MUNASABOBIN MUSULUNCI

YAU NE RANAR MATA NA DUNIYA {15 RABI’USSANI 1433}

Hakkin Mace A Kan Mijinta
Daga cikin hakkin mace a kan mijinta shi ne ya girmamata, kuma ya tausaya mata da tausasawa, ya ciyar da ita, idan ta yi laifi ya yafe mata, kada ya la'ance ta ko ya zage ta ko ya doke ta, kada ya muzanta ta ko ya kunyata ta ko ya daidaita mata asiri.
Haka nan akwai hadisai da dama da suka zo game da falalar mutumen da yake taya matarsa aikin gida, don haka bai kamata ba al'ada ta rinjayi Addini, don wasu sukan ki hakan saboda wani dalili maras ma'ana na al'ada.
Dole ne miji ya yi adalci ga matarsa da tsakanin 'ya'yansa da matansa, kamar yadda yake wajibi a kansa ya nuna mata soyayyarsa, kuma ya nuna mata wannan a fili ta yadda zata zama abokiyarsa a komai. Kuma ya rika yi mata maganganu irin na soyayya da nuna kauna ga juna, bai isa ba ya ba ta kudi kawai don yana da shi, wannan ba ya isa ga bukatun mace. Shi ya sa Allah (S.W.T) ya fada a cikin littafinsa cewa: "Ya sanya soyayya (kauna) da tausayi (rahama) a tsakaninku"[39].
Haka nan ba shi da kyau ga miji ya munana zato ga matarsa, ko ba komai munana zato ga musulmi haramun ne, idan mace ta san mijinta yana munana mata zato alhalin tana mai kame kanta wannan yana iya rusa alakar soyayya da girmama juna da ke tsakaninsu har ya kai su ga rabuwa.
Hakkin Miji A Kan Matarsa
Daga cikin hakkin miji a kan matarsa shi ne: Kada ta ki shimfidarsa in ya neme ta, kada ta bayar da izinin shiga gidansa ga wanda ba ya son shigarsu, kada ta yada sirrinsa ko ta yi masa barnar dukiya, ta kula da yaransa da kuma ayyukansa na gida da suka shafeta, kada ta kausasa masa harshe, ta yi kokarin faranta masa rai. Sannan ta rika ba shi uzuri a kan wasu al'amuran, kada ta yi abin da zai sa shi ya ji baya son zama da ita a gida ko abin da zai sanya shi nisantar hira da ita ko kaurace mata.

Wasu ruwayoyi sun kawo hakkin miji kan matarsa kamar haka: Yayin da wani sahabi ya ba wa Manzon Allah (S.A.W) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki sai ta yaye masa shi, idan kuwa ba ya nan tana kare shimfidarsa ba ta ha'intarsa, kuma ta kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar 'ya'yansa. Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya ba shi amsa da cewa: "Allah yana da ma'aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidi"[40]. Haka nan wata ruwaya ta nuna cewa: "Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah"41.

Haka nan dole ne ta yi biyayya a gare shi[42] domin shi shugaba ne a gida babu kuma yadda mutane biyu zasu hadu a wuri ba tare da shugaba ba, ta sani rashin biyayya a gare shi yana rusa masa ruhinsa da karya masa zuciya, sai ya fara tunanin daukar fansa sai gaba ta faru, kuma zamansu ya gurbace, ko kuma wannan fushin ya tura shi ga miyagun halaye da kuma yawan fusata da fada.

Kada wata mata ta rika gasa da wasu mata ta ce: An saya wa kawata kaza kai ma sai ka yi min kaza wannan ko kadan ba shi da kyau. Yana da kyau mata su dauki samfurin rayuwar zamantakewa daga Imam Ali (A.S) da sayyida Zahara (A.S), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (A.S) ya shiga wajan Fadima (A.S) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu sai ta ce: "Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komai". Sai ya ce: "Me ya sa ba ki gaya min ba" Sai ta ce: "Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shi".[43]

Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (A.S) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado, kamar yadda maza su kuma su kiyaye ba kwauro ba barna.








                                                    Gabatarwa
"Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan aiki.."Surar Taubati, 9:71.
"Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al'ummu da kabilu (dabam-dabam) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah..."Surar Hujarati, 49:13.

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da tsarkaka daga lyalansa da zababbu daga Sahabbansa.
Zamantakewar dan Adam ba ta taba zama a wata rana cikin wadatuwa daga mace ba, alhali kuwa ita ke matsayin rabin samuwarsa ko ma fiye da haka. Duk wanda ya nutsa cikin zurfin tarihin dan Adam, zai ga cewa, hatta a lokutan da suka fi koyaushe ci baya, mace na da wata babbar gudummawa, duk kuwa da cewa wannan gudummawa ta faku daga gannai.

Idan har wayewar zamani ta fuskanci yin ta'akidi a kan gudummawar mace (a rayuwa) da ta da yekuwar kiyaye hakkokinta, duk da cewa na bayyane ne kawai, to Musulunci tun farkon bayyanarsa, ya yi kira kan cewa mace ta taka rawarta a rayuwa, kuma ta dauki nauyin da ya hau kanta wajen ginin wayewar bil-Adama. Allah Madaukaki Ya ce:­

"Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): `Hakika Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinsu, namiji ne ko mace', sashinku daga sashi yake..." Surar AIi-Imrana, 3:165. Idan har mace a lokacin jahiliyya ta kasance wani kashi da aka yi watsi da shi wanda kuma ya fada karkashin tsiraici da kaskancin matsayi, to a cikin zamantakewar Musulunci ta dawo ta zama mutum wadda ke da abin koyi ga sauran muminai. Tarihin Musulunci ya shaida wasu lokuta masu muhimmanci na wasu fitattun mata, kamar Uwar Muminai Khadija, da shugabar matan duniya Fadimatu (a.s.).

Wata kila karnonin karshe-karshen nan, saboda jahilcin da ya bayyana cikin wasu garuruwan Musulmi kamar sauran garuruwan duniya, sun shaida wani nau'i na kangiya ga mace daga irin tasirin ta na dabi'a, da hardiya ga tafiyarta na cika; abin da ke sanya tilascin yunkurar wa da tunatar da tunane-tunanen Musulunci da suka ta'allaka da ita, domin kuwa sanya mace a fagen da ya dace da ita cikin rayuwa, yana da babbar gudummawa cikin yunkurin al'umma da bunkasarta.

Babu shakka kan cewa wannan gudummawa ya saba da hakikanin yadda mace ke rayuwa a al'ummun da ke bin abin duniya na zahiri, wandanda suka janye wa mace karamarta da mutuncinta, suka so ta zama na'urar tallace-tallace a kafafan watsa labarai, kuma kayan wasa wadda masu kudi ke amfani da ita bisa son zuciyoyinsu; a karshe sai mace ta rasa matancinta, uwartakarta, daukakar tunaninta da taushin ranta, ba ta girbe komai daga hakan ma face ta'addanci, yin watsi da ita a gefe, yanke kauna, wahalhalu da shigar iyali cikin halin kaico da wastewa.

Binciken da ke hannunka, ya kai mai karatu, wata 'yar sassarfa ce a kan gudummawar mace da ayyukanta cikin al'umma bisa tunanin Musulunci. Muna fatan zai sami lura da muhimmanci daga gare ka.
Dukka godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.
Ma'anar Al'umma
AI'umma: na nufin tawagar nan ta mutane da ta hadu daga daidaiku, wadanda alakokina akida da amfanonin rayuwa iyakantattu suka hada su. Idan har wannan ne gamammiyar ma'anar al'umma, to al'ummar Musulmi ita ce wannan al'umma wadda ake gina alakokin kuma ake tsara amfanoni a cikinta bisa asasin Musulunci. Za mu iya ta'arifin al'ummar Musulmi da cewa:
"Taron Jama'ar da a siyasance suke zaune a wani lungu na kasa, wadanda suka yi imani da Musulunci, kuma ake tsayar da alakokinsu da tsarin rayuwarsu a bisa asasin Musulunci".[1]
Don haka al'ummar Musulmi al'umma ce ta akida, wadda ke da abubuwan da suka kebanta da ita da siffofinta da ke bambanta ta da wasunta na daga al'ummu. Ita al'umma ce da ta kebanta da tunane-tunanenta, halayenta, dokokinta, tsarin rayuwarta, dabi'unta da sannanta. Hakika AIkur'ani mai girma ya takaita wadannan siffofi da cewa:­ "Rinin Allah, ba kuwa wanda ya fi Allah iya rini, kuma mu Shi muke bautawa". Surar Bakara, 2:138..
Mafarin AI'umma
Daga cikin al'amura na asasi da babu makawa a kan karanta su, binciken su da bin diddiginsu a ilmance, akwai mas'alar nan ta tashin al'umma da rayuwar zamantakewa, da sanin dalilai da musababbin shi (tashin); saboda abin da ke cikin na murdewa da haduwa da alakoki.

Don bayyana ra'ayin Musulunci game da tashin al'umma da haduwar rayuwar zamantakewa, bari mu karanta abin da ya zo daga ayoyin AIkur'ani wadanda ke magana game da sha'anin zamantakewa, kuma suke kira zuwa ga ginin al'ummar dan Adam, da rina rayuwar mutum ta hanyar hada gamammen zaman tare bisa asasai karfafa da akidu tabbatattu; ga wasu daga cikin ayoyin kamar haka:­

"Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al'ummu da kabilu (daban-daban) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah..." Surar Hujarati, 49:13. "Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lalle cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu 33:21. "Shin su ne za su raba rahamar Ubangijinka? Mu ne muke raba musu arzikinsu a rayuwar duniya, kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima; rahamar Ubangijinka kuwa, ita ta fi abin da suke tarawa (na duniya)." Surar Zukhrufi, 43:32.
Darasi da bin diddigin wadannan ayoyi zai fitar mana da sabubba da dalilan tashin al'umma, wadannan sabubba kuwa su ne:­
1-Tubalin asali na ginin zamantakewa shi ne gamammun dokokin dabi'a na auratayya, wadanda suka hadu daga saduwar jima'i ga mace da namiji; ke nan su ne tubalin asasi na ginin rayayyen zamantakewa ta fuskoki biyu: Abin da zai auku a gaba da halayya.
Wannan alaka wadda ke nufin kariyar nau'i, kuma take tunkudawa zuwa jima'i don nufin jin dadi; ta dukkan bangarorinta biyu na halayya da `yan Adamtaka tana tsayawa ne a bisa asasin kauna, jin kai da samar da natsuwa.

Da wannan AIkur'ani ya dauki mace a matsayin tushen natsuwa ta hanyar tabbacin hankali da na zamantakewa ga namiji da rayuwar zamantakewa baki dayanta; wannan kuwa saboda kosar da rai daga son wani jinsi da jaraba ta jiki daga gare shi, suna haifar da kawar da damuwar rai da na zuciya, da cika irin faragar da rai din ke da shi, da sarrafa karfin bukatar jima'i da halayya don tabbatar da daidaici ga jinsosin biyu da ke tsaye a kan asasin cika ta hanyar gamammiyar dokar auratayya ta halitta.
Daga nan nauyin da ya rataya a wuyan mace wajen gina rayuwar al'umma mikakkiya kuma mai lafiya ta jiki da zamantakewa ke iyakantuwa; saboda ita ce mabubbugar natsuwa, kauna, tausayi da jin kai cikin rayuwar zamantakewa.

2-Sanayya: Abu na biyu da ke sa mutum hada rayuwar zamantakewa, shi ne ka'idar nan ta sanayya tsakanin mutane, abin da ke tsaye a bisa asasin nan na jin son zaman tare wanda masana falsafa ke nunawa da cewa: 'Mutum mai zaman tare ne bisa dabi'a". Jarabce-jarabce na halayya da zamantakewa sun tabbatar da cewa mutum ba ya jin tabbas da kwanciyar hankali, kuma mutuntakarsa ba ta cika sai da zamantakewa da rayuwa tare da wasu. domin shi yana da matsananicyar bukata ta rai kuma mai Zurfi zuwa ga wasu, saboda haka ne ma Allah Ya fad'i cewa: ".-don ku san juna"; kalmar sanin juna na nuni ne ga boyayyen abin da ke tura mutum zuwa zamantakewa da hada al'ummar dan Adam.
3-Musayar amfanoni: Sababi na uku daga sabubban gina al'umma shi ne musayar amfanoni na abin duniya dabam-dabarn. Hakika Allah Ya so daidaikun mutane su sami cika da irin karfi da kwarewarsu ta tunani, jiki da hankali, kuma wannan cika na tabbata ne ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaiku. Kowane mutum -shi kadai- yana da bukatu da wasu abubuwa da yake nema masu yawa, kuma ba ya iya samar wa kansa da su duka; don haka yana bukatar wasu, su ma suna da bukata da shi, wannan sabani cikin kwarewa wanda daga gare shi ne ake samun sabani cikin nau'o'in abubuwan da ake samarwa da hidimomin da mutum ke iya yi ga wasu, da musayar wadannan abubuwa da amfanoni da hidimomi don biyan bukatu, shi ne wanda AIkur'ani mai girma ya yi maganarsa da cewa:­
"..kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima..." Surar Zukhrufi, 43:32.

A bisa wannan asasi ne ayyukan zamantakewa ke faruwa, kuma (haka) ya fassara tubalin faruwar ayyuka a cikin al'umma don rayuwa ta sami cika kamar yadda gabubban jiki ke cika wajen cika ayyukansu.
Haka nan AlKur'ani ke yi mana bayanin abubuwan da ke haifar da al'umma, mutuntaka da abin duniya. Kuma cikin dukkan wadannan tubaloli da asasai, gudummawar mace na bayyana karara tun daga tushe, sawa'un ta bangaren abin duniya ne ko ta halayya ko aiki cikin rayuwar zamantakewa, ita babbar sashi ce ta al'umma. Hakika alkaluman mutanen duniya baki daya na nuna cewa adadin mata a duniyar dan Adam ya wuce adadin maza.

