goma sha biyu ya yi a wuyan Imam Husaini ya cire kan daga jikinsa. Wannan kan da ya dade yana wa Allah sujjada, da harshen cikin bakin shi da bai taba kasala ba wajen ambaton Allah da zikiri.

Na’am, yau kan dan ‘yan Manzon Allah ya zama kyautar da za a kai Sham, a mika shi ga mashayin giyan nan da ya sayar da lahirarsa don duniya mai karewa.

Sannan Ibin Sa’ad ya sa aka hau dawaki aka yi sukuwar sallah a kan jikin Imam Husaini da na sauran danginsa, ‘ya’yansa da Sahabbansa, bayan an cire kawunansu. Haka aka barsu a zube a sararin hamadar Karbala har na tsawon kwanaki uku ba tare da an bisne ba.

Sannan aka kwashi mata da kananan yara da Imam Zainul-Abidin, wanda Allah Ya jarabta da rashin lafiya kamar ba zai yi rai ba don ya saura Hujjar Allah a doron kasa, aka daddaure su aka tafi da su Kufa, daga can kuma zuwa Sham, alhali an cire lullubi daga kawunan matan gidan Annabci, aka kafa kawunan a kan kibiyoyi, kan Imam Husaini ke gaban ayari, aka kwashe su a matsayin fursunonin yaki, ana yawo da su daga wannan gari zuwa wancan.

Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un. Wadanda suka zalunci iyalan Annabi za su dandana kudarsu! Lallai kyakkyawar makoma na tare da masu takawa.*

[1] Dabrisi, I’ilamul-Warah bi A’alamul-Huda, shafi na 217; da Khaurazimi, Maktalul-Husaini, juz’i na 1, shafi na 87.

[2] Fairuz Abadi, cikin Fadha’il al-Khamsah Fi Sihah al-Sittah, juz’i na 3, shafi 263; da I’ilam al-Wara, shafi na 219.

[3] Sibd Ibin al-Jauzi, cikin Tazkiratu Khawas al-Ummah, babin da ya yi magna a kan ‘Son Manzon Allah ga Hasan da Husain’.

[4] Fairuz Abadi, cikin Fadha’il al-Khamsah Fi Sihah al-Sittah, juz’i na 3, shafi 262-263.

[5] Abu Ilm, cikin Ahlul-bait, babin dake magana a kan tawali’un Imam Husaini da gudun duniyarsa.

[6] Ibin Abil-Hadid, cikin Sharhin Nahjul-balagha, ju’zi na 11, shafi na 43.

[7] Ibin Athir, cikin al-Kamil Fit-Tarikh, juz’i na 3, shafi na 462.

[8] Ibin Kathir, cikin al-Bidayatu wal-Nihayah, juz’i na 8, shafi na 236.

[9] Mas’udi, cikin Muruj al-Zahbi, juz’i na 3, shafi na 67.

[10] Ibin Dawus, Maktaltul-Hussain, shafi na 11.

[11] Shaikh al-Mufid, cikin Kitab al-Irshad, shafi na 204.

[12] Dan’uwa Mustafa Gadon-Kaya, cikin kasidarsa ta Fadimiyya.

* Wadanda suka bi yakin tekun Fasha a lokacin da Saddam Hussaini ya mamaye Kuwait, kuma sojojin kawancen Amurka suka kudurin aniyar fitar da shi don tserar da dukiyar da suke sacewa daga kasashen Larabawa; za su iya gane irin tasirin wannan ‘Propaganda’ a zukatan gama-garin mutane. Saddam ya iya sa mutane sun yarda da cewa yana da wata runduna da, indan ta bayyana rundunar taron-dangi ta gama yawo. Wannan runduna ta ‘Republican Guards’ har yau ba a ganta ba. Sai ma shi da ya mika wuya ga kudurinsu ya janye daga Kuwait da kan shi. To ga mutanen yau kenan, yaya ka ke gani a da can da ido bai bude kamar yanzu ba?

[13] Abdul-Razak al-Mukarram, cikin Maktalul-Hussaini, shafi na 193.

[14] Ibin al-Athir, cikin al-Kamil Fi al-Tarikh, juz’i na 3, shafi na 48.

[15] Shaikh al-Mufid, cikin Kitab al-Irshad, shafi na 230.

[16] Dabari, cikin Tarikh al-Umam wal-Muluk, juz’i na 4, shafi na 321. Haka nan Shaikh al-Mufid ya fitar da shi a Kitab al-Irshad, shafi na 233 daga Imam Zainul-Abidin (alahis-salam). Haka Imam Al-Bakir (AS) ya shaida wannan al’amari, a lokacin yana yaro dan shekara 4 da haihuwa.

* Labbaika ya dan Manzon Allah! Wannan kira ne ba na wadanda ke halarce a wancan fage kawai ba. Kira ne ga zamuna masu zuwa. Kamar dai Imam na magana da mu ne cewa duk lokacin da aka shata jan layi tsakanin karya da gaskiya da bata da shiriya, to duk wanda ya taimaki gaskiya yana kare haramin Annabi ne kuma shi ke fatan haduwa da Allah kuma shi ne ma’abucin tauhidi na gaskiya. Haka ne!! ga kira nan ina mai amsawa?

[17] Ibin Tawus, Maktalul-Hussaini, shafi na 50.

[18] Dabari ya fada, a cikin Tarikh al-Umam wal-Muluk, cewa adadin sukan mashi talatin da uku da saran takobi talatin da hudu aka samu a jikin Imam Husaini. Duba littafin na sa, juz’i na 4, shafi na 344-346.

