Thursday 20 September 2012

YADDA AKA GABATAR DA MUZAHARAR AMSA KIRAN MANZON ALLAH [SAWA] A ZARIA

                                          [S3K4] Daga:www.harkarmusulunci.org

                                                        Sayyid Zakzaky [H]            
Yadda aka gabatar da muzaharar amsa kiran Manzon Allah[SAWA] a Zaria
________________________________________
Da sanyin safiyar yau alhamis 3 ga Dhul Qa'adah shekara 1433 dadidai da 20 ga Satumba, 2012 ne, al'umma daga sassa daban daban na Nigeria da makwabta suka fara dafifi a garin Zariya a arewacin Nigeria domin amsa kiran jagoran harka Islamiyya a Nigeria Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)..........
________________________________________
Da sanyin safiyar yau alhamis 3 ga Dhul Qa'adah shekara 1433 dadidai da 20 ga Satumba, 2012 ne, al'umma daga sassa daban daban na Nigeria da makwabta suka fara dafifi a garin Zariya a arewacin Nigeria domin amsa kiran jagoran harka Islamiyya a Nigeria Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) na nuna rashin yardar mu a kan fim din batanci ga Fiyayyan Halitta, Manzon Tsira Muhammad (SAWA).
Da misalin karfe 9ns agogon Nigeria ne al'umma suka fara shiga sahu a filin da ke daf da masallacin cikin birnin Zariya,  suna masu daga sauti suna LABBBAIKA YA RASULILLAH!!! BA MU YARDA DA A CI ZARAFIN MANZO BA!!!.
Tattakin ya kunshi Maza da mata, matasa da tsaffi, Musulmi har da wadanda ba Musulmi ba (wanda wani mai kiyasi ya ce za a fi miliyan) rike da alamomi na nuna yarda, so da kauna ga Manzon Allah (SAWA) da kuma nuna ki da kiyayya ga duk wadanda ke kin Manzo (H) musamman uwar shedanu Amerika da Israila wadan da suka dauki nauyin shirya wannan mummunan Fim na batanci.
Tattatkin ya bi ta filin babban Dodo, sannan aka bi ta kofar doka, ta Tudun-wada, PZ a ka bi ta Sakkwato road aka kuma karke a filin sukuwa da ke daf da Hussainiyya Baqiyatullah.
Har wajen karfe 12nr muzaharar bata kare ba, Jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Zakzaky(H) ne ya rufe muzaharar bayan an kammala da jawabin da ya gabatar na tsawon kimanin awa daya.
Shaikh Zakzaky (H) ya baiwa al'umma da ba su iso filin taron ba hakuri yayin da ya fara jawabi saboda lokaci. Haka nan kuma a jawabin nasa ya taba sassa daban daban da ya kunshi wanene Manzo (SAWA).
Shaikh(H) ya nuna cewa: ya ishe dukkan Musulmi nuna fushin su ga wannan aibata Manzo (SAWA), idan an aibata Manzo Allah(SAWA) wanene ba za su aibata shi ba? Mu Musulmi alhamdulilah Allah Ya hane mu ga aibata kowa hatta masu bautan gumaka, amma ba za mu yarda a aibata Manzo ko alamin addinin mu ba.
Shaikh ya kara nanatawa da babbar murya Musulmi a duk fadin duniya ba za su taba yarda da aibata Manzon mu ba. Idan wasu kan fake da 'yanci fadan albarkacin bakin su aibata Manzon mu, ai suna yin doka su hana wadansu abubuwa da ya shafe su ko? To mu ma ya zama lazim a kafa doka a hana wani ko wasu aibanta Manzon mu.
An kona tutocin Uwar Shaidan Amerika da Israila, da mutun mutimin masu tafiyar da ita yayin da mahalarta suka daga sauti suna ambaton ALLAHU AKBAR! LABBAIKA RASULULLAH, MUTUWA GA AMERIKA DA ISRAILA.
Shaikh Zakzaky (H) ya gabatar da dua, kuma ya yi hira na 'yan mintoci da kafafan watsa labarai da suka hada da Press TV, Al-alam TV, NTA da sauran su.
An tashi muzaharan lafiya kuma tuni alumma sun nufi inda suka fito.

No comments:

Post a Comment