Ta wannan hange na cikan aiki da AIkur'ani ya bayyana a baya, za a iya ginin gudummawar mace kamar yadda ake ginin gudummawar namiji daidai-wa-daida cikin tsaikon manufofi da halayyar Musulunci, mace ba asasi ta biyu ba ce, ba kuma karin halitta ba ce, duk kuwa da cewa jarabce-jarabcen dan Adam sun tabbatar da cewa gudummawar namiji wajen gina ilimi da tattalin arziki ya fi gudummawar mace zurfi da yawa kuwa, amma nata gudummawar wajen hada shika-shikan ruhi don gina iyali ya fi gudummawar namiji girma nesa ba kusa ba kuwa. wannan shi ne abin da AIkur'ani ya nuna da cewarsa:­

"..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita". Surar A'arafi, 7:189. Ke nan namiji shi ne yake natsuwa zuwa ga mata, ya sami tabbaci da rayuwa tare da ita, ita ce cibiyar haduwa kuma tsaikon aminci, kauna da soyayya. AIkur'ani na magana a kan 'natsuwa' a wurare da yawa, ta nan za mu iya fahimtar ma'ana irin wadda mace kan samar ga mijinta, za mu fahimce shi ta hanyar fadarSa Madaukaki:­
"Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku.." Surar Rumu 33:21. Da fadarSa:­ "..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita". Surar A'arafi, 7:189.

Za mu fahimci kimar kalmar `Natsuwa' a zaman tare ne yayin da muka san cewa AIKur'ani ya siffanta alaka tsakanin miji da mata da cewa alaka ce ta (Natsuwa, kauna da soyayya).Ke nan bari mu karanto kalmar `natsuwa' a wurare da dama cikin AIkur'ani, don mu san ma'anarta a zamantakewa da iyali. Allah Madaukaki ya fadi cewa:­"(Allah) Ya sanya muku dare a natse" wato mutane na nastuwa a cikin shi natsuwa na hutawa. Haka nan Allah Ya fadi cewa:­ "Ka yi salla gare su lalle sallarka natsuwa ce garesu". wato suna natsuwa da addu'arka, kuma hankalinsu na kwanciya da ita. A wani wuri kuma Ya ce:­ "Shi ne wanda ya saukar da natsuwa a zukatan Muminai"

Ya samar da tabbas da kwanciyar hankali.Malaman harshen larabci sun yi wadataccen sharhi a kan kalmar, tare da bayar da misalai, inda duk suka fassara `Natsuwa' da: Kwanciyar hankali, rashin jin kadaici da duk abin da ka sami tabbas tare da zama da shi kuma ka huta da rayuwa tare da shi.[2]
Da haka za mu iya fahimtar natsuwar da mace ke samarwa ga mijinta da iyalinta, wato shi ne: hutawa, aminci, dauke kadaici, tausayi, albarka da tabbaci, kamar yadda za mu iya fahimtar sirrin zabar wannan kalma mai ma'anoni da yawa, da AIKur'ani ya yi.

Hakika darussa na ilimi sun tabbatar da irin tasiri da yanayin rai da halin mutum ke da shi a kan daukacin harkokinshi cikin rayuwa; saboda a tabbace yake a ilmance cewa ayyukan zamantakewa, alhakin aiki da neman abin duniya, na daga noma, sana'a, hada-hadar siyasa, zamantakewa da hidima ga al'umma kamar ayyukan gudanarwa, aikin injinya, karantarwa, aikin likita, kasuwanci, fannoni da sauran irinsu wadanda kowane daya daga namiji da mace ke yi; duk suna da tasiri kai tsaye daga yanayinsu na halayya. Namijin da ke raye a tsakiyar matsalolin iyali da damuwar zuci da bacin rai, samun shi ga abin duniya kadan ne, haka nan nashadinshi wajen aiki da tunanin kirkiran wani abu cikin ayyukan shi su ma suna tasirantuwa, kuma matsalarsa na karuwa wajen alakarsa tare da abokan aikinsa da wadanda yake da alaka da su.
Da haka dabi'ar alakokin auratayya tsakanin namiji da mace ke taimakawa wajen kyautata matsayin nema da samun, ta hanyar bayyanar tasirinsu na rai da zuciya a kan iyawar mutum da harkokinsa na yau da kullum, da alakarsa da neman abinci da abokan aikinsa.

Ba ma kawai wannan ba, Uwa na taimakawa wajen bunkasa al'umma da gina ta a tunani, abin duniya, da dabi'u ta hanyar tarbiyyantarwa da fuskantar da su; domin yaron da ya tashi nesa daga kunci da damuwar rai da matsalolin iyali, zai tashi mai mikakkiyar mutuntaka, mai kyakkaywar alaka da mu'amala da wasu, haka mai bayar da gudummawa mai kyau ga al'umma. Sabanin yaron da ya tashi cikin yanayin iyali da ke cike da matsaloli da tashe-tashen hankula da mummunar mu'amala ga yaro, irin wannan zai tashi ne birkitaccen mutum, mai adawa cikin dabi'u da alakokinsa; don haka ne ma mafi yawan halayen laifuka da mujirimanci cikin al'ummu na samo asali ne daga mummunar tarbiyya.

Akwai kuma wani fage daga fagagen ginin al'umma da Uwa ke taka rawa a cikin shi kamar yadda uba ke takawa, wannan kuwa shi ne fagen tarbiyya mai kyau.. Yaron da ke tashi a bisa son aiki da kiyaye lokaci, ake fuskantar da shi fuskantarwa ta karantarwa mikakkiya ta hanyar iyali, kuma yake ci gaba da karatunshi, kuma yana gina iyawarsa na kirkire-kirkire, zai zama wani da ake amfana da shi ta hanyar abubuwan da yake samarwa na kwarewa da sannai na ilimi. Sabanin malalacin yaron da iyayenshi ba sa kwadayin fuskantar da shi ga aiki da samar da wani abu, domin shi zai zama na'ura ga wasu, kuma irin wadannan na haifar da ci baya mai yawa da ta6ar6arewar samar da abubuwa da daskarewar rayuwar zamantakewa, tattalin arziki da ilimi.

Haka fagagen gini ke kulluwa tsakanin tarbiyya, samarwa da bunkasar tattalin arziki, halayya da zaman lafiyar al'umma, kuma irin gudummawar mace wajen ginin zamantakewa na bayyana a dukkan wadannan fagage.
Tubalin Ginin Al'umma
Alaka tsakanin daidaikun mutane a rayuwar zamantakewa kamar alaka ce tsakanin haruffan (wani) harshe, matukar wadannan haruffa ba su hadu ba kuma an tsara alakokin da ke tsakaninsu ba, gamammen ginin harshen ba zai samu ta yadda zai dauki tunanin mutum ya suranta jiyayyar rayuwar mutum gaba dayanta ba.
Haka ma daidaikun mutane, ba sa daukar siga ta mutuntaka da hada al'umma da ke da samuwarta da tushenta da ya bambanceta daga samuwa da tushen daidaiku sai sun shaje da wasu alakoki, sun tsaru da alakokin da ke tsara harkokinsu da halayensu, wadannan alakoki su muka sammata da Tubalan ginin al'umma, wadannan kuwa su ne:­

1-Akida: Alakar akida na daga mafi girman alakokin dan Adam wadanda ke hada daidaikun mutane ta mayar da su abu daya da ke hade kamar jiki daya; kamar yadda hadisin Annabi ya nuna haka da nassinshi:­ "Za ka ga Muminai cikin tausayin junansu da kaunar junansu da jinkan junansu kamar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta koka, sai sauran sassan jiki ya dauki zazzabi da hana barci".[3]
Akida na da tasirorinta da abubuwan da take haifarwa na halayya da jiyayya a aikace cikin alakokin mutane baki dayansu, kuma tasirorinta na fadada daga gini zuwa kyautatuwa da kiyaye ginin zamantakewa; don haka za mu sami AIkur'ani mai girma yana bayyana wannan alaka da cewa:­

"Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan alkl.." Surar Taubati, 9:71. Wannan aya mai albarka tana tabbatar da akidar kauna tsakanin maza da matan da suka yi imani da Allah Madaukaki da sakonSa, haka nan tana tabbatar da ka'idar tunani da halayya da suka fi kowace ka'idar ginin zamantakewa karfi. Mace na shiga cikin wannan alaka a matsayin wani tubali na asasi, kamar yadda ya zo cikin nassin AIkur'ani, tana shiga cikin da'irar soyayya, kuma tana daukar alhakin gini, sauyi da kawo gyara ga zamantakewa kamar yadda namiji ke daukar na shi daidai wa daida; wannan na bayyana karara cikin nassin AIkur'ani da ambaton shi ya gabata a baya.
Da wannan mace ke samun wannan matsayi na shakalin ginin zamantakewa, take kuma da nauyin da ya hau kanta ta hanyar alakar kauna ga daidaiku da al'umma da dukkan jinsosin biyu namiji da mace.
2-Dokoki da tsare-tsare: Ana ta'arifin doka da cewa ita ce: "Wasu gungun ka'idoji da aka tsara don halayyar daidaiku a cikin al'umma, wadanda kuma hukuma ke tilasta mutane a kan mutuntasu ko da kuwa ta hanyar yin amfani da Rarfi ne a lokacin da haka ya zama dole. "[4]

Don haka dokar zamantakewa ita ce hanyar da ke tsara harkokin al'umma, take kuma hada daid'aikunta, kuma take fuskantar da su da sha'anoninsu, kamar yadda dokokin dabi'a (na halitta) ke tsara motsin rana da wata da sauran irinsu. In ba tare da doka ba ba, za a iya gina surar zamantakewa ko bunkasata ba.
Dokokin Musulunci kuwa, su ne dokokin da aka ciro daga AIKur'ani mai girma da Sunna mai tsarki don tsara al'ummar Musulmi daidai da tunani da manufofin Musulunci, don su suna magance matsaloli a kan asasin ilimi; don haka ne ma (dokokin) suka yi la'akari da dabi'ar rai da jiki ga kowane daya daga namiji da mace. Bayan an gina su a kan kai'doji na ilimi, ana kasa dokokin Musulunci zuwa kashi uku kamar haka:­
a-Dokoki da hukunce-hukunce da suka kebanci mace. b-Dokoki da hukunce-hukunce da suka kebanci namiji. c-Dokoki da hukunce-hukunce gamammu da ke hawa kan namiji da mace baki daya, wadannan su ke da fadi a fagagen dokoki da hukunce-hukuncen Musulunci. Wannan nau'i na tsari mai la'akari da jinsi, yana kallafa wa mace, kamar yadda yake kallafa wa namiji, wanda kowannensu ke motsawa a fagage biyu, na farko a fagen da ya ke6anta da jinsinsa kuma da yanayinsa na jiki; na biyu kuma ya hado dukkan al'umma da duk gininshi da haduwarsa.

3-AI'adun Musulunci: AI'ummar Musulmi na da al'adunta wadanda ke matsayin wani tubali na asasi daga tubalan gininta wadanda suka kebanta da ita, wadanda kuma ya wajaba a kwadaitar a kansu a kuma tabbatar da su don kiyaye ka'idojinta.
4-Hidima da musayar amfanoni: Ta bayyana gare mu ta hanyar ayar nan mai girma: "..kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima..." Surar Zukhrufi, 43:32. Cewa bukatar zuwa ga wasu shi ne sababin asasi na shigar mutum cikin taron mutane da hada ginin Zamantakewa; don su shiga aikin musayar amfanoni, kamar yadda rayayyun abubuwa da dabi'a ke musayar amfanoni tsakaninsu a fagensu na dabi'a da ya kebanta da su. Ta haka mutum zai sami biyan bukatarsa, kuma ya taimaka wajen cikar rayuwar dan Adam.
A sakamakon bunkasar bukatun mutum da al'umma, da sabanin daidaikun mutane daga maza da mata wajen kudura da iyawa ta hankali da jiki da rai; da karfin irada, sai kebance aikin kowa ya faru a cikin al'umma a hankali a hankali ta wata fuska, ta wata fuskar kuma tare da zabin mutum ga aikinsa na zamantakewa, wato nau'in aikin da zai yi cikin al'umma, kamar noma ko aikin likita ko kasuwanci ko karantarwa da wasun su, ko wani mai tsare-tsare daga gwamnatin Musulunci, ta fuska ta uku, wato wanda nauyin tsara al'umma da fuskantar da kudurarta ke wuyansa, don biyan bukatun daidaiku da magance matsalolin da ke samo asali daga bukatu daban-daban. Cikin abin da zai zo za mu yi nazari gudummawar mace a wadannan fagage, mu dan yi bayani a kansu ko da kuwa a takaice ne.
Bambance-bambancen Yanayin Halitta Da Ke Tsakanin Namiji Da Mace
Daya daga cikin mas'alolin ilimi da kowa ya mika wuya garesu a tsakanin masana halayyar dan Adam da likitanci, shi ne cewa kowane daya daga namiji da mace na da yanayin halittarsa ta kebanta da shi, da cewa a dabi'ance dole a sakamakon haka ayyukan mace a cikin rayuwar zamantakewa ya saba da na namiji. don haka daidaitar rayuwar zamantakewa na bukatar kowane daya daga namiji da mace ya kiyaye bangare da yake ciki na jinsi, namiji ya kiyaye mazantarsa mace kuma ta kiyaye matancinta.
Hakika AIkur'ani mai girma ya yi bayanin bambanci halitta da ke tsakanin jinsosin nan biyu, abin da ya haifar da bambancin ayyuka, haka nan ya bayyana inda jinsosin biyu suka dace, Allah Madaukakin ya ce:­
"Kuma kar ku yi burin abin da Allah Ya fifita wasunku da shi a kan wasu. Maza na da sakamakon abin da suka aikata, haka ma mata suna da sakamakon abin da suka aikata. Kuma ku roki Allah daga falalarSa, hakika Allah Ya kasance Masani ne da dukkan komai". Surar Nisa'i, 4:32.
Haka nan hadisai sun yi ta'akidi a kan cewa mabayyanar kamala cikin mutuntakar kowane daya daga namiji da mace, suna da alaka da irin kebance-kebancen nau'i ga kowane daya daga cikinsu, da kiyayewarsa a kan su da daukakarsa da su, don haka hadisai suka hana kamantuwar mata da maza, kamar yadda suka hana maza ma hakan. Darussan halayyar dan Adam da gwaje-gwajen da aka gndanar A cikin hadisai akwai hani da tsawatarwa masu tsanani a kan irin wannan hali, kai! har ma sun la'anci irin mutane masu wannan hali.
Babban malamin hadisin nan kuma masanin furu'a Hurrul Amili (Allah Ya rahamshe shi) ya kawo hadisai masu yawa karkashin babin `Rashin halaccin kamantuwar mata da maza da maza da mata'.

An ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) da Imam Ridha (a.s.) cewa: - "Lalle ni ina kin namiji ya kamantu da mace'. [5]Ma'anar `ki' a nan shi ne haramci da rashin halalci, kamar yadda ya zo a sunan babin. Haka nan an ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) daga Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:­
"Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana tsawatar da maza kar su kamantu da mata, yana kuma hana mata kamantuwa da maza cikin suturarta".[6]
An karbo daga Ibin Abbas ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana tsinewa mazan da ke kamantuwa da mata, da matan da ke kamantuwa da maza.[7] Fayyace wadannan bambance-bambance zai haifar da amincewa a ilmance da bambance-bambancen ayyuka a wasu fagage da wajiban da aka kallafawa kowane daya daga namiji da mace. Daga wannan asasi ne bambance-bambance da inda ake tare cikin ayyukan zamantakewa ke iyakantuwa.
Mace Da Wayewar Duniyanci
Karanta tarihin al'ummu da kasashe a tsawon zamunansu, yanafito mana da wahalhalun mace, kuntata mata da takura mata. Babu wani tsari ko akida da ya yaye wa mace mayafin zalunci da kuntatawa in ba ka'idojin Allah da suka hadu da mafi kyawun surarsu a sakon Musulunci madawwami ba.
Kafin mu bayar da bayani game da kimar mace, hakkokinta da matsayinta mai ban sha'awa a Musulunci, yana da kyau mu kawo wasu alkaluman kididdiga wadanda ke magana a kan wahalhalun mace da masifun da ta sha a karkashin wayewar duniyanci na zamani karkashin jagorancin Amirka da kasashen Turai, wadanda ke daga taken 'hakkokin mace'.

Alkaluman kididdiga na ta'akidi a kan cewa, dan Adam din da ya ji jiki a karkashin wannan wayewa, kuma ya zama bawa da na'urar jin dadi shi ne: Mace. Ga wasu daga cikin alkaluman kiddidiga na cewa:­
"Wani rahoto da kamfanin dillacin labaran kasar Faransa ya kawo ya bayyana cewa: kashi 70 bisa dari na mutane biliyan 1.3 da ke raye a cikin halin mugun talauci a duniya su ne mata, kuma akwai kimanin mata biliyan 2.3 da ba su iya karatu da rubutu ba a duniya. Haka nan kashi uku bisa hudu na daukacin matan kasashen Norway, Amirka, Holland da Newzaland na fuskantar hare-haren fyade. AAmirka kuwa, cikin kowadanne dakikoRi 8 mace daya na fuskantar mummunar mu'amala; haka cikin kowadanne dakikolti 6 ana sace mace daya"[8]

Rahoton ya kara da cewa:­ Kimanin mata rabin miliyan daya ke mutuwa a kowace shekara saboda ciki da suka dauka da cutukan shi, kuma kimanin kashi 40 bisa dari na wannan adadi yan mata matasa ne. Kuma albashin mata miliyan 828 da ke aiki a fagagen tattalin arziki ya fcaranta daga albashin maza da abin da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa kashi 40 bisa dari, kuma irin dan tagazawar nan na bankuna da ake ba ma'aikata a duniya ba sa samun fiye da kashi 10 bisa dari na wadannan agaje-agaje".[9] Haka nan ya zo cikin wani rahoton cewa:­

"A bisa wani bincike da ma'aikatar adalci ta kasar Amirka ta aiwatar, an gano cewa adadin sace mutane ko yunkurin sace mata na faruwa a Amirka har sau 310 a kowace shekara, wannan kuwa ya ninka alkaluman da hukumar 'yan sandan cikin Amirka ta F.B.I. ta bayar."[10]
Kuma kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga Washigton ya bayar, a kowace shekara akwai halin yi wa mata fyade har sau rabin miliyan a Amirka; alhali kuwa hukumar 'yan sanda ba ta bayar da sanarwar adadin samuwar sace (mata) ko yunkurin sace su a Amirka ba face dubu 140, kamar yadda alkaluman kididdigar hukumar F.B.I. ya bayyana..

Haka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar kasar Iran mai suna lddila'at ta bayar a adadinta na 20,401 daga kamfanin dillancin labaran Iran da ke birnin Rom na kasar Italiya, cewa:­ "Matsalar halayyar rashin tausayi na kara matufcar tsananta a tsakanin iyalan Italiyawa, domin halin kashe iyaye a hannun `ya'ya da kashe 'ya`ya a hannun iyaye ya karu fiye da yadda ya kasance a da can. Haka wata jaridar Kasar Italiya, a adadinta na baya-bayan nan, ta dauko wani rahoton Kididdigar shekara-shekara na kungiyar Eruospas cewa: cikin watanni goman farkon na shekara ta 1994, an rubuta halin rashin tausayi har 192 a cikin iyalan Rasar Italiya, wadanda 129 daga wannan adadi suka Kare da kisa. Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, irin wannan nau'i narashin tausayi a shekara ta 1993 adadin shi ya kai 112, wanda kusan wannan adadin ya kare da halin kashe-kashe. wani abu, da ya zama dole a nuna shi ne cewa kimanin kashi 40 bisa dari na laifuffukan iyali ya faru ne a arewacin Italiya, kuma kashi 40.8 bisa dari daga cikinsu sun faru ne a kudancin kasar, alhali kashi 16.1 bisa dari ya faru a tsakiyar kasar. Kuma mafi yawan kashe-kashen iyali da aka yi a shekara ta 1994 sun faru ne a lardin Lombardi da ke arewacin Italiya".

Haka nan jaridar 'Jumhuri Islami', a adadinta na 4,485, fitowarta shekara ta 1994, ta bayar da rohoton cewa:­'MujallarEpidemiology (ilimin annoba) da ke Karkashin hukumar lafiya ta duniya (WHO), a adadinta na 11, na shekara ta 1993 ta rubuta alkaluman Kididdiga na karshe da ya Kunshi adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki (AIDS) a duniya baki daya, inda aka rarraba alkaluman daidai da yankunan duniya dabam-dabam. Alkaluman na nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki da suka tabbata ga wannan hukuma har zuwa shekara ta 1993, ya kai kimanin 718,893. Kimanin 371,086 na wannan adadi na wadanda suka kamu da cutar Kan jiki sun fito ne daga nahiyar Amirka, yayin da kimanin 247,577 suka fito daga nahiyar Afrika, kimanin 92,482 kuwa sun fito ne daga nahiyar Turai, adadin da ya kai 4,188 sun fito ne daga Australiya, 3,561 kuwa daga nahiyar Asiya. Wan aka bi kasa-Kasa kuwa, Kasar da ta fi kwasan adadi mai yawa ita ce Amirka, wadda ta kwashe adadin wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta kimanin 289,320, sai kuma kasar Tanzaniya da ke biye mata da kimanin 38,719, sai Kasar Birazil mai 36,481, sai Kenya da 31,185, sai Uganda mai 34,611, sai kuma Biritaniya mai 26,955, sai Faransa mai 24,226, sai kuma kasar Zaire mai 21,008, sai Spain mai 18,347, sai Italiya mai 16,860, sai Congo (Brazavill) mai 14,655, daga nan sai sauran kasashe su biyo baya. Kamar yadda za a iya lura, ba kawai kasar Amirka namatsayi na daya ba ne ta fuskar adadin wadanda suka kamu da cuta mai karya garkuwa jiki, a'a har ma akwai sabani mai yawan gaske tsakanin ta da Kasashen da ke biye mata. Kuma idan muka dauki wadannan alkaluma na adadin dari, za mu sami wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta a kasar Amirka sun kai kashi 40 bisa dari na dukkan wadanda suka kamu da ita a kasashen duniya 150, wannan kuwa duk da cewa adadin mazauna Amirka bai wuce kashi 5 bisa dari na dukkan al'ummar duniya
ba'.