* Na san ‘yan’uwa za su so jin abubuwan da suka faru daga inda na tsaya. Sai dai hakan ba zai yiwu ba. saboda kasancewar takaitaccen tarihin Imam Husaini na ke magana a kai, wannan ne ma ya sa na kau da kai daga yadda shahadar sauran shahidan ta kasance da irin muguntar da aka yi wa kowannensu. Na takaita ne da bangaren Imam Husaini, shima din a takaice kwarai. Fata na shi ne in samu nasarar shiga cikin sahun ‘yan’uwan da suka ce wani abu a wannan fannin, ni ma in kara abin da na sani a wani lokaci nan gaba.

6- Imam Ali Zainul Abidin (a.s):
________________________

Shi ne Ali bin Husaini, wanda ake yiwa lakabi da Sajjad da Zainul-Abidin. Da ga Imam Husaini (AS), wanda nasabarsa ta gabata. Ke nan shi dan Annabci ne, wanda kuma ya sha daga marmaron nan mai tsarki na gidan wahayi.

Mahaifiyarsa kuwa ita ce Shahr Banu, wadda ta kasance ‘ya ga sarkin Farisa; an kama ta tare da danginta a lokacin da Musulmi suka ci Farisa da yaki a lokacin Khalifancin Umar dan Khaddabi. Imam Husaini ya saye ta ya ‘yanta ya kuma aure ta, cikin yardar Allah kuma ta sami darajar zama uwa ga daya daga cikin Hujjojin Allah Madaukaki. Allah Ya zabe ta daga cikin danginta Ya sa ambatonta zai saura har duniya ta tashi. Wannan aure na Imam Husaini da Shahr Banu, wadda ta shahara a tsakanin mutanenta da Shah Zanan (wato Shugabar mata), ya yi matukar taimakawa wajen kara jan hankalin Farisawa su kalli Musulunci ta mahangarsa ta hakika*, saboda hakan ya kusanta su da Musulmi a matsayinsu na daidaiku, sun ga kowa da irin kalarsa ta gaskiya kuma sun ga Musulunci ta masu aikata shi ba tare da kuskure ba. Wannan ya sa Musuluncin su ya kyautata, kuma har ma suka gabatar da hidimomi masu kimar gaske gare shi.

Haihuwarsa (AS)

A ranar biyar ga watan Sha’aban na shekarar hira ta talatin da takwas ne uwargida Shahar Banu ta sauka, inda ta haifarwa Imam Husaini (AS) abin haihuwa mai albarka. Wanda daga baya zai zama kwalliyar masu ibada (ma’anar Zainul-Abidin kenan). Lokacin Amirul-Mu’uminin Ali (AS) na da rai; ai ka so ka ga farin-cikin da ya yi na samun wannan babban jika, wanda aka kaddarawa zama Imami na hudu daga tsarkakan Imaman Ahlulbait goma sha biyu (AS|).

Matsayinsa (AS)

Malaman Musulunci da manazartansa, a lokuta da wurare dabam daban, sun yi bayanin girman Imam Sajjad (AS), haka nan kuma sun ambaci matsayin shi na daraja, ilimi, takawa da kusanci da Allah Madaukaki. An riwaito daga Zuhri, ya ce:

Ban riskiwani daga mutanen wannan gidan (na Annabi) da ya fi Ali bin Husain ba)[1].

Haka an rwaito daga Sa’id bin al-Musayyib, daya daga manyan Tabi’ai, yana magana da wani saurayin bakuraishe da ya yi mishi tambaya game da Imam Zainul-Abidin (AS), sai ya amasa masa da cewa:

Wannan –da kake tambaya a kan shi- shi ne shugaban masu ibada, (wato) Ali dan Husaini dan Ali bin Abi Dalib[2].

Haka nan Ibin Hajar al-Haithami ya fitar da cewa:

Zainul-Abidin, shi ne wanda ya gaji mahaifinsa a ilimi, gudun duniya da ibada[3]

An riwaito daga Imam Malik ya ce:

Ana kiran shi da Zainul-Abidin ne saboda yawan ibadun shi[4].

Saboda yawan sujjadarsa ne aka yi masa lakabi da Sajjad. An riwaito daga Imam al-Bakir (AS), cewa ya ba da labarin Imam Zainul-Abidin (AS) da cewa:

Ba ya tuna wata ni’ima ta Allah madaukaki har sai ya yi sujjada, kuma ba ya karanta wata aya da aka ambaci sujjada a cikin ta daga Littafin Allah madaukaki har sai ya yi sujjada, haka ba ya idar da wata salla ta farali har sai ya yi sujjada, kum ba ya samun nasarar daidaita mutane biyu har sai ya yi sujjada. Alamum sujjada ya kasance bayyane a wurin sujjadarsa (goshi), don haka ne ma ake kiransa al-Sajjad[5].

Haka nan Abu Ja’afar al-Bakir (AS) ya ce:

Ya kasance yana daukar buhun hatsi a bayan shi, cikin duhun dare , sai ya je kofar wani mabukaci ya buga, ya ba duk wanda ya fito daga gidan, ya kasance yana lullube fuskarsa a lokacin da yake mikawa mabukacin don kar ya gane shi[6].

Haka wannan hali na shi na sadakar boye ya ci gaba har sai da ya yi shahada sannan mutane suka fahimci cewa ashe shi ke yin ta[7].

Kan hakurinsa kuwa, an riwaito cewa wani mutum ya taba zaginsa a gaban shi, amma ya yi shiru bai ce uffan ba. Sai mutumin ya ce mishi: “Da kai fa na ke magana.” Sai Imam ya ce mishi: “Ni ma daga gare ka nake kau da kai.”

Haka ya taba zuwa ya sami wasu mutane na yi da shi, sai ya tsaya a wajen su ya ce:

In har kuna da gaskiya (kan abin da kuke fada) Allah Ya yafe min. in kuwa karya kuke yi to Allah Ya yafe muku.

