[S4i5] TARIHIN: Shaikh Ahmad Tijjani {R.A}. Ga salsalarsa: Sunansa: Ahmadu Dan Muhammad Mukhtar, Dan Ahmad, Dan Muhammda, Dan Salim, Dan Abil-Eid, Dan Ahmad, Dan Ahmad, Dan Ali, Dan Abdallah, Dan Abbas, Dan Abduljabbar Dan Idris, Dan Idris, Dan Ishaq, Dan Zainul-Abideen, Dan Ahmad, Dan Muhammad, Dan Nafs-Zakiyah, Dan Abdullahil-kameel, Dan Hassan ...Muthanna, Dan Imam Hassan, Dan Amirul-muminina Ali bin Abi-Dalib {AS} Mijin shugaban Matayen Duniya Fatima Zahrah 'yar Manzon Allah Muhammad {S.A.W.A}. An haifi Shehu Ahmad Tijjani a cikin shekara ta 1150 a wani kauye mai suna Ainamadi a gabashin saharar Marocco, amma yanzu yana karkashin ikon Kasar Algeria, kimanin mil 30 daga birnin Laghuat {Al-Aghwat} Suna Mahafiyarsa Lalla A'isha {A'icha} Al-Sunusi. Shehu Tijjani ya fito ne daga Gidan Sharifai. Ba'a dade da haihuwar Shehu ba sai kakansa Sidi Muhammad Ibn Salim tare da duk Iyalansa suka yi kaura daga Garin Asfi {Safi} ya koma da Iyalansa a garin Tijjani, a wannan Garin ne Shehu Ahmad ya sami lakibin Tijjani. Shehu ya sami kyakkyawar kulawa daga Babansa Sidi Muhammad Ibn Mukhtar, a wannan Garin Shehu ya girma kuma yayi aure. Shehu Mutumne wanda Duniya ta san shi da tsoron Allah. Mahaifiyar su Shehu ta haifi 'ya'ya da yawa amma da yawa sun rasu. Shehu yana da yaya mace mai suna Rukayyan sannan kuma Shehu yana da wani dan uwa namija mai suna Sidi Muhammad. Allah {T} ya karbi ran Shehu Tijjani a Garin Faz ranar laraba bayan ya kammala sallar asuba sai ya ce "a kawo mani kofi" bayan ya kammala shan ruwa sai ya kwanta da sashin dama bisa gadonsa daga nan Allah ya dauki ruhinsa {ALLAHU-AKBAR}. Wanda ya yi masa sallah shine limamin Babban Masallacin Sidi Abi-Muhammad Ibn Mohammad Ibn Ibrahim Dukkawiya, sannan an yi wa Shehu Sallah ne a Masallacin Qirawaniy kuma an bisne shi ne a Zawiyyarsa.