Haka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar Ittila'at ta kasar Iran ta kawo, a adadinta na 20,482, fitowarta ta 21 ga watan Maris na shekara ta 1995, daga wakilinta a Madrid ta kasar Spain, inda yake cewa:­ "A shekara ta 1995 kashi 72 bisa dari na Rananan yara na raye ne a KarKashin ubanninsu, amma yanzu kimanin kashi 60 bisa dari daga cikinsu suna raye ne ba tare da ubanni ba. Yawan saki da fitinun uwaye sun sa maza sun gudu daga gidaje. Marubucin nan dan Kasar Amirka (David Blanc Horn), bayan ya bayyana wadancan alKaluman Kididdiga a cikin wani littafi na shi, ya kuma bayyana cewa: "Samun iyaye maza na gari na buKatar samun kyakkyawan misali na mata (wato yana bukatar samun mata na gari), wannan shi ne dalilin gudun iyaye maza daga gidajensu a Amirka.' Haka nan wakilin jaridar Faes ta Fcasar Spain, a wani rahoto na shi da ya bayar daga Amirka, ya bayyana cewa: Himmatuwa mai yawa da matan Rasar Amirka ya kare da cutar da ubanni da haramtawa `ya `ya inuwar ubanninsu".
A wani rahoto da jaridar Itiila'at, a adadinta na 20,407, fotowar ranar 31 ga watan Yulin shekara ta 1995 ta dauko daga ofishin kamfanin dillancin labaran Iran (IRNA) da ke London game da yanayin da kananan yara ke cikin a Biritaniya, am bayyana cewa:­"Majalisar Dinkin Duniya, a wani rahoto nata, ta yi kakkausar suka a kan yanayin da yara ke ciki a Biritaniya, da kuma dokoki da tsarin lura da yara a wannan kasa. Rahoton, wanda hukumar kiyaye hakkokin yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, ya nuna cewa dokokin da ake amfani da su a kan abin da ya shafi lafiya da ilimin kananan yara da shigar da su cikin al'umma a Biritaniya, ba a yi la'akari da cewa ya wajaba dokokin su lura da amfanonin yaran ba. Masana a hukumar kiyaye hakkokin yara ta Majalisar Dinkin Duniya na ganin cewa dokokin da suka kebanci kananan yara a Biritaniya sun fi mayar da hankali a kan yin ukuba da kulle yara da balagaggun matasan da suka karkace.
Daga cikin wuraren da ake suka a cikin wannan rahoto akwai karuwar yawan kananan yara da ke rayuwa cikin halin talauci a Biritaniya, da karuwar alkaluman rabuwar aure, da raguwar tallafin hukuma ga matalautan iyalai, da karuwar yawan yara da samari da ke sake suna kwana a tituna.
Haka nan masu rubuta rahoton sun bayyana damuwarsu da mummunar mu'amala da amfani da miyagun kwayoyi da fyade da ke fuskantar kananan yara.
Kamar yadda majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana, rahotannin majalisar game da yanayi kananan yara a kasashen Sweden, Norway da Denmerk sun yi soke-soke kamar irin na rahoton kasar Biritaniya".
Haka nan ya zo cikin jaridar Jumhuri Islami, a adadinta na 4,485 cewa:­"Ofishin kamfanin dillancin labaran Jumhuriyar Musulunci ta Iran a Born (ta fcasar Jamus) ya bayyana rahoton hukumar kidaya ta kasar Jamus (a shekara ta 1993) na cewa: adadin `ya `ya mata da ubanninsu ke tarbiyyantar da su su kadai yana ci gaba da karuwa a kowace shekara. Rahoton ya kara da cewa: A halin yanzu akwai kimanin uwaye mata dubu 455 a jihohin Jamus ta gabas (wato kashi 12 bisa (Tari na jimillar uwaye mata da ke wadannan jihohi ke nan) da ke tarbiyyantar da ya yansu su kadai. A gefen wannan kuma, daga uwaye mata miliyan 7 da ke jihohin Jamus ta yamma, kimanin dubu 915 (wato kashi 12 bisa dari) na uwaye matan suna daukar dawainiyar tarbiyyar 'ya `yansu su kadai. Da wannan ke nan zai zarna akwai kimanin uwaye mata miliyan daya da dubu 370 a tsakanin uwaye miliyan 9 da dubu 260 da ke tarbiyyar 'ya`yansu su kadai a tarayyar Jamus.
Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, kashi 46 bisa dari na wadannan uwaye a gabashin Jamus, da kashi 30 bisa dari daga yammacinta duk ba su yi aure na shari'a ba; kashi 43 bisa dari na wadannan uwaye kuwa mazajensu sun sake su, kasancewar kuma rike 'ya’ya a hannun uwaye mata yake, ya zama musu dole su dauki dawainiyar tarbiyyarsu.
Haka nan a kasar Jamus akwai fiye da uwaye mata miliyan 9.26 da suka haifi 'yaya alhali shekarunsu na haihuwa bai kai 18 ba, kuma miliyan 5.4 daga cikinsu ko da yaushe ko rabin lokutansu suna ayyuka ne a wajen gida, banda kuma ayyukansu na gida da ayyukan tarbiyyar yara. Wani abu da ya kamata a bayyana a nan shi ne cewa yawan halin rabuwar aure a halin yanzu ya ninka yadda ya kasance a shekara ta 1968, wato ya karu daga dubu 65 da ya kasance a shekara ta 1968 zuwa dubu 135 a ‘yan shekarun nan, kuma a kowace shekara ana rijistar aurarraki dubu 390 a kasar Jamus, wadanda kashi 33 bisa dari daga cikinsu ke karewa da rabuwa, har ma wannan adadin a manyan garuruwa irin Hanburg ya kai kashi 50 bisa dari".
Har ila yau jaridar Ittila'at a adadinta na 20,503 ta dauko wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillacin labaran Iran (IRNA) ya kawo kamar haka:­
"Taimakon kasar Amirka ga hukmar (UNICEF), bai kai na kasa daya daga cikin kasashe 20 masu arzikin masana'antu a duniya ba.Bankin kula da Kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ma ya tabbatar da haka, ya kuma kara da cewa: Duk da Amirka da ke bayar da taimakon dala biliyan 9.7, ita ke martaba ta biyu bayan Kasar Japan wajen taimakawa hukumar UNICEF, wannan adadin kudi kuwa ba komai ba ne face kashi .15 bisa dari din kudaden shiganta, alhali kuwa Rasar Holland da sauran kasashen yankin Sakandanebiya su ke marhala ta daya a wannan fagen; domin taimakonsu na kaiwa kahi 8 bisa dari na kudaden shigansu. Shugabannin hukumar UNICEF sun nuna damuwarsu a kan raguwar taimakon da kasashe masu zarafi ke yi ga matalautan kasashe, har ma sun kara da cewa: 'Wannan abu na faruwa ne a daidai lokacin da rnuhimmancin taimakawa wajen kyautata lafiyar Kananan yara da kyautata yanayin ayyukan uwaye mata ke Karuwa a matalautan kasashe da tsananin gaske kuwa.' Kuma kamar yadda wannan rahoton ya nuna, a kowace shekara Kananan yara kimanin miliyan 13 a duniya ke mutuwa saboda cututtukan gudawa, bakon-dauro da sauransu.Haka nan kimanin Kananan yara miliyan 200 ke fama da rashin abinci mai gina jiki irin su vitamin A, abin da ke haifar musu da makanta!". Har ila yau ya zo cikin jaridar Ittila'at, a adadinta na 20,370, fitowar ranar 15 ga watan Disamban shekara ta 1994 cewa:­
"Kamfanin dillancin labaran Jumhuriyar Musulunci ta Iran (IRNA) daga Tehran ya bayarda labarin samuwar kananan yara kimanin rabin miliyan wadanda suka tarwatse a Amirka, a wasu lokuta ana aje su a wajen neman gina marayu, abin da al'ummar Amirka ke dauka a matsayin Kaskanci garesu. Wata marubuciya a jaridar Washintog Post mai suna Suzan Phildaz, ta rubuta cewa: 'Da yawa daga kananan yaran da ke da majibinta wadanda ke raye a karkashin iyalan da ke taimakonsu, suna fuskantar duka, wulakanci da mummunan mu'amala, kai! awasu lokuta ma ana kashe su.' Har ilayau Phildaz nacewa: 'Nau'in mu'amalar kowace al'umma tare da 'ya'yanta wata muhimmiyar alama ce da ke nuna hakikanin wannan al'umma.' Har ila yau ta kara da cewa: Adadin kananan yara da ke watse sai kara yawa yake yi a Amirka kullum, har ta kai ga a wasu lokuta `yan sanda na gano jarirai a wuraren tara juji. A irin wannan hali taimakon uwaye mata na kudade ba ya wadatarwa, maimakon haka, babu makawa a samar da wasu cibiyoyi don amsa manyan bukatun wadannan kananan yara."
Mace a Inuwar Musulunci
Ina Dalilin Sukar Matsayin Musulunci Game Da AI'amarin Mace?
Nazarin wannan al'amari (na hakkokin mace a Musulunci) na daga cikin manyan al'amurra na tunani da wayewa a wannan lokaci da muke ciki. Masu fada da Musulunci, `yan amshin Shatansu da wad'anda suka jahilci tunane-tunanen Musulunci, basu gushe ba suna ci gaba da kai hare-harensu na zalunci a kan tunane-tunane da shar'ance-shar'ancen Musulunci, suna masu ikirarin cewa anzalunci mace a Musulunci.
Ta hanyar nazari da bin diddigin asasan wannan yaki na tunani (game da hakkokin mace) tsakanin Musulunci da akidar abin duniya na zahiri da bai yi imani da addini ba, zai bayyana mana cewa tsaikon ka-ce-na-ce din duk ya kewayu ne a kan wani al'amari na asasi, shi ne tunanin rashin imani da addini da ke kira zuwa ga sakewa da kwance duk wani kaidi ga jima'i; wato wannan ra'ayi da a cikin shi mace ta zama wata na'urar jin dadi da biyan bukatun jaraba, wad'anda ke haifar da wargajewar iyali da al'umma da mace. Alhali kuwa Musulunci na kira zuwa ga karrama mace da dage wannan matsayi na wulakanci, da ba ta hakkoki da matsayin da suka ba ta daman yin kafada da kafada da namiji wajen gina rayuwa, da bayyana mutuntakarta a kan asasin 'yan Adamtaka madaukakiya, wadanda za mu yi bayaninsu a takaice a wannan babin.
Kafin mu fara magana a kan wannan babi, ya kamata mu bayyana manyan sabubban wannan ka-ce-na-ce (na hakkokin mace), da dalilan sukan Musulunci na cewa ya tauye mata hakkokinsu.
Marubuta, manazarta, masu da'awa zuwa ga Musulunci, malamai da kungiyoyin kira da wayarwa ta Musulunci, masamman ma wadanda ke zaune a kasashen da ba na Musulmi ba, masamman a kasahen Turai da Amirka; dukkansu suna aiwatar da wajibin da ya hau kansu na bayanin wannan mas'ala mai muhimmanci ta hanyar bincike-bincike, nazarce-nazarce, da tarurrukan karawa juna ilimi a dukkan fagage, na siyasa, halayyar dan Adam, zamantakewa, iyali da zaman gari dabam-dabam.
Mafi girman dalilan da ke boye a karkashin wad'annan hare-hare da ake yi wa tunane-tunanen Musulunci a wannan fage, ana takaitasu cikin abubuwa masu zuwa:­
1-Ta'allaka wasu al'adu da suka ci baya da nazarin zamantakewa a Musulunci: Daga cikin al'amurra na asasi da ya wajaba a kan marubuta, wayayyun Musulmi da masu kira zuwa ga Musulunci su yi bayaninsu, akwai kuskuren da masu jayayya da Musulunci ko wadanda suka yaudaru da tunanin abin duniya na zahiri ko wadanda ma'anoni suka cakude musu kuma mummunar fahimta ta yi galaba suke yi, wannan kuwa shi ne cakudawa da rashin rarrabewa tsakanin abin da Musulunci ya ginu a kai na halaye da ka'idoji na Musulunci, da al'adun zamantakewa na ci baya da suka taso a wasu kasashen Musulmi da ba su waye ba. wadanda kuma suke sabawa ruhin Musulunci da ka'idojinshi da tsare-tsaren zamantakewa da alakokin jima'i da asasan alaka tsakanin namiji da mace; don haka sai suka shiga danganawa Musulunci -bisa jahilci ko da gangan- duk abin da suke shaidawa a kasashen Musulmi. A nan babu makawa mu yi ishara ga bambancin da ke tsakanin yadda al'ummar Musulmi take a halin yanzu da yadda ya kamata al'ummar Musulmi da ke tsaye a kan asasan Musulunci take, mun kuwa riga mun yi ta'arifin (bayanin ma'anar) al'ummar Musulunci.
Hakika wannan ci baya na zamantakewa da al'ummar Musulmi ke fama da shi, wani yanki ne na gamammen ci baya a fagagen ilimi, sannai, bunkasa, masana'antu, lafiya da saurarnsu.
Mummunan surar da wasu masu bincike game da zamantakewa ke cirowa daga yanayoyin zamantakewa dabam-dabam, kamar nazarin nan da aka gudanar a kan yanayin zamantakewar mace a kauyen Masar ko Iraki ko Maroko ko yankin saharar tsibirin larabawa da wasunsu; duk suna fitar da matsalolin mace ta hanyar hangen kauyanci da sahara wadanda suka ci baya kuma suke zaluntar mace.sa'an nan sai wadannan nazarce-nazarce suka shiga bayar da misali ga zamantakewar Musulunci da su.saboda mutanen wadannan wurare Musulmi ne. sun gafala da cewa wadannan tunane-tunane da ayyuka ba su da wata alaka da tunane-tunanen Musulunci da ayyukansa. kuma ba kawai suna karo da halayya da hukunce-hukuncen Musulunci ba ne. a'a har ma Musulunci ya kebe wani sashe daga tunane-tunanensa da dokokinsa da halayyarsa don yaki da su da sauya su.
2-Jahiltar Musulunci: Daga cikin matsalolin da ke tunane-tunanen Musulunci ke fuskanta a wannan lokaci da muke ciki, akwai jahiltar Musulunci da wasu ke yi, masamman ma a kasashen Turai, Amirka da sauran nahiyoyin da ba na Musulunci ba. Wadannan na jahiltar mafi karanci daga ka'idojin Musulunci.kai! suna ma yi mishi wata mummunar fahimta karkatacciya da ke siffanta Musulunci da siffofin: bata, ta'addanci, zubar da jini, ci baya da tsattsuran ra'ayi. Wadannan tunane-tunane na daga abubuwan da kungiyoyin Mustashrikai (masanan Turawa da su ke karantar halayyar kasashen Musulmi da addinin Musulunci don manufofi dabam-dabam), Sahyoniyawa(kungiyar Yahudawa masu tsaurin ra'ayi).da kungiyoyin Coci-Coci da mishan-mishan na Majami'an Kiristoci suka sana'anta.
Babu wata surar hakikanin Musulunci a kwakwalwar mutumin yamma, maimakon haka, duk abin da ke cikin kwakwalwarsa da fahimtarsa itace mummunan sura. kuma da mutumin yammaci ya san hakikanin Musulunci da ya yi maraba da shi. kuma da ya bude hankalinsa don yin muhawara ta ilimi. haka da ya karbe shi da `yanci da budaddiyar kwakwalwa.
A takaice za mu iya karanta wannan babbar matsala cikin jawabin da shugaban kasar Jamus Roman Hutsog ya yi a ranar 10/1/1995 a lokacin bikin girmama baturiyar nan masaniyar kasashe da al'adun Musulmi (Mustashrika) a kasar Jamus, Anamari Shamel, mai adalci cikin abubuwan da take rubutawa da fada, a lokacin bukin bata kyautar zaman lafiya da kungiyar marubutan kasar Jamus ta ba ta. Ya fadi abin da ya fada ne yana mai mayar da martani ga masu sukan kyautar zaman lafiya da aka ba Shame[ saboda kawai tana kariya ga tunane-tunanen Musulunci, kuma tana mu'amala da shi bisa gaskiya da adalci.tana kuma kira zuwa fahimtarsa da sauya mummunar surar da kafafan watsa labaran Turawa ke yi ga Musulunci da Musulmi; sai ya ce:­
"Akwai wani al'amari da ke bayyane karara cikin alaka da mu'amalarmu da Musulunci a wannan lokacin da muke ciki. Ba za mu yi karya ga ra'ayin da ya watsu a Jamus ba, idan muka ce: abin da ke zuwa cikin tunanin mafi yawanmu a duk lokacin da aka ambaci Musulunci shi ne: `Dokokin uKuba na rashin tausayi' ko `rashin sassaucin addini' ko zaluntar mace ko tsaurin ra'ayi irin na adawa. sai dai wannan Kuntata yanayi ne da ya wajaba mu sauya shi; mu tuna da ambaliyar nan ta hasken Musulunci wadda tun kafin Karnoni shida ko bakwai ta kiyaye wa kasashen yammaci wani sashe babba na tsofaffin abubuwan tarihi, wadda kuma a wancan lokacin ta sami kanta a gaban wani irin nau'i na tunanin yammaci; babbu shakka (wannan ambaliya) ta ji cewa ashi (wannan nau'i na tunanin yammaci) mai tsaurin ra'ayi ne mara sassauci".
A yankin karshe na maganarsa, shugaban na Jamus ya yi bayanin dalilin adawa da Musulunci da cewa shi ne jahiltar da Turawa suka yi wa Musulunci, kan haka za mu same shi yana cewa:­