Imam Sajjad Ya Ci Gaba Da Ja-goranci

Kamar yadda ya gabata a tarihin abin da ya faru a Karbala, hikimar Allah Madaukaki ta hukunta Imam Zainiul-Abidin (AS) ya saura a raye don ci gaba da ja-gorancin addini.

Ya shaida masifar Karbala alhali babu yadda zai yi saboda tsananinin rashin lafiya da ya hana shi hatta motsawa. Ya shaidawa wani mai suna Minhal bin Umar, da ya taba tambayarsa cewa: Ya ka wuni ya dan Manzon Allah? Sai ya amsa masa da cewa:

Na wuni kamar Bani Isra’ila a hannun Fir’auna, yana yanka musu ‘ya’ya maza yana barin matan a raye[8].

Bayan musifar Karbala, kai tsaye Imam Sajjad ya fara aiwatar da aikin shi na ja-gorancin addini ta hanyoyin da dama ty ba shi. Mai bin diddigin wannan bangaren na tarihi zai iya ganin tasirin yunkurin Imam Sajjad ta fuskoki biyu kamar haka:

Na Daya: Cika gaba da aikin kawo gyara da Imam Husaini (AS) ya fara. Da ma Umayyawa da karnukan farautarsu na sane sarai da matsayin Imam Husaini da Ahllulbaiti (AS) da irin matsayimsu a zukatan mutane. Don haka sun kwana da sanin cewa kashe Imam Husaini da Sahabbansa a Karbala ba zai wuce haka nan shiru ba; sun san cewa Musulmi za su fusata, don haka ne suka yi tsare-tsarensu na shawo kan haka, suka yi iya kokarinsu wajen toshe duk wata hanya da suke tsammanin ana iya yunkurin daukar fansa. Haka sun yi amfani da kafafansu na sadarwa a wancan lokacin wajen yardar da mutane cewa Imam Husaini da Sahabbansa Khawarijawa ne ‘yan hamayya. Wannan kage ya samu wani nau’i na tasiri a fadar mulkinsu dake Sham.Wannan ya sa Imam Sajjad da Sayyida Akila Zainab (kanwar Imam Husain) da Ummu Kulthum da wasunsu daukar siyasar tona asirin siyasar Umayyawa, da tunatar da al’umma nauyin da ya hau kanta, wanda Allah zai tambaye ta a kan shi.

Wannan yana bayyana daga abin da ya faru lokacin da wani dattijo ya zo wajen Imam Sajjad (AS) a lokacin da aka shigo da kamammun zuriyyar Annabi Sham. Dattijon ya ce da Imam Sajjad: ‘Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya halaka ku ya tabbatar da Amirul-Mu’uminin (yana nufin Yazid).’

Sai Imam Sajjad ya ce mishi: Ya kai wannan dattijo, shin kana karanta AlKur’ani?

Sai dattijon nan ya ce: kwarai kuwa.

Sai Imam ya ce mishi: “Ko ka karanta fadar Allah Adaukaki: Ka ce: ba na tambayar ku wani lada a kan shi (aikin isar da sako) face kaunar Makusanta? Da fadarSa Madaukaki: Ku ba (kowane daya daga) Makusanta hakkinsa. Da fadarSa Madaukaki: Ku sani cewa lallai abin da kuka ganimantu daga wani abu, lallai Allah da ManzonSa da Makusanta na da khumusinsa (wato kashi daya bisa biyar dinsa)?

Sai dattijon ya ce: Kwarai na karanta haka.

Sai Imam ya ce: “Wallahi mu ne Makusanta a wadannan ayoyin”.

Daga nan sai Imam ya ce: Ko ka karanta fadar Allah Madaukaki: Lallai Allah na nufin kawar da duk wata dauda ne daga gare ku Ahlulbait, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa?

Sai dattijon ya ce: kwarai na karanta.

Sai Imam ya ce: “Mu ne Ahlulbait din da Allah Ya kebe su da tsarkakewa.”

Sai dattijon nan ya ce: Don Allah ku ne wadannan? Imam ya ce: “Hakika mu ne su ba shakka”.

Sai dattijon ya ciji hannu don takaicin abin da fada, ya kuma yi bara’a daga Umayyawa da kungiyarsu[9].

A nan bangaren, Imam Sajjad (AS) ya tsaya kyam wajen tona asirin Umayyawa da bayyana ainihin kalar Yazid ta hakika. Wannan ya bayyana a lokacin da ya mike a gaban taron al’ummar Musulmi ya yi hudubar da, a cikinta, ya ke cewa:

Ya ku mutane, an ba mu abubuwa shida an kuma fifta mu da wasu bakwai. An ba mu: ilimi, hakuri, yafiya, fasaha, gwarzontaka da kauna a zukatan muminai. An kuma fifita mu da cewa: a cikin mu akwai Mukhtari (wato Annabi), a cikin mu akwai Siddiki, a cikin mu akwai mai tashi (tayyar)*, a cikin mu akwai zakin Allah da zakin Manzon Allah, a cikin mu akwai shugabar matan duniya, Fadima al-Batul, da jikoki biyu na wannan al’umma. Ya ku mutane, wanda ya san ni ya san ni, wanda kuwa bai san ni ba yanzu zan ba shi labarin danganena da matsayina. Ya ku mutane, ni ne dan Ka’aba da Mina. Ni ne dan Zamzam da Safa. Ni ne dan wanda ya dauki bakin dutse da gefen mayafi. Ni ne dan mafi alherin wanda ya sa sutura da mafi alherin wanda ya yi dawafi, ya yi sa’ayi, ya yi hajji ya amsa kiran Allah. Ni ne dan wanda aka dauka a Buraka (zuwa Isra’i) kuma Jibrilu ya kai shi Sadratul-Muntaha, sai ya kasance kamar kusancin tsakiyar baka ko fiye da haka. Ni ne dan wanda ya yi salla da Mala’ikun sama. Ni ne dan wanda Mabuwayi Ya yi mishi wahayin abin da Ya yi wahayi. Ni ne dan Fadima al-Zahara da kuma Khadija al-Kubra. Ni ne dan wanda ke lullube da jini! Ni ne dan yankakken Karbala.

Daidai lokacin da ya kawo nan hankulan mutane sun gama tashi, sai hayaniyar kuka ya rufe wajen baki daya yayin da suka fahimci gaskiya. Wannan ne ya sa Yazidu ya hori mai kiran sallah ya daga murya ya kira sallah don ya yanke Imam daga hudubarsa. Imam ya saurara wa mai kiran salla har sai da ya gama fadar: Ashhadu anna Muhamman Rasulullah (wato na shaida cewa Muhammadu Manzon Allah ne); sai ya waiwayi Yazid ya ce:

Wannan Manzon kakanka ne ko kakana? in ka ce kakanka ne, to masu sauraro da sauran dukkan mutane sun san kai makaryaci ne. In kuwa har ka yarda kakakana ne, to mai ya sa ka kashe babana bisa zalunci da kiyayya, ka kwace dukiyarsa ka kama matansa? To bone ya tabbata gare ka ranar kiyama in har kakana ya zama abokin husumar ka[10].

Matan gidan Annabci ma na da irin wannan matsayi, masamman Zainab al-Kubra, wadda ita ma ta yamutsa gidan Yazidu da taron mutane a waje. Wannan na nan a littafan tarihin da suka tabo bangare abubuwan da suka faru da jikokin Annabi bayan masifar Karbala.

Na biyu: Sabon tafarkin kawo gyara da ya kirkira. Bayan Imam Zainul-Abidin (AS) ya dawo Madina, ya tsara wa kansa sabon tafarkin da zai gina ci-gaban aikin shiriya da da ya gada daga kakanninsa. Wannan ya zo bayan ya yi kyakkyawan narzari a kan sabon yanayin da al’umma ta shiga.

Abin da Imam ya mayar da hankali a kai shi ne gina ruhin al’umma da kyautata bangaren halayya da wayar da kai. Wannan aiki na shi ya sami kyakkywan sakamako saboda irin kyakkyawan tasirin da ya samu, da kuma tabarbarewar yanayin siyasa da zamantakewa da suka tilastawa al’umma waiwayen Ahlulbaiti (AS)

Waje cimma wadannacan manufofi, Imam ya ginu a kan wasu hanyoyi kamar haka:

a) Ya mayar da gidansa ya zama wata babbar cibiyar wayar da kan Musulmi, inda a tsawon lokacin Imamancin shi –wanda ya share kusan shekaru talatin da biyar- hasken shiriya ya rika bubbugowa daga can.

b) Biyan bukatun jama’a da kokarin magance matsalolinsu dabam-daban. A kan wannan aka riwaito daga dansa Imam al-Bakir (AS) cewa:

Ya kasance yana daukar dawainiyar gidajen talakawa dubu daya a Madina. Yana sha’awar ya bayar da abincinsa ga marayu da talakawa da marasa lafiya da miskinai, wadanda ba su da wata dabara. Ya kasance yana ciyar da su da hannun shi. Wanda ke da iyali daga cikin su kuwa, yakan dauki abincin shi ya kaiwa iyalin.[11]

Ya kasance yana debowa gajiyayyu daga makotansa ruwa da daddare. Yana yawan sayen bayi ya ‘yantar da su daga bautar.

Saboda yawan zama da nau’o’in mutane dabam-daban har sai da wani ya taba neman ya nuna masa cewa haka bai dace da matsayinsa ba, amma sai Imam ya amsa masa da cewa:

Ni ina zama ne da wadanda zan amfanar da su a addinina.[12]

A takaice wannan hanya ta ba Imam Sajjad (AS) daman hada hankulan mutane wajen sauraron karantarwar Musulunci.

c) Raya ranakun Imam Husaini da Ashura. Wannan ma wani tafarki ne mai tasiri da Imam Zainul-Abidin (AS) ya yi amfani da shi wajen aikinsa na isar da sako. Ya kasance koda yaushe yana tsayar da zaman makoki a gidansa. Ya na zafafa zukata da mosta su. Wannan kuwa ya yi matukar tasiri wajen dauwamar da wannan sako na Imam Husain a cikin tarihin Musulunci da lamirin al’umma.

Da haka ana iya cewa Imam Sajjad, ta wannan hanya, ya iya jan al’umma gaba zuwa manufar shahadar Imam Husaini (AS) da iyalansa, danginsa da sahabbansa.

d) Addu’a. Tarihin Imam Zanul-Abidin (AS) na hakaito mana tarin arzikin addu’o’in da ya bar wa wannan al’umma. Ba tare da jin cewa akwai mai gaskiyan da zai iya karyata ni ba, zan iya cewa: Musulmi, da dukkan bangarorinsu, sun kasa wadatuwa daga addu’o’in Imam Sajjad (AS). Ina nufin cewa so tari Musulmi kan takaita abin da suka ya zo daga wajen shugabannin bangarorinsu a fannoni irin fassarar AlKur’ani, hadisai da ka’idojinsa, gine-ginen akida, mas’alolin furu’a da sauransu; tare da kawar da kai da yin kunnen uwar-shegu daga masu abin (Ahlulbaiti AS). Amma wajen addu’a sun kasa wadatuwa da abin da ke wajen amintattun na su. Don haka littaffan Musulmi sun dace akan fitar da wadannan addu’o’i da kiyaye su ba tare da wani shakka ko tantama a kansu ba.