"Ashe ba ta yiyuwa dalilin rashin fahimtarmu ga Musulunci ya zamashi ne ginuwarsa a kan asasai masu zurfi na al'umma mai riKo da addini alhali mu masu riko ne ta fuska mai girma da wani tafarki da bai yarda da addini ba? danhaka ya tabbata ya ya za mu yi mu'amala da wannan nazari mai matsala? Shin ya yi daidai mu siffanta Musulmi masu tsoron Allah da siffofin `masu tsattsauran ra'ayi, 'yan ta'adda' don kawai mu mun rasa ingantaccen riskar yadda izgili yake a zukatan mabiya wasu addinai, ko kuwa saboda mun zama ba za mu iya bayyana irin wannan ingantacciyar fahimta ba?".
Daga nan sai shugaban na Jamus ya bayyana cewa shi bai san Musulunci yadda ya kamata ba sai bayan da ya karanta littaffan wannan Mustashrika mai adalci (wato Shamel), sai ya ce:­ "Tsinkayata ga irin wannan babban nau'i na fuskance-fuskance cikin tarihin Musulunci da hakikaninsa a halin yanzu bai fara ba sai ta hanyar littafan Anamari Shamel, akwai kyakkyawan zaton kuma cewa wasuna ma sun fuskanci irin wannan gwaji. Hakika muna bukatar musanya abin da ya kuke mana na fahimtar sashinmu ga sashi... ".
Sannan sai shugaban na Jamus ya yi kira da a fahimci Musulunci don shata wani matsayi game da shi koma bayan matsayin da ya ginu a kan jahiltar sa, sai ya ce:­ "Ina yin ikirari da cewa a gabanmu babu wani zabi face kara samun masaniya game da duniyar Musulmi matukar muna nufin yin aiki don kare hakkin dan Adam da Dimokuradiyya".
Sai kuma ya kara da cewa:­ "Hakika babban dalilin son sanin Musulunci da fahimtar wadatacciyar wayewar nan ta shi ya samo asali ne daga kasancewarmu cikin wata wayewa da ba shi ba. Hakika kuwa uwargida Shamel ta fadaka da wannan bukata ta rai, ina fata kuma wannan ya zama shi ne yadda wasuna masu yawa ke ji..". "Hakika Uwargida Anamari Shamel ta share mana fagen haduwa da Musulunci.. [11]
Hakika wannan rikici na bayar da kyautar zaman lafiya a kasar Jamus ga masaniyar kasashe da al'adun Musulmi (Shamel) a shekara ta 1995, da dacewan `yan siyasa da wayayyu daga ma'abuta tunani, shehunnan malamai, Turawa masana kasashen Musulmi da al’adun Musulunci, ma'abuta fanni da adabi a kasar Jamus, wadda ake dauka daga cikin manyan daulolin duniya a tarihin wannan zamani namu, da nasarar bangaren Shamel, wato masu kira zuwa a fahimci Musulunci a bisa hakikaninsa don shata matsaya, daga cikin wadanda ke sahun gaba na wadannan kuwa har da manazarta da 'yan siyasa, a cikin su har da shugaban kasar Jamus wanda muka karanta muhimman zantuttukansa; duk yana nuna mana wani abu ne mai girma daga abubuwan da ke wuyan Musulmi marubuci, manazarci kuma ma'abucin fanni da adabi. kamar yadda ya ke wuyan cibiyoyi da malaman addini. wannan kuwa shi ne nauyin yin bayanin Musulunci a bisa hakikaninsa mai haske. wanda yake tafiya tare da hankali da zuciya cikin sauki. tahanyar aiki da tafarkin nan na AIkur'ani wajen kira zuwa ga Allah Madaukaki:­
"Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau, kuma ka yi muhawara da su kan abin da yake shi ya fi kyau.." Surar Nahali, 16:125.
Wannan ka-ce-na-ce na wayewa da ya faru a Jamus da yadda ya kare da nasarar masu kira zuwa ga fahimtar Musulunci, yana tabbatar mana da girman Musulunci, da shirin da d'an Adam ke da shi na fahimta da karbar Musulunci, duk kuwa yadda ya kai da isa. Wannan ka'ida da AIKur'ani ya tabbatar da ita da fad'arsa:­
"Ku tafi zuwa ga Fir'auna don kuwa hakika ya yi tsaurin kai. Sannan ku gaya masa magana mai taushi, ko watakila zai karbi gargadi ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah)". Surar Daha, 20:43-44.
Daga nan za mu fahimci cewa Alkur'ani na horon masu kira zuwa ga Musulunci da su kare tunanin imani, kuma su yi magana ta Musulunci (hatta) ga wadanda suka fi kowa adawa da tsanantawa da kin imani, kuma kar su fada tarkon yanke kauna har su rufe kofar yin muhawara ta tunani.domin yanayi da halayen da ba a karbar zantukan Musulunci a cikinsu suna da sabani daga wata marhala zuwa wata, kuma daga wani yanayi na rai, zamantakewa, al'adu da tarihi zuwa wani; domin (da yawa daga) abin da aka ki karba a yau, ana karbarsa a gobe, kuma abin da aka ki yarda da shi ta wannan hanya, ana karbarsa ta wata hanyar.
3- Sha'awa da karkacewa ta jima'i: Watakila daga mafi bayyanar sabubban wad'annan da ke kira zuwa ga 'yancin mace ko sakewar jima'i akwai sababi na sha'awa da karkacewar jima'i. Hakika Alkur'ani mai girma ya yi magana game da wannan sababi, ya kuma bayyana had'arinsa da mummunar akibarsa. Allah yana cewa:­
"...Sai wasu suka maye gurbinsu a bayansu, wadanda suka watsar da Salla suka kuma bi sha'awace-sha'awace; to ba da dadewa ba za su gamu da gayyu (wani kwari ne na azaba a jahannama)". Surar Maryam, 19:59.
Ya kuma ce:­"An kawata son sha'awace-sha'awace na mata da `ya'ya da dukiyoyi tsibi-tsibi na zinariya da azurfa ga mutane..." Surar Ali-Imrana, 3:14.
Ya kuma ce:­ "..Wadanda kuwa suke bin sha'awace-sha'awace suna so ne su kauce mummunar kaucewa". Surar Nisa'i, 4:27.
A cikin wadannan ayoyi Alkur'ani na bayani ne game da hadarin sha'awace-sha'awace, da cewa suna samo asali ne daga jahilci da ya samo asali daga mummunan akida, da karkacewa daga madaidaiciyar hanya, wanda bayaninsu ya zo karara a wata ayar:­
"Wadanda suke kawo cikas a hanyar Allah, suna kuma son ta karkace alhali su masu kafircewa ne da ranar lahira". Surar Hudu, ll:l9.
Abin da muka gabatar na alkaluman kididdiga suna magana a kan karkacewar jima'i saboda wasu dalilai na ayyuka da Alkur'ani ya yi bayaninsu ga mutane ya kuma tsawatar a kansu.
4-Mugun kulli na gado da tsoron Musulunci: Daga cikin sabubban kai hari ga Musulunci da yi wa matsayinshi game da mace bakin fyanti, akwai mugun kullin da aka gada a kan Musulunci da yin aiki wajen munanta ka'idojinsa da daukakan halayensa tun daga bayyanar Manzon Allah (s.a.w.a.), wanda kuma ya ci gaba har zuwa yakokin gicciye. Duk wannan saboda tsoron Musulunci a matsayin shi na wani shiri na wayewa wanda ke rushe amfanoninsu da suka haddasa, kuma ba su gushe ba suna haddasawa a duniyar Musulunci, kuma yana gamawa da wuce-iyakarsu da mamayarsu ga duniya, masamman ma duniyar Musulmi; masamman bayan bayyanar wayewar Musulunci da bayyanar Musulunci a matsayin wani shiri da yunkure-yunkurenshi ke ginuwa, kuma wani rayayyen gwajin da ya aikatu ta hanyar tsayar da gwamnatin Musulunci a Iran.
Hakika kuwa manyan kasashen duniya sun watsa karti datsare-tsarensu, suka watsa'yan barandansu a ko'ina don yaki da wayewar musulunci, da sukar shirinshi da masu kira zuwa gare shi da wadanda ke dauke da tutarsa.
Mace a Rayuwar Annabawa (A.S)
Hakika mace ta kasance tana da babban kashi hayyananne a tafiyar kira zuwa ga Allah da yunkurin Annabawa da Manzanni (a.s.). Hakika mace ta taka muhimmiyar rawa wajen yakin tunani da siyasa, ta kuma sha azaba, kisa, hijira da dukkan nau'o'in wahalhalu da ta'addancin tunani, siyasa da fin karfi. ta kuma mike ta bayyana ra'ayinta bisa 'yanci, ta shiga cikin kira zuwa ga Allah, duk kuwa da abin da ya same ta na hasarar mulki, matsayi da dukiya; da abubuwan da ta hadu da su na kora, kisa da ta'addanci.
Misali a kan haka ita ce Maryam Uwar Annabi Isa (a.s.), wadda AlKur'ani ya girmamata kamar yadda Annabin Musulunci (s.a.w.a.) ya girmamata. Hakika Alkur'ani, a ayoyi masu yawa, ya yabi wannan mace abin koyi, ya kuma kaddamar da ita a mastsayin wata abin koyi ga maza, kamar kuma yadda ya gabatar da ita abin koyi ga mata don su yi koyi da dabi'unta da daidaiton tunaninta da mutuntakarta.
Duk wanda ke karanta tarihin mace cikin da'awar Allah, zai same ta ana magana da ita kamar yadda ake yi da namiji, ba tare da maganar Allah ta nuna wani bambanci tsakaninsu ba saboda kasancewa namiji ko mace.
Ta hanyar nazari tarihin rayuwar mata cikin tafiyar kira zuwa ga Allah, za mu iya fahimtar matsayi na ja-goranci da tasiri da mace ta samu a rayuwar Annabawa da kiraye-kirayensu, da haka kuma kimar mace a cikin al'ummar Musulmi da shigar ta cikin harkokin siyasa, da hakkokinta na mutuntaka da doka, za su bayyana. Za mu ga irin wannan tarayya mai fadi idan muka karanta kissar gwagwarmayar uban Annabawa Ibrahim (a.s.) da mutanensa a Babil da ke kasar Iraki, da fito-na-fitonsa da Namarudu, fito-na-fiton nan da ta kare da tsirar Annabi Ibrahim (a.s.) daga wuta ta hanyar mu'ujizar Allah wadda tafi karfin tunanin hankali na zahiri. kumaal'amarin da ya sa shi (Annabi Ibrahim) yin hijira zuwa garin Sham. Matarsa Saratu wadda ta yi imani da kiransa ta kasance abokiyar jihadinsa.wadda ta kasance tare da shi a lokacin hijirarsa zuwa Sham. daganan zuwa Masar. kuma ya sake dawowa Sham ya zauna a can. inda wani babban zango daga zangogin tarihin dan Adam ya fara a hannun Annabi Ibrahim (a.s.) alhali matarsa Saratu na tare da shi, tana tsaye a gefensa cikin jihadinsa, wahalhalunsa da hijirarsa.
Alkur'ani mai girma na magana game da kissar hijira da rayuwar wannan iyali, kamar yadda yake magana game da gudummawar matar Ibrahim (a.s.) ta biyu, da shigar ta wajen rubuta littafin wannan zango mai haske a tarihin mutum a kasar Hijaz, a garin Makka mai girma wanda ya iso shi yayin da ya baro Masar.
Hakika kissar wannan mata na daga mafi shaharar kissoshin tarihi kuma wadanda suka fi ban mamaki kuma suka fi girman gwagwarmaya da hakuri. domin ta ta'allaka a saman tarihi ta hanyar renon dan Annabi Isma'ila (a.s.) a wani kwari da baya shukuwa a wajen Daki mai alfarma, don ya zama uba ga mafi girman Annabawa a tarihin bil Adama, wannan shi ne Muhammadu (s.a.w.a.); Alkur'ani na bayyana wannan al'amari da cewa:­
"Ya Ubangijinmu, hakika ni na zaunar da wasu daga zuriyyata a wani kwari wanda ba a shuka a cikinsa a wajen DakinKa mai alfarma.."Surar Ibrahim, 14:37.
Haka nan AlKur'ani na magana game da mahaifiyar Annabi Musa (a.s.) da yadda ta karbi fuskantarwar Allah da aka jefa a zuciyarta don ta kare Annabi Musa (a.s.) daga zaluncin Fir'auna, da yadda aka karrama ta ta hanyar dawo mata da shi, inda ta zama mahaifiyar Annabi mai ceto, wanda da taimakon Allah ya wargaza mafi girman dagutu a tarihin dan Adam.Alkur'ani na bayyana ta a matsayin tsaikon asali na faruwar wadannan al'amurra.
Sannan kuma yana magana game da matar Fir'auna Asiya, da Maryam mahaifiyar Annabi Isa (a.s.), yana bijiro da su a matsayin mata madaukaka abin koyi ga zamunan dan Adam, inda ya ce:-­
"Allah Ya buga misali ga wadanda suka ba da gaskiya (na) matar Fir'auna, lokacin da ta ce: `Ya Ubangiji Ka gina min gida a wurinKa a Aljanna, kuma Ka tserar da ni daga Fir'auna da aikinsa, kuma Ka tserar da ni daga mutane azzalumai. (Wani misalin) kuma da Maryamu `yar Imrana wadda ta kiyaye farjinta, sai Muka yi busa a cikinsa daga RuhinMu, ta kuma gaskata ayoyin Ubangijinta da IittattafanSa, ta kuma kasance cikin masu bautar Allah". Surar Tahrim, 66:11-12.
Mu karanta wadannan ayoyi biyu kuma lura da abubuwan da suka kunsa natunane-tunane masu kyau wadanda ke magana a kan matsayin mace da girmamawa da mutuntawa, babu wata wayewa da abin duniya na zahiri
da ta ba ta irin shi. Hakika AlKur'ani, aaikace, ya gabatar da managarciyar mace a kan maza da mata, ya kuma bukace su da yin koyi da ita cikin fadarsa:
"Allah Ya buga misali ga wadanda suka ba da gaskiya" Surar Tahrim, 66:11. domin kalmar: "Allah Ya buga misali" da "ga wadanda suka ba da gaskiya...", kamar yadda yake bayyane, suna nuna wata wayewa ta imani makadaiciya a duniyar tunani, da wata wayewa da ta kebanta ga managarciyar mace; hakika an sanya ta babbar abar koyi ga maza kamar yadda take abin koyi ga mata cikin akida da matsayin siyasa; sai ya bijiro da wasu misalai biyu na daukakar mutuntakar mace Mumina da matsayinta a tunanin Musulunci, sai ya bijiro da matar Fir'auna sarauniyar Masar, matar gidan mulki da siyasa da babbar daula a waccan duniyar, wadda ta kalubalanci babbar daula; da Maryamu 'yar Imrana wadda ta kalubalanci manyan Bani Isra'ila da makirce-makircensu da mummunan yakinsu a kanta.
Kamar yadda mace ta kasance tana da gudummawarta a rayuwar Ibrahim, Musa, Isa (a.s.); haka nan za mu same ta tana da bayyananniyar gudummawa mai girma a rayuwar Annabi Muhammadu (s.a.w.a.) da da'awarsa. Hakika wannan zango na akida makadaici ya shaida Khadija bint Khuwalid Bakuraishiya (r.a.), wadda ta kasance mace mai babban matsayi a cikin al'ummar garin Makka, mai dukiya da kasuwanci da ra'ayi. Ta kasance farkon wadda Annabi (s.a.w.a.) ya fara magana da ita da kiranshi -bayan Ali (a.s.)­kuma ta yi imani da shi ta gaskata shi, ta bayar da dukiyarta
masu yawa don taimakon kiran shi, ta fuskanci nau'o'in cutarwa da wahalhalu tare da shi na tsawon shekaru goma daga rayuwarta; ta shiga shigifar nan tare da shi, ta jure wahalhalun takunkumin nan da ya ci gaba har na tsawon shekaru uku, sai ta zama cikin mutane mafi girma a tarihin Musulunci; don haka ne ma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kira shekarar da ta rasu a ciki da shekarar bakin ciki. Musulmi na matukar girmama wannan mata, kuma suna koyi da halayensa da irin wadancan matsayai na ta masu girma.
A wata muhawara da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi da matarsa A'isha (r.a.), a wani martani da ya mayar ga wata maganarta, ya ce:­
"Wallahi Allah bai sauya min ita da wadda ta fi ta ba, ta kasance uwar iyali, mai tarbiyyar gida, ta yi imani da ni lokacin da mutane suka karyata ni, ta taimaka min da dukiyarta lokacin da mutane suka hana ni, kuma an azurta ni da `ya'ya ta hanyarta aka hana ni da wasunta".[12] A wani lokaci ya kasance yana magana game da ita da cewa:­ "Lalle ni ina son mai son ta".[13]
Kuma kamar yadda ya yi magana a kan matsayinta a ranshi da yunkurin da'awarshi da tafiyar sakonshi, haka nan ya yi magana a kan `yarsa Fadimatu al-Zahara (a.s.), inda ya ce:­ "Fadimatu wata tsoka ce daga gare ni, abin da ke cutar da ita yana cutar da ni. [14]
Haka an taba tambayarsa cewa: Ya manzon Allah, wa ya fi soyuwa gare ka cikin iyalinka? sai ya ce: "Fadimatu 'yar Muhammadu. [15] Daga madannan nassosi za mu fahimci matsayin mace da mutuncinta a rayuwar Annabi (s.a.w.a.) da da'awarsa, kuma wannan matsayi na Annabci yana misalta tunanin Musulunci na mafi girman daga matsayin mace na mutuntaka da girmama ta. Watakila ta hanyar wannan takaitaccen bayani na Alkur'ani da tarihi za mu gane cewa mace a fahimtar AlKur'ani da sakon Allah, ita ce mai renon manyan Annabawa (a.s.), wadda ke dawainyar kare su da lura da su da tsayuwa a gefensu; wannan na bayyana karara a rayuwar Annabi Ibrahim, Musa, Isma'il, Isa da Muhammadu (Amincin Allah ya tabbata gare su baki daya), manyan Annabawa da Manzanni (a.s.), jagororin tunani, kawo gyara da wayarwa a doron kasa.