Addu’o’in Imam Sajjad na da mafuskanta biyu na asasi. Na daya mafuskantar ibada, na biyu kuma mafuskantar zamantakewa. A dukkan fuskokin nan biyu Imam na aikawa ne da sakonsa na kawo gyara da ya ke shugabanta.

An tara wadannan addu’o’i karkashin sunan Sahifa al-Sajjadiyyah, wanda a halin yanzu suna nan suna kai-komo a hannun Muminai.

A hakika Sahifa na tattare da sakonnin Annabawa, Manzanni, da (masamman) Annabi Muhammadu (SAWA) da tsarkakan Imaman Ahlulbait (AS). Bugu da kari, wata jami’a ce ta tarbiyya da samun alakar kud-da-kud da Ubangiji Allah Madaukaki.

Masu Mulki In Sun Shiga Kasa Sukan Bata ta

Kamar yadda suka saba, mahukuntan Umayyawa, karkashin ja-gorancin Abdul-Malik, suna nan a kan bakarsu na kokarin ganin bayan sakon Musulunci. A wannan dan tsakankanin sun yi ta yada ta’addanci da kashe-kashe ta hannun Hajjaj bin Yusuf al-Thakafi. Hajjaj ba boyayye ba ne a tarihi, domin hatta masu akidar boye barnace-barnacen magabata sun kasa kawar da kai daga irin ta’asosin shi. Ya kasance gwamna a Kufa –wadda ta kasance helkwata ga Ahlulbait a wannan lokacin-, ai kuwa al’umma ta ga abin da ta gani, domin ya bayyana boyayyen shirin Umayyawa da muguntarsu a fili.

Hajjaj ya kashe talikai bisa tuhuma da zato a Kufa. Muminai ne suka fi wahala, masamman’yan Shi’a, a hannunsa. Imam al-Bakir (AS) ya siffanta wannan ta’addanci da cewa:

Sannan Hajjaj ya zo ya kashe su (yana nufin mabiya Ahlulbait) da dukkan (wani nau’i na) kisa. Ya rike su da kowane zato da tuhuma, har ya zama a kira mutum da zindiki kafiri ya fi mishi kan a kira shi da Shi’ar Ali)[13].

Wasu masu tarihi sun bayyana adadin mutanen da Hajjaj ya kashe a shekaru ashirin din da ya yi yana gwamana da cewa dubbai ne ba kadan ba. A kurkukunsa kawai sama da maza dubu hamsin da mata dubu talatin ya kashe.[14]

Imam Shahidi

Bayan mutuwar Abdul-Malik al’amura sun kara rincabewa. Domin yayin da dansa Walid ya dare kujerar mulki ba wanda ya rage a fagen aikin kawo gyara sai Imam Sajjad (AS), a sakamakon murkushe duk wani yunkuri na kawo gyara da aka yi. Wannan ya sa, a dabi’ance, dole Imam ya zama tsaikon matsalolin mahukunta da tsoronsu. Don haka sai suka shiga makirce-makirce da neman hanyar gamawa da Imam.

Haka kuwa abin ya kasance. Domin Imam ya yi shahada a sakamakon gubar da aka shayar da shi a zamanin mulkin Walid bin Abdul-Malik.

Haka ne, sun sa birki ga ci-gaban aikin da Imam Sajjad ke yi, amma ba su iya dakatar da ci-gaban abin da ya riga ya yi ba. Ya zama wani tsaiko na sanin Allah Madaukaki da samun kusanci da Shi. Tunane-tunane shi da hasken da ya bari na nan na walwali a samaniyar dan Adam. Ambaton shi ya saura da alheri.

Amincin Allah ya tabbata gare shi da iyayen shi da ‘ya’yan shi tsarkaka.

* Domin kafin wannan lokacin, kusan duk Farisawa na kallon Musulunci a matsayin addinin da ake tilasta shi a kan mutane da karfin tsiya. Wannan tunani na su kuwa ya samo asali ne daga hukunta Musulunci da suka yi da dabi’un Khalifofin da suka mulke shi, masamman ganin irin samamen da aka kai musu dare daya ba zato ba tsammani.

[1] Shaikh al-Mufid, cikin Kitab al-Irshad, shafi na 240.

[2] Kitab al-Irshad.

[3] Sibt Ibin al-Jauzi, cikin Tazkiratu Khawas al-Ummah, babin ambaton Imam Zainul-Abidin (AS).

[4] Taufik Abu Ilm, cikin Ahlul-Bait, babin magana kan ‘ya’yan Imam Husain.

[5] Al-majalis al-siniyyah, mujalladi na biyu.

[6] Duba littafin Manakibu أli Abi Dalib, babin ambaton darajojin Imam al-Sajjad.

[7] Kitab al-Irshad, shafi na 242.

[8] Abdul-Razak al-Makarram, cikin Makatalul-Hussaini; ya ciro daga littafin al-Ihtijaj na Tabrasi.

[9]Al-Mukarram, maktalul-Husaini, shafi na 449.

* Shi ne Ja’far dan Abi Dalib, wanda ya yi shahada a yakin Hunaini bayan an yanke hannuwansa biyu. Manzon Allah ne ya bada labarin cewa Allah zai yi masa fika-fikai irin na Mala’iku da zai rika tashi sama da su tare da Mala’iku a gobe kiyama.

[10] Al-Tabrisi, cikin al-Ihtijaj, juz’i na 2, shafi na 49.

[11] Ibin Shahr Ashwab, al-Manakib, juz’i na 4, shafi na 154.

[12] Ibin Shahr Ashwab, al-Manakib, juz’i na 4, shafi na 154.

[13] Ibin Abil-Hadid, Sharhin Nahjul-Balagha, juz’i na 11, shafi na 44.

[14] Muhammad Jawad al-Mugniyah, al-Shi’atu wa’lhakimun, wajen maganar Hajjaj.

7- Imam Muhammad Al-Bakir (a.s):
________________________

Shi da ne ga Imam Zainul-Abidin (AS) da tarihin shi ya gabata. Daya daga cikin tsarkakan da Allah Ya zaba don wakilcin Shi a cikin bayin Shi. Hujja daga HojjojinSa, wadanda wanzuwar duniya ta ta’allaka da kasancewarsu.

Haihuwarsa (AS)

An haifi Imam al-Bakir (AS) a farkon watan Rajab na shekara ta hamsin da takwas (ko da bakwai) bayan hijira, wato shekaru uku ko hudu kafin shahadar kakansa Imam Husaini (AS), wadanda su ne shekarun da ya yi ke nan da kakansa. Ya rayu da mahafinsa na sama da shekaru ashirin (wala’alla da biyar ne) yana sha daga marmaron Annabci. Bayan shahadar mahaifinsa kuma ya rayu shekaru talatin ba ‘yan watanni a duniya. Yana cikin kananan yaran da suka halarci masifar Karbala, a lokacin yana da shekaru hudu ko uku.

Ya yi zamani da sarakunan Umayyawa. Amma shi ya yi sa’ar samun na kirkin su (kwaya daya rak din nan), wato Umar bin Abdul-Aziz.

Matsayinsa (AS)

Wani hadisi da Musulmi ke riwaitowa daga Manzon Allah (SAWSA) ya takaita irin baiwar da Allah Ya kebe Imam al-Bakir (AS) da ita. Zubiru bin Muslim al-Makki ya ce: “Mun kasance a wajen Jabir bin Abdullah al-Ansari, wanda Sahabin Annabi ne, sai Ali bin Husaini (Zainul-Abidin) ya zo gare shi tare da dansa Muhammad (al-Bakir) a lokacin yana yaro. Sai Ali ya cewa dansa: Je ka sumbaci kan baffanka. Sai Muhammad ya je wajen Jabir ya sumbaci kansa. Sai Jabira ya yi tambaya ko wanene wannan –a lokacin ya rasa ganinsa- sai Ali bin Husaini ya ce mishi: wannan dana ne Muhammad. Sai Jabir ya rungume shi ya ce: “Ya Muhammad, kakanka Manzon Allah na gaisheka.” Sai suka ce masa: ya aka yi haka ya Jabir? Sai Jabir ya ce:

Na kasance a wajen Manzon Allah (SAWA) a lokacin Husaini na zaune a cinyarsa shi kuma yana wasa da shi, sai ya ce min: “Ya Jabir, dan nan nawa Husaini zai sami wani da da za a kira shi da Ali, idan kiyama ta tsaya mai kira zai yi kira cewa shugaban masu ibada ya tashi, sai Ali bin Husaini ya tashi. Haka za a haifarwa Ali din da wani da da za a sa masa suna Muhammad. Ya Jabir, in ka riske shi ka isar da gaisuwata gare shi, in kuma ka hadu da shi to ka san ranakunka sun saura kadan ne”. bayan nan Jabir bai wuce kwanaki uku ba[1].

Imam al-Bakir (AS) ya shahara da tarin sani da zurfin ilimi, ta yadda har masoyi da makiyi suka dace a kan fifikonsa da daukakar matsayinsa a duniyar dan Adam na lokacinsa; wannan ne ma ya sa ake yi masa lakabi al-Bakir (wato mai tsaga ilimi). Malamai sun daga masa tuta a kan haka.

An hakaito Ibin Imad, wanda dan mazhabar Hambaliyya ne, yana cewa:

Abu Ja’afar, Muhammad al-Bakir, ya kasance cikin fakihan Madina. Ana kiransa al-Bakir ne ma saboda yadda ya tsaga ilimi, ya san tushensa ya kuma fadada a cikin shi[2].

Haka nan Muhammad bin Dalha, wanda dan Shafi’iyya ne, ya ce:

Muhammad bin Ali al-Bakir: Shi ne mai tsaga ilimi, wanda ya tara shi, wanda ya daga ilimi ya sa ya shahara, wanda ya zurfafa shi kuma ya shayar da shi, wanda ya kyautata tsironsa ya gyara shi. Zuciyarsa ta wanku, aikinsa ya tsarkaka, halayensa sun daukaka, lokutansa sun kawatu da bin Allah, kafafunsa sun kafu bisa takawa. Alamun kusanci (da Allah) da tsarkin zabi (zabin Allah) na bayyana daga gare shi. Darajoji na rige-rige zuwa gare shi, kuma (kyawawan) siffofi na daukaka da shi[3].

A duk lokacin da Jabir bin Yazid al-Ja’afi zai riwaito daga Imam al-Bakir (AS) yakan ce:

Wasiyyin wasiyyi kuma magajin ilimin Annabawa, Muhammad bin Ali bin Husaini ya ba ni labari[4].

Dabi’unsa (AS)

An riwato daga dansa Imam al-Sadik (AS), ya ce:

Babana ya kasance mai yawan zikiri, na kasance ina tare da shi a halin tafiya alhali shi yana ambaton Allah. Ina cin abinci da shi yana ambaton Allah. Hakika ya kasance yana magana da mutane alhali wannan bai shagaltar da shi daga zikirin Allah ba…[5]

An riwaito daga Hasan bin Kathir, ya ce: Na taba kai bukata da kukan rashin taimakon ‘yan’uwa zuwa ga Abu Ja’afar Muhammad bin Ali (AS), sai ya ce: “Mummunan dan’uwa shi ne dan’uwan da ya lura da kai kana mawadaci, ya watsar da kai a halin rashi. Sai ya hori wani yaron gidansa ya fito da jaka kunshe da dirhami dari bakwai, sannan ya ce: “Ka ciyar (da gidanka) da wannan, in sun kare kuma ka sanar da ni”.[6]

Bisa Raganar Imamanci

Ragamar ja-gorancin al’umma ta zo hannun Imam al-Bakir bayan shahadar mahaifinsa. Ya ci gaba da wannan aiki ta salon da zamaninsa ya hukunta masa dauka, wannan kuwa shi ne salon karantarwa da yada tunane-tunane da sannai. Ya yi namijin aiki wajen tarbiyyar malamai da masana, wadanda za su zama ja-gorori a fagagen tunani; kuma wadanda suka waye da Shari’a kamar yadda ya kamata.