Hakika AlKur'ani ya zana mana gudummawar mace a rayuwar Annabi (s.a.w.a.) da kiransa, da shigar ta cikin hijira da jihadi, kafada kafada da gudummawar namiji, a lokacin da yake magana game da hijira, mubaya'a, mika wilaya, cancantar lada da babban matsayi, alakar namiji da mace da wasun su, a cikin daruruwan ayoyi na bayanai da maganganunsa a kan wadannan al'amurra, kamar fadarSa Madaukaki:­
"Muminai maza da muminai mata kuwa, masoya juna ne; suna umurni da aikata alheri kuma suna hani da daga mummunan aiki..."Surar Taubati, 9:71.
"Ya Ubangiji, Ka gafarta min ni da mahaifana da kuma wadanda suka shigo gidana suna masu imani, da kuma (sauran) Muminai maza da mata, kuma ka da Ka kari kafirai da komai face halaka". Surar Nuhu, 71:28. "Ranar da za ka ga Muminai maza da muminai mata haskensu na tafiya a tsakaninsu.." Surar Hadidi, 5'l:l?.
A wadannan ayoyi AIKur'ani ya daga mace zuwa mafi girman matsayi da mutun zai iya kai wa a duniya da lahira, shi yana mu'amala da ita da dan'uwanta namiji daidai wa daida; ita da namiji a fahimtar sakon Musulunci masoya juna ne da soyayya ta akida, suna aikin gyara al'umma, da yaki da barna, laifuka da lalacewa, suna daukar sakon alheri da zaman lafiya da gina fcasa.
A aya ta biyu Annabi Nuhu (a.s.) ya fuskanci Ubangijinsa da addu'a ga Muminai mata kamar yadda ya fuskance Shi da addu'a ga Muminai maza; daga abin da wannan ganawa (da Ubangiji) ta kunsa; asasan karimci, kauna da girmama mace na fitowa, wannan kuwa saboda yin addu'a ga wani dauke da dukkan wadannan ma'anoni.
Matsayin mace na kara haske da tartsatsi mai tsarki a shafukan Alkur'ani ta hanyar surantawarsa ga Muminai maza da Muminai mata a wani sarari na haske, ranar haduwa da Ubangiji, sa'ar cancantar sakamakon da ayyana makomar mutum ta hanyar ayyukansa da tafiyarsa a rayuwa.
Haka muke fahimtar cewa AlKur'ani ya ba managarciyar mace kauna da soyayya, ya kuma yi mata addu'a da gafara, afuwa da rahama; ya kuma kewaye ta da sarari na haske; misalinta ita ce Asiya matar Fir'auna, Maryamu mahaifiyar AlMasihu, Khadija matar Manzon Allah (s.a.w.a.) da Fadimatu 'yar Muhammadu (s.a.w.a.). Za mu riski girman mace a sakon Musulunci da rayuwar Manzon Allah (s.a.w.a.) ta hanyar da ta daukaka mutuntakarta, ya yabe ta da girmamawa; idan muka san cewa farkon wanda ya yi shahada a Musulunci ita ce Sumayya, mahaifiyar babban Sahabin nan Ammar bin Yasir, jagoran shirka Abu Sufyan ne ya kashe ta. Hakika ta bayar da rayuwarta ga asasan sakon Musulunci, a lokacin da fito-na-fito ya fara tsakanin 'yan ta'adda da dagutai (a wani bangare), da Muahammadu (s.a.w.a.) da wadanda aka raunana da bayi, wadanda suka sami sakon Musulunci mai kwato hakkin dan Adam, mai 'yanto mutane daga jahilci da danniyar mutum ga dan'uwansa mutum (a daya bangaren).
Haka nan da yawa daga matan da aka raunana sun yi gaggawa wajen gaskata Annabi (s.a.w.a.) a farkon kiransa, sun jure cutarwa, azabtarwa da wahalhalu. sun yi hijira zuwa Habasha da zuwa Madina, sun taimaki Allah da ManzonSa (s.a.w.a.) da duk karfin da suke da shi. Mutuntakar managarciyar mace za ta kara kyautata lokacin da muka shiga sararin nan da ke cike da Shahidai ta hanyar surantawar AIkur'ani da labarinsa da ya bayar da cewa:­
"Kuma kasa ta haskaka da hasken Ubangijinta, aka kuma ajiye takardu (na ayyuka), kuma aka zo da Annabawa da Shahidai, aka yi hukunci a tsakaninsu da gaskiya, alhali su ba za a zalunce su ba". Surar Zumari, 39:69.
Lalle mace Musulma ba ta gano matsayinta na hakika a Musulunci ba tukuna, haka nan namiji Musulmi bai san matsayin mace a Musulunci a bisa hakikanin shi ba tukuna; don haka ma'aunin mu'amala da alaka suka gurbace, irin wanda ba ya tabbata sai an dawo zuwa ka'idojin Alkur'ani don kowane daga cikinsu ya san hakkinsa da matsayinsa da nauyin da ya hau kansa a kan dayan, da alakarsa da shi. Macen da ke haniniya a bayan hohon nan na wayewar abin duniya na zahiri wanda babu abin da ke bayansa face mafada da wulakanci ga mace.da ta san abin da ke cikin Musulunci na kima da hakki, da ba ta kira komai ba in ba Musulunci ba. kuma da ta san cewa abin da zai ceto karamarta da hakkinta su ne ka'idojin Alkur'ani.
Tanadin Mace Don Cika Aikinta
Shiri da tarbiyya na da tasiri mai karfi wajen gini da hada mutum da aikinsa a cikin al'umma, da fuskantar da iyawarsa da kokarinsa zuwa mafuskanta ta gini mai kyau. A halin yin watsi da mutum da hana shi tarbiyya da fuskantarwa, da tanaji mai tsari kuwa, zai sa ya tashi sakakke, wanda yanayi da fare-fare ke galaba a kan shi, irin wad'anda a galibi suke musabbabin lalacewar mutum da tafiyar kokari da kwarewarsa da yi wa ci gaban zamantakewa tangarda; daga nan sai mutum ya zama mai rauni sukurkutacce, baya iya mu'amala da al'umma da fare-fare da matsaloli da damammaki da mu'amala mai nasara.
Surar nan ta misali a Musulunci wadda ya wajaba ta yi nazarin yanayin mace ta hanyar ta, ita ce surar mace a cikin AIKur'ani da sunna, wadda kuma ke tsaye a kan asasai masu yawa kamar haka:­
1-Kadaitar Nau'in dan Adam: Wadda ta ginu a kan asasin fadar Allah Madaukaki:­ "Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, wanda Ya halicce ku daga rai guda daya (Adamu), Ya kuma halittar masa mata (Hauwa'u) daga gare shi, Ya kuma baza maza da mata masu yawa daga gare su. Ku ji tsoron Allah Wanda kuke tambayar (taimakon junanku) da Shi, kuma (ku ji tsoron hakkokin) zumunta. Hakika Allah Ya kasance Mai kiwo ne a gare ku". Surar Nisa'i, 4:1.
Muna iya fahimtar cewa girman wannan aya ba kawai daga abin da ta kunsa na manyan ma'anoni ba ne, a'a har ma daga bude Surar Nisa'i, wadda ke magana game da sha'anonin mata, da wannan aya; wadda kuma take cikin manyan surori, da d'aukar wannan aya a mastayin asasi da mabubbugar tunani da shar'ancin Musulunci wadanda suka tsara alaka tsakanin namiji da mace, suka kuma iyakance matsayinta da gudummawarta a cikin al'umma.
2-Asasi na biyu da ya wajaba a yi nazarin shi a bisa asasin alaka tsakanin namiji da mace shi ne alakar so, kauna, tausayi, tabbaci da natsuwar zuci, wad'anda suka misaltu a fadar Allah Madaukaki:­
"Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lalle cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu 30:21. 3- Daidaitawa cikin hakkoki da wajibai:­
"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.." Surar Bakara, 2:228.
Wannan yana nufin cewa kowane daya daga namiji da mace akwai hakki na wajibi da ya hau kanshi kuma ya zama wajibi ya aiwatar da abin da ya hau kanshi game da dayan da kyautatawa da zamantakewa mai kyau. Da wannan Musulunci ya auna kuma ya tsara a sasan alaka da wannan ka'ida ta shari'a da halayya makadaiciya, sai ya tabbatar da mafi daukakar ka'ida ga hakkin mace.
4-Amma alakar zamantakewa tsakanin namiji da mace, ita ce alakar kauna kamar yadda AIKur'ni mai girma ya fada: "Muminai maza da muminai mata kuwa, masoya juna ne.."
Alkur'ani na bayar da wannan kyakkyawar sura ta alakar namiji da mace a al'umma da cewa ita ce alakar kauna, wadda ta hada mafi girman so da girmamawa, kalmar (?????) da ayar ta yi amfani da ita da larabci, tana nufin: mai taimako, masoyi da aboki,da wannan za mu fahimci kimar managarciyar mace, da ita da namiji daidai ne a wannan bayani na Alkur'ani.
Wani abu na zamantakewa da za a iya ganin shi a duniyarmu ta yau wadda ta kaskantar da kai ga mulkin mallaka, danniya da fin karfin dagutai, shi ne bayyanar danniya, fin karfi da mamaya, tasirin wadannan ya bayyana a cikin mu'amalar zamantakewa da tarbiyya a makarantu da gidaje da alakokin ayyuka da tsare-tsaren zamantakewa ta surori dabam-dabam.
Fakuwar 'yanci, kaskanta mutuntakar wasu da yi musu danniya da rashin mutunta bukatunsu, duk wasu abubuwa ne da ake raye tare da su a cikin duniyarmu ta yanzu; ba a yunkurin hamayya da rashin amincewa sai aiyakokin da ba su dace da wadancan halayya ba.
Abin da ya sami mace a karkashin fitinun wadancan halaye ya fi tsananin kan abin da ya sami namiji, domin hakika kasashenmu sun gaji ci baya na al'adu da tunane-tunane na kauyanci wadanda ta hanyarsu aka yi mu'amala da mace da wulakanci ga mutuntakarta, iyawarta da `yan Adamtakarta; kai! a wasu yanayoyi masu yawa namiji ya yi mu'amala da ita a matsayin wata halitta da ba ta kai matsayin mutum namiji ba, sai wasu tunane-tunane, wadanda suka kawar da mace daga rayuwar zamantakewa na ci gaba, suka taso a tsakanin wasu kauyawa wadanda ke fuskantar fakuwar wayewa da rashin fahimtar Musulunci daga cikin Musulmi, wannan kuwa wani sakamako ne na dabi'a ga yanayin tunani, siyasa da zamantakewar da suka yadu. Sai dai abin mamaki shi ne yadda wasu marubuta da masu kira zuwa ga tunane-tunanen abin duniya na zahiri, ke dangana wa Musulunci, wadannan tunane-tunane da abubuwan da mace ke dandanawa na tauye hakki da ture ta daga fagen zamantakewa.
A karkashin yaduwar yanayin jahilci da ci baya ne Musulumi suka kaskantar da kai ga yakin nan na tunanin abin duniya na zahiri da ya fito daga tafarkokin nan biyu na jahiliyyar gabashi da yammaci; ya zama daga manyan abubuwan da wannan yaki ya sa a gaba, akwai yakar tunane-tunanen Musulunci da mayar da hankali a kan yanayin mace a duniyar Musulmi; sai cibiyoyin al'adu da kafafan watsa labarai da ba na Musulumi ba da jam'iyyun da ba su yi imani da addini ba da masu kira zuwa ga abubuwan zahiri na duniya da kawo sauyi, duk suka himmatu wajen janye mace daga wannan yanayi da take raye a ciki a kasashen da suka ci baya, suka jefa ta a tsaikon sakewa da zubar da kimar mace da yin kasuwanci da al'amarinta na siyasa da wayewa; bayan ta bayyana gare su cewa lalata mace ta hanyar jima'i karkashin ikirarin 'yancin mace da hakkokin mace shi ne kawai hanyar lalata bangaren matasa maza da mata; wannan kuwa saboda mace ita ce tushen rudarwa da tayar da sha'awar jima'i. Hakan yada tunanin sakin akalar jima'i da suka kirkirarwa suna da hakkokin jima'i, yana daga mafi hadarin hanyoyin rushe iyali, watsa 'ya'ya da wargaza alakokin mutuntaka masu karfi da ke tsakanin namiji da mace. Haka shirin tarbiyya da tanajin mace ke fuskantar fuskoki uku kamar haka:­
1-Fuskar da yanayin kauyanci da al'adun da suka ci baya suka haifar da su:itace fuskar da ta ginu a kan asasan wulakanta mutuntakar mace, murkushe iyawarta da boye gudummawarta na zamantakewa da mutunka da ke kafada-da-kafada da na namiji. Wannan itace fuskar da aka gada daga al'adun da suka samo asali daga jahiltar Musulunci, yanayoyin danniya, fin karfin namiji da ci baya na tunani.
2- Fuskar abin duniya na zahiri: Wadda wayewar duniyanci na yammaci ke kira zuwa gare ta. Wannan itace fuskar da ke kira zuwa ga sakin akalar jima’i, abin da ke haifar da wargajewar iyali da mamayar danniya da zalunci a kan mace amma ta wata hanya a karkashin yekuwar hakkokin mace da hakkokin jima'i da wasun wadannan, wanda ya sanya mace ta zama kan-mai-uwa-da-wabin fyade da cutukan zinace-zinace.
3-Fuskar Musulunci: Ita ce fuskar da ta yi imani da kadaicin nau'in dan Adam, ya kuma tsara alaka tsakanin namiji da mace a kan asasan girmamawa da taimakon juna wajen gina al'umma; da tsara alakar jima'i ba a kan asasin halattar jikin mace da jin dadi da shi (haka nan) ba, ko rushe asasan alakokin iyali, kamar yadda yake faruwa a halin yanzu a kasashen Turai, Amirka, Rasha, Sin, Japan da sauransu na daga kasashen da suka tasirantu da wayewar abin duniya na zahiri ba.maimakon haka, a kan asasin girmama mutuntakar mace da ba ta hakkokinta a matsayinta na mutum da ke da abubuwan da suka kebance ta da hakkoki da abubuwan da hakikaninta suka ginu a kai.
Gina Al'umma Ta Hanyar Alakokin Iyali
Ta bayyana gare mu cewa al'umma na tsayuwa ne a kan asasai uku kamar haka:­
1-Tasiri tsakanin halayyar nan ta mace da namiji da siffofin da kowannensu ke da shi na jiki da rai, da cewa jin dadin al'umma da amincinsa na rai da bunkasar zamantakewa da bukatun rayuwa da fadadar hanyoyin shiga da daidaiton halayyar su, duk suna da alaka mai nisa ta hanyar daidaitaccen tasirin da ake musaya tsakanin jinsosin biyu, wato jinsin namiji da jinsin mace.
2- Alakar tunani da wayewa da suka hadu a kai.
3- musayar amfanoni tsakanin daidaikun al'umma mazansu da matansu.
A kan asasai na daya da na uku ne ayyukan zamantakewa ga kowane daya daga daidaikun al'umma mazansu da matansu ya samo asali, kowanne da yadda ya dace da karfinsa na jiki da hankali da kuma inda ransa ya fi karkata.
Daga nan ne mace ke motsawa don tarayya cikin aikin gina gida da al'umma, kuma mafi fadin fagagen wannan tarayya shi ne fagen iyali.
Hakika sakamakon darussan kan halayyar dan Adam sun isa zuwa ga abin da Alkur'ani mai girma ya bayyana, na cewa iyali shi ne ginshikin ginin al'umma, kuma tushe da asasi daga muhimman asasan da ake gina rayuwar al'umma a kan su; don haka AIkur'ani ya bayyana haka, ya kuma sanya ka'idojin alakar auratayya, ya bayyana hakkokin da wajiban da ke kan kowane daya daga namij da mace, don su iya aiki da gina rayuwar zamantakewa mai lafiya.
"Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lallai cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu, 30:21. "Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai daya (wato Annabi Adamu), Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita.." Surar A'arafi, 7:189.
"Maza sama suke da mata saboda abin da Allah Ya fifita sashensu (da shi) a kan sashi, da kuma abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu. Sannan mata na gari masu biyayya ne (kuma) masu kiyaye asirin abin da ke boye wanda Allah Ya kiyaye..." Surar Nisa'i, 4:34.
"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.." Surar Bakara, 2:228. "..Kuma ku zauna da su da kyautatawa.." Surar Nisa'i, 4:19.
"Kuma ma'abucin yalwa ya ciyar daga yalwarsa.." Surar Dalaki, 65:7. "Kuma ku taimaki juna da aikin alheri da tsoron Allah, kuma kar ku taimaki juna a kan yin sabo da ta'adda.." Surar Ma'ida, 5:2.
Haka nan kamar yadda AIkur'ani mai girma ya yimagana game da asasai da alakokin `yan Adamtaka da doka a iyali, haka nan ma hadisan Annabi suka yi magana a kan haka, za mu ambaci abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.):­
"Dukkan ku masu kiwo ne kuma wadanda za a tambaya a kan kiwonsu; sarki da ke saman mutane mai kiwo ne kuma abin tambaya a kan abin da yake kiwo, namiji mai kiwo ne a kan iyalinsa kuma shi abin tambaya ne a kansu; mace mai kiwo ce a kan gidan mijinta da `ya'yanshi kuma ita abar tambaya ce a kansu, bawa mai kiwo ne a kan dukiyar ubangidansa kuma shi abin tambaya ne a kan shi. Ku saurara, dukkan ku masu kiwo ne, kuma kowannenku abin tambaya ne a kan abin da yake kiwo."[16]
Da abin da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) cewa:­"Daga cikin dabi'un Annabawa akwai son mata".
Da abin da aka ruwaito daga gare shi (a.s.) cewa:­"Bana tsammanin mutum na kara alheri a kan imani har sai ya kara so ga mata.[17]
Yana da kyau a nan mu yi ishara da cewa ginin da mace ke yi a cikin al'umma a wasu lokuta ya kan zama aiki ne kai tsaye, a wasu kuma ya kan zama ta hanyar alakarta ta rai da halayya da miji da `ya'ya. Matar da ke samarda yanayin hutawa da kyakkyawan zamantakewa da miji, take kuma tabbatar da kauna, soyayya da kwanciyar hankali, kamar yadda ya kamata a alakokin da ke tsakaninsu, to irin wadannan yanayoyi na rai suna tasiri ga miji da alakarsa ta zamantakewa da wasu, da ikonsa na neman abinci da bayarwa. wannankuwa saboda yanayin rai ga mutum yana tasiri a daukacin harkokinsa da alakokinsa da wasu.
Amma lokacin da rayuwar aure ta cika da matsaloli da damuwa da tashe-tashen hankula, to wannan yana tasiri mara kyau ga miji, aikinsa, neman abinci da alakokinsa da wasu. Kamar yadda yanayoyin rai a cikin iyali ke tasiri ga miji, haka yake tasiri ga `ya'ya; domin yaron da ya tashi cikin yanayin kiyayya, rikice-rikce, matsaloli da mummunan mu'amala, da wuya ya zama daidaitaccen mutum cikin halayyarsa da alakokinsa da wasu, da fuskantar da iyawarsa ta tunani da jiki; domin so tari yaro, saboda yanayin mummunar tarbiyya, yakan sauya ya zama karkataccen mutum mai adawa, ko malalaci da ba ya amfanin komai, ko birkitacce mai kawo matsaloli da aikata laifuka. Alhali kyakkyawar tarbiyya na taimakawa wajen samar da mikakken mutum, ta yadda irin wannan tarbiyya ke tasiri a rayuwar gobe ta yaro ta ilimi, zamantakewa da tattalin arziki.
Don haka gudummawar mace ke da tasiri wajen ginin zamantakewa ta hanyar tarbiyya da tanajin ingantattun mutane ga al'umma; haka nan ta hanyar samar da yanayi mai kayu ga miji.
A cikin wadannan nassosi Akur'ani mai girma da hadisai masu tsarki sun iyakance asasai da ka'idoji na dokokin, halayya, tarbiyya, tsari da gudanar da iyali; a kan wannan hanya kuma mace na taimakawa wajen ginin al'umma. Ginin al'umma kuwa ya ginu a kan asasai kamar.Soyayya da kauna da jin kai da girmamawa tsakanin ma'aurata.
b-Mace na da hakkoki kamar yadda wajibobi suka hau kanta.
c-Maza ke rike da nauyin shugabanci da daukar dawainiyar gudanar da al'amurran gida.
d-Taimakekeniya cikin sha'anonin rayuwar aure.
e-Yin tsaka-tsaki wajen ciyarwa da kiyaye tattalin iyali. f-Kula da nauyi, wato kulawar miji da nauyin da ya hau kansa game da matarsa da sauran wadanda ke cikin iyali; da kulawar mata da nauyin da ya hau kanta game da mijinta, `ya'yanta da iyalin ta. Domin a kanta nauyin kulawa da gida da `ya'ya, tarayya wajen ba su ingantacciyar tarbiyya da yin mu'amala da su da kauna da tausayi da kulawa.
Mace Da Tattalin Arzikin Iyali
Daga cikin manyan matsalolin da suka addabi al'umma,akwai matsalar kudi da hanyoyin shiga ga mutane; da aunawa tsakanin abin da ke shigowa da wanda ake kashewa; hakan na faruwa a tattalin iyali da zarafinshi na kudi wajen ciyarwa da hada-hadar gida. Barnar abinci, abin sha, kayan kwalliya, sutura, mazauni da sauran hidimomi na daga mafi hadarin matsalolin dan Adam; domin akwai almabazzaranci da kashe kudi ba tare da basira ba da ke gurgunta tattalin arzikin iyali, al'umma da gwamnati, wadanda so tari ba sa dacewa da hanyoyin shigar iyali da abin da yake samu.
Saboda tsara ma'aunin tattalin arzikin al'umma ne Musulunci ya yi kira zuwa ga daidaito wajen ciyarwa, ya kuma haramta barna kamar yadda ya yi hani ga, matsolanci, kwauro da rowa.
Daya daga cikin manyan matsaloli wajen ciyarwa ita ce matsalar biyan bukatun iyali da kasafin sa, wadanda mace ke da babban alhakin da ya hau kanta wajen tsara shi da iyakance dabi'arsa.
Hakika shari'ar Musulunci ta sanya gamammun asasai don tsara ciyarwa daga sakewarsa; kamar yadda ta tsara iyakoki na asasi wajen biyan bukatun iyali da kasafinsa a iyakance; daga irin wannan za mu ambaci abin da Allah Ya siffanta "Bayin Mai rahama° da shi a matsayin wani madaukakin abin koyo wajen tsari da lizimci, wanda kuma ya bayyana mikakken tafarkin wajen ciyarwa irin wanda aka yi kira ga mutane su yi riko da shi, Allah Madaukaki Yana cewa:­
"..Kuma wad'anda idan suka ciyar ba sa almubazzaranci kuma ba sa yin kwauro, sai dai ya kasance tsaka-tsaki ne". Surar Furkani, 2s:67.
A wani wuri kuma AIKur'ani na hani da almubazzaranci kuma yana tsanantawa a kan haka da fad'arsa:­
"...kuma ku ci ku sha, amma kuma kada ku yi almubazzaranci, hakika shi Allah ba Ya son masu almubazzaranci". Surar A'arafi, 7:31. Da fadarsa:­
"Kuma ku bai wa makusanci hakkinsa, da miskini da matafiyi; kada ka batar (da dukiya) ta hanyar almubazzaranci. Hakika almubazarai dangin shedanu ne; shedan kuwa mai yawan kafirce wa Ubangijinsa ne". Surar Isra'i, 17:26-27. "Kuma kar ka kunkunce hannuwanka a wuyan ka (wato yin kwauro), kuma kar ka shimfida gaba daya (wato yin almubazzaranci), sai ka wayi gari abin zargi (saboda kwauro), mai nadama (saboda almubazzaranci)". Surar Isra'i, 17:29. "Kuma ku zaunar da su (mata) ainda kuka zauna daidai halinku, kuma kar ku cutar da su (da kwauro) don ku kuntata musu; idan kuwa sun kasance masu ciki ne, sai ku ciyar da su har sai sun sauke abin da ke cikinsu; sannan idan sun shayar muku (da `ya'yanku), sai ku ba su ladaddakinsu, kuma ku daidaita tsakaninku da kyautatawa; idan kuma abin ya gagara daidaitawa, sai wata (matar) ta shayar masa (da jaririn). Ma'abucin yalwa ya ciyar daga yalwarsa, wanda kuwa aka kuntace masa arzikinsa sai ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi, Allah ba Ya dora wa rai face abin da Ya ba ta, da sannu Allah Zai sanya sauki bayan matsi". Surar Dalaki, 65:6-7.
Haka gamammun asasan kasafin iyali da kashewa da ciyarwa ke iyakantuwa cikin tsaikoki biyu na doka, tarbiyya da fuskantarwar halayya; su ne tsaikon zamantakewa da tsaikon iyali.
Kuma gudummawar mace cikin gudanar da tattalin arzikin gida na bayyana wajen kiyayewarta ga kudaden iyali da lurar ta da daidaito wajen kashewa da kayayyakin kyale-kyale da (kiyayewa daga) nuna takama da son a sani wajen kashe kud'i.
Uwa na iya bayar da wani kashi daga mashigar iyali ta ragewa namiji nauyin basussuka ta hanyar rage kashe kud'i da yin tasiri a kan yara, kai! a kan miji ma ta hanyar tsara siyasar ciyarwa madaidaici ga iyali, irin wanda ke daidai da bukatu da gwargwadon abin da ake kashewa.
Yawan kashe kud'i da almubazzaranci a iyali na barin tasirinsa ba kawai a cikin iyali ba, har ma a kan yanayin tattalin arzikin mutane da gwamnati, domin farashin kayayyakin masarufi za su hauhawa a kasuwa saboda hauhawar ciyarwa da kashe kud'i, wad'anda ke haifar da fad'uwar darajar kud'i da tashin kayayyki; da haka sai yawan talauci ya karu, iyalai su rika nutsuwa cikin basussuka da matsalolin zamantakewa; kamar yadda takardun kud'i za su yawaita, sai matsalolin siyasa, tsaro da d'abi'u su kunno kai a sakamakon tabarbarewar yanayin tattalin arziki a cikin al'umma.
Wayar da kan mace da kebance wasu darussa na masamman cikin tsare-tsaren karantarwa game da tattalin arzikin gida a Musulunci, da wayar da kan mace a kan daidaita wa wajen ciyarwa da tsara kasafin iyali, duk suna taimakawa wajen gina yanayin tattalin arziki da ceto shi daga matsaloli, masamman ma matsalar tsadar kayayyaki da rashi ga talakawa.
Da wannan mace na bayar da gudummawa wajen ginin al'umma ta hanyar fuskantarwa da tsarin tattalin arzikin iyali, da daidaitawa wajen ciyarwa ta hanyar bin tsare-tsaren AIKur'ani da kiransa mai hikima. Kuma don mace ta sauke nauyin da ya hau kanta a matsayinta na mai lura da gidan mijinta, kuma wadda za a tambaya a kan shi kamar yadda ya zo cikin bayanin Annabi mai girma (s.a.w.a.).
Yin Aiki a Shari'ar Musulunci
Hakika shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki, ta kuma karakwadaitarwa a kan shi da abin da ba ya bukatar kari a cikin nassosi da karantarwa da matsayi na aikace. Daga cikin su akwai fadar Allah Madaukaki:­
" (Allah) Shi ne Wanda Ya sanya kasa horarriya, saboda haka ku yi tafiya a cikin sassanta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma makoma zuwa gare Shi ne (kawai)". Surar Mulki, 67:15. Haka nan akwai fadarSa Madaukaki:­
"Sannan idan aka idar da Salla, sai ku bazu cikin kasa ku nemi falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa tsammaninku ku rabauta". Surar .Tuma'ati, 62:10
Haka nan akwai fadarSa:­ "Kuma ka nemi gidan lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka, kuma kar ka manta da rabonka na duniya..". Surar Kasasi, 28:77.
Kamar yadda shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki da neman kudi, haka ta yi bayani a kan bambamce-bambamcen karfi da iyawar dan Adam, da wajibcin samun kamala ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaikun nau'in dan Adam; Allah Madaukaki Ya ce:­
"...kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hldima." Surar Zukhrufi, 43:32.
Kamar yadda AIkur'ani ya kwadaitar a kan yin aiki,neman abinci da musayar amfanoni; Manzon Allah (s.a.w.a.) na daukar yin aiki da neman arziki a matsayin jihadi da ibada; hakika haka ya zo cikin abin da aka ruwaito daga gare shi (s.a.w.a.) cewa:­ "Mai wahalar neman kudi don iyali kamar mai jihadi ne a tafarkin Allah".[18]
"Ibada kashi bakwai ce, mafificiyarsu neman halaliya". [19]
Hakika malaman furu'a (fikihu) sun yi kokari mai yawa wajen karance-karance da bin diddigin game da yin aiki da neman abinci, inda suka fitar da hukunce-hukuncen shari'a da matsayinta game da aikin sana'a da hidima, kuma suka kasa su kashi biyar ta fuskar shari'a kamar haka:­
1-Shari'ar Musulunci na daukar yin aiki don samun biyan bukatun rayuwa ga mutum ko ga wanda daukar dawainiyarsa ta zama dole a kan shi, a matsayin wajibi; kai! ta ma wajabta wa wanda ake bi bashi kuma yake da ikon yin aiki da ya yi aiki don biyan bashin da ke kansa.
2-Haka nan Shari'ar Musulunci na daukar yin aiki don yalwatawa cikin ciyarwa, samar da jin dadin rayuwa da ayyukan alheri; a matsayin mustahabbi da take kwadaitar da mutum a kan yin haka.
3-Shari'ar Musulunci ta haramta yin ayyukan da aka haramta, kamar sana'anta giya, miyagun kwayoyi, raye-raye, zina da wasun wadannan; kamar yadda ta haramta duk wani aiki da ke ja-gora zuwa aikata haram, ko da kuwa shi a kashin kanshi halal ne.
4-Shari'ar na daukar wasu ayyuka a matsayin makaruhai a kashin kansu ko saboda wani abu dabam.
5-Koma bayan abubuwan da muka ambata a sama, asalin da shari'ar Musulunci ke tabbatarwa game da aiki shi ne halalci; da haka yin aiki don tara dukiya ko kara yin kudi wani al'amari ne na halal matukar yana gudana a kan hanyar da shari'a ta halalta.
Yayin nazari da bin diddigin ma'anonin ayoyi da nassosi, a cikinsu ba za mu samiabin da ya hana mace yin aiki ba, ko ya kebe halaccin haka ga namiji, duk kuwa da cewa kwadaitar da namiji da magana da shi sun zo cikin wasu nassosi.
Ayyukan Matar Aure: Shari'ar Musulunci ta iyakance wasu hukunce-hukunce da suka kebanci aikin matar aure da abubuwa kamar haka:­
1-Yana daga hakkin mace ta shardanta wa miji cewa ba zai hana ta yin aiki ba a lokacin daura aure.
2-Miji ya amince a kan aikin matarsa ta hanyar fahimtar juna tsakaninsu; wannan idan ta so yin aiki ba tare da wani sharadi da ya gabata ba ke nan. Idan kuwa miji ya ki amincewa da matarsa ta yi aiki a irin wannan hali, wannan ba ya nufin cewa shari'ar Musulunci ta hana mace aiki. maimakon haka wannan na komawa ne ga alakar miji da matarsa.
3-Idan mace ta yi aure alhali ta riga ta yi yarjejeniyar aiki na wani ayyanannen lokaci da wasu. to yarjejeniyar aikin ba ta baci ba, ko da kuwa ya sabawa hakkin miji.
4-Idan matar aure ta kulla yarjejeniyar aiki ba tare da izinin mijinta ba. to ingancin wannan yarjejeniya ya tsayu ne a kan yardar mijin idan aikin na sabawa hakkokin miji. idan kuwa ba ya sabawa hakkokinsa, yana aiwatuwa.
5-Hukuncin macen da ta kulla duk wata yarjejeniyar aiki da mace ta kulla yana gudana.
Ta hanyar nazarin hukunce-hukuncen shari'a ba za mu taba samun wani nassi da yake haramta yin aiki ga mace a matsayin ka'ida ta farko ba; maimakon haka masu haramta aikin mace suna bayar da dalili ne da kasancewarsa a wajen gida; wasu kuwa ba su amince da aikin mace cikin ma'aikatun da ake cakuda maza da mata ba, saboda hakan na haifar da fasadi da fadawa cikin abubuwan da aka haramta; ma'ana haramcin ya zo ne saboda abin da cudanyar maza da mata ke haifarwa a lokacin ayyuka na fadawa cikin abubuwan da aka haramta.
Don haka wannan haramci ne ta la'akari da ka'ida ta biyu ba ka'ida ta farko ba; da wata magana, wannan yana cikin babin haramcin mukaddamar haram da ake kira da "kawar da sabuaba" ko haramta halal din da ke haifar da fadawa cikin abin da aka haramta.
A nan ya kamata mu yi ishara da cewa aikin da ke haifar da aukawa cikin haram, haram ne ga dukkan jinsosin biyu, namiji da mace; don haka matsayin na tilasta hana cudanya, da yin amfani da irin jinsin da aikin ke bukata ba tare da la'akari da kasancewarsa namiji ko mace ba.
Ya bayyana gare mu ta hanyar ayar nan mai girma mai cewa: "...kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima.." cewa bamabancin iyawa, kwarewa da karfin aiki na sabawa daga wani mutum zuwa wani, ba tare da la'akari da kasancewarsa namiji ko mace ba; da cewa musayar amfanoni da biyan bukatun rayuwa da hidima na cika ne tsakanin daidaikun al'umma baiki daya, kuma

kowane daya, ba tare da la'akari da jinsinsa (namiji ko mace) ba, yana yin kokarinsa da abin da zai iya wajen biyan bukatun al'umma, don shi ma ya sami tashi biyan bukatar ta hanyar aikin musayar abin duniya da hidima a cikin al'umma. Manomi na gabatar da kayan noma, injiniya da masanin fanni suna sana'anta na'ura, likita na bayar da lafiya, malami na yin aikinsa na karantar da manyan gobe, dan kasuwa na samar da kayayyakin masarufi a kasuwa, soja na kare kasa, mai gadi na maganin barayi da dai sauransu.
Darasi da nazarin hukunce-hukuncen Musulunci dukkansu, za su tabbatar mana da cewa Musulunci bai haramta wani nau'i na aiki ko ilimi ga mace bayan ya halalta shi ga namiji ba; mace na iya yin kowane irin aiki, kamar noma, sana'a, likitanci, injiniyanci, gudanarwa, ayyukan siyasa, tela, tukin jirgin sama da sauransu.
A musulunci babu wani aiki na samar da wani abu ko hidima da aka halalta ga namiji alhali kuma an haramta shi ga mace; kowa a shari'ar Musulunci daya ne a kan haka; bambancin kawai da ke tsakanin namiji da mace a wasu wajibai ne da aka kallafa wa namiji ko mace ko wasu maslahohi da suka ginu a kan asasan ilimi da aka yi la'akari da yanayin halitta ta rai da ga66ai ga kowannen su, da wajibcin tsara rayuwar zamantakewa da gudanar da ita.
Abin da yake asali a shari'ar Musulunci shi ne halaccin aiki, kai! wajibcin shi ma a wasu halaye; in banda abin da shari'a ta haramta ko abin da ke haifar da fadawa cikin abin da aka haramta.
Idan kuwa har akwai wata hayaniyar haramta aiki ga mace daga wajen wasu, to wannan na bukatar dalili, babu kuwa dalili na shari'a a kan wannan haramci.
Lura na ilimi ga bin diddigin malamai game da wajibai, da kasa su zuwa wajibi na Aini (shi ne irin wajibin