Daruruwan zukata masu kwadayin zurfafa sani sun yi tattaki zuwa makarantarsa daga kusan kowane lungu na duniyar Musulmi. Sun kunshi mashahuran malamai da manazarta banda dalibai, daga bangarorin Mu’utazilawa, sufaye kai har da irin Khawarijawa da sauran sauransu.

A zamaninasa karantarwar Ahlulbait (AS) ta fadada kwarai da gaske masamman a fagagen ilimi da zurfin sani. Shaikh al-Mufid ya bayyana haka da cewa:

Ilimi da tarin hadisai, ilimin AlKur’ani, sira da fannonin ilimin lugga ba su bayyana a hannun daya daga cikin ‘ya’yan Hasan da Husaini kamar yadda suka bayyana a hannun Abu Ja’afar al-Bakir (AS) ba. Hakika Abu Ja’afar ya riwaito labaran Annabawa kuma littafan trihin yakoki da na hadisai sun riwaito abubuwan da ya riwaito daga Manzon Allah (SAWA) daga gare shi, sun dogara da shi a kan haka a lokutan aikin hajji. Sun rubuta tafsirin AlKur’ani daga gare shi. Haka Ahlussuna da Shi’a sun riwaito hadisai daga gare shi. Ya kuma yi muhawara da duk wanda ya zo wurinsa daga ma’abuta ra’ayi. Mutane sun sun hardace ilimin akida mai yawa daga gare shi[7].

So tari wasu na zuwa da rikirkitattun tambayoyi, da manufofi dabam daban, zuwa ga Imam al-Bakir (AS), amma sai su sha mamakin ganin yadda Imam ke amsa musu ba tare da ya daga kai sama ba. Daya daga cikin almajiransa, mai suna Muhammad bin Muslim, ya ce:

Wani abu bai taba zuwa tunanina ba har sai na tambayi Abu Ja’afar game da shi, har sai da na tambaye shi tambayoyi dubu talatin[8].

Kamar yadda ya ke da nau’o’in ilimi, haka ya ke da hanyoyin yada su. A wasu lokuta ya kan bijiro da tunane-tunanensa a zauren karatunsa, a wasu lokuta kuma ta hanyar munazara da muhawara, wani lokaci kuma ta hanyar haduwa da malaman Ahlussunna a lokutan aikin hajji, a yawan lokuta kuma ta hanyar wa’azozi, nasihohi da tunatarwa da wasun wadannan.

Siyasar Umayyawa A Lokacin Imam al-Bakir

Imam al-Bakir (AS) ya imamanci al’umma har na tsawon shekaru tara da ‘yan watanni, daga shahadar mahafinsa a shekara ta 95 bayan hijira. A shekaru biyu na Imamancinsa ya yi zamani da Walid bin Abdul-Malik, ya yi shekara biyu kuma a mulkin Sulaiman bin Abdul-Malik –wanda wannan ne tsawon mulkin da (shi Sulaiman din) ya yi.

Da Umar bin Abdul-Aziz ya karbi ragamar mulki sai salo ya canza, yayin da aka sami babban sauyin siyasa. Duk da karancin lokacin mulkin Umar bin Abdu-Aziz, ya dauki madaidaicin matsayi game da Ahlulbait (AS). Domin ya kawar da wasu zalunce-zalunce da aka yi ta yi gare su, ya hana zagin Imam Ali da Mu’awuya ya kirkira ya yada a garuruwa har sai da ya zama al’adar da mahukuntan Umayyawa ke yadawa a mumbarorin Musulmi har na tsawon shekaru tamanin. Ya mayarwa da Imam al-Bakir Fadak din kakarsa Fatima, wanda filin noman dabinon Manzo ne da ya ba ‘yarsa Fatima tun yana da rai, amma sai mahukuntan wancan zamanin suka kwace saboda dalilansu na siyasa. Sai dai bayan mutuwarsa Umayyawa sun sake kwace wannan fili.

Sai dai Umar bin Abdul-Aziz ya fuskanci matsin lamba daga ‘yan’uwansa Umayyawa, saboda irin sabon su na rashin sassauci ga ‘ya-gidan Annabi. Wannan ya sa mulkin shi bai wuce shekaru biyu da watanni biyar ba, yayin da ya mutu a wani yanayi mai cike da tankiya.

Bayan shi sai Yazid bin Abdul-Malik ya hau kujearar Khalifanci, wanda sananne ne a tarihi da sheke-aya, wasannin banza da fasadi. Wannan taliki ya yi matukar taimakawa wajen kara gurbata tarihin Musulunci kamar kakanninsa, ya kuwa fuskanci mummunan kalubale daga bangare ‘yan gwagwarmaya da Imam al-Bakir kewa ja-goranci.

Bayan shi sai Hisham bin Abdul-Malik ya karbi ragamar mulkin Umayyawa. Shi ma dai bai kasa sauran azzaluman kakannin shi ba. Ya kasance mai dabi’ar mugunta, marowaci, mai tsaurin rai; ga shi jahili, ya ki jinin Musulmin da ba larabawa ba, ya rika ninka harajin dukiya a kansu, ya maimaita ranakun Yazid da na Hajjaj masu cike da zubar da jini. Wannan ya ja mishi bore daga bangaren masu magoya bayan Ahlulbait (AS), a sakamakon kashe Zaid dan Imam Ali Zainul-Abidin da ya yi. Shi kuwa Zaid ya ja-goranci masu boren neman fansan kashe Imam Husaini ne.

Bayan Hisham ya kashe Zaid, sai ya sa aka bankare gawarsa sannan aka kona ta aka zubar da tokar a kogin Furat.

Hisham ya shiga bin Sahabban Imam al-Bakir da mabiyansa yana kama su daya bayan daya. Har ma ya hori gwamnansa a Kufah da ya kashe Jabir bin Yazid al-Ju’ufi, wanda ya kasance babban malami kuma daga fitattun almajiran Imam (AS). Sai dai Imam al-Bakir ya bata wannan makirci, yayin da ya hori almajirin na shi da bayyana haukar karya don haka ne kawai hanyar tserar da kan shi daga kisa. Haka Jabir kuwa ya rika shiga cikin yara yana bayyana kamar shi mahaukaci ne, wannan ya sa gwamanan ya aikawa da Hisham cewa Jabir ya haukace; sai wannan ya tsirar da shi daga kisa[9].

Imam Ya yi Karshe Irin Na Kakanninsa

Hisham ya kwana da sani cewa cibiyar yaduwar Musulunci ta ingantacciyar fuska na tare da Imam al-Bakir (AS), kuma matukar Imam na yawo cikin ‘yanci to yana kara samun daman jan yunkurin kawo gyara ne a cikin al’umma. Don haka sai ya murda kanbun makircin nan na Umayyawa, don ya kama Imam ya nisanta shi daga cibiyar kakansa al-Mustafa (SAWA), wadda mutanenta da na Hijaz baki daya, suka dace a kan girmama shi da riko da shi.

Wannan ya sa aka kama Imam al-Bakir da dansa Imam al-Sadik (AS) aka kai su Damashk (Syriya) don dakatar da tasirin da suke da shi cikin al’ummar Musulmi, da kange Imam daga aiwatar da babban aikin shi na isar da sako, sai aka jefa shi a daya daga gidajen kurkukun gwamnati na can.

Sai dai irin tasirin da Imam ya yi, ko dai a tsakanin mutanen dake kulle a kurkukun[10], ko saboda tasirinsa ga jama’ar Damashka, a sakamakon mukabalar da ya yi da shugaban mabiya addinin Kirista na can ya kuma galabce shi[11], ya sa dole Hisham ya sake shi ya koma da shi Madina. Ba mamaki duka al’amurran biyu ne suka tilasta sakin Imam (AS).

A karshe dai da duk hanyoyin matsi da hana tasirin Imam al-Bakir (AS) ci-gaba da zama a zukatan mutane suka ci tura, sai siyasar Umayyawa ta ga ba makawa sai ta kashe shi.

A shekarar hijra ta 114 mahukuntan suka cimma burinsu, yayin da sabbaba ajalinsa ta hanyarsu ta guba. Haka ya bar duniya yana shahidi mai hakuri da halin da ya shiga.

Da wannan reshe daya daga rassan bishiyar nan ta gidan Annabci mai tsarki ya fadi, ‘yantattu suka yi bakin cikin rashin babban ja-gora. Amincin Allah ya tabbata gare shi a duk halin da ya ke ciki.

KARKAREWA

Kamar yadda muka fada a gabatarwar wannan littafi, daga tarihin Imam al-Bakir (AS) wannan juz’in zai kamnala. Sai kuma mun hadu da mai karatu a juz’i na biyu.

Juz’i na biyu, in Allah Ya yarda, zai kammala tarihin Imamai bakwai din da suka saura ne; farawa da Imam Ja’afar al-Sadik (AS), har zuwa na karshensu Imam Mahdi da ake jira (AF).

Bayan nan kuma sai sashin akidun Shi’a, inda bayani a kan wasu zababbun akidun Shi’a da dalilansu a kai ke zuwa. Kamar akidarmu a kan Khalifanci, AlKur’ani, Sahabbai, Takiyya, Bada’, zalunci da hulda da azzalumai da sauran akidun da suke a bugun farko na wannan littafi. Har ila yau akwai kari a kan haka, inda za mu yi nazari kan alakar Shia’anci da Iran. Haka za mu sanar da akdar Shi’a a kan zamantakewa da Kirista da sauran makotanmu wadanda ba Musulmi ba. Haka nan tunaninmu game Shari’a, ta’addanci da wasu rikice-rikicen duniyarmu ta yau.

Allah Ya sa mu dace. Ya kuma amsa mana. Amin summa amin.

[1] Shaikh al-Mufid, cikin Kitab al-Irshad. Da Ibin Sabag cikin al-Fusul al-muhimmah.

[2]Imam Sadik wal-mazahib al-arba’, juz’i na 2, shafi na 436/

[3] Imam Sadik wal-mazahib al-arba’, an ciro daga Matalib al-Su’ul, juz’i na 3, shafi na 50.

[4] Bihar al-Anwar, juz’i na 47, babin kyawawan dabi’unsa.

[5] Inda aka ambata a sama.

[6] Kitab al-Irshad, babin falalolin Muhammad al-Bakir (AS).

[7] Kitab al-Irshad, babin falalolin Muhammad al-Bakir (AS).

[8] Allam al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juz’i na 46, babibin magana akan iliminsa

[9] Manakibu مli Abi Talib, juz’i na 4, shafi na 191.

[10] Kamar yadda mai littafin Manakibu مli Abi Talib, ya fada a juz’i na 3, shafi na 322-323.

[11] Kamar yadda Dabari ya fitar a cikin littafin Dala’ilul-Imamah, shafi na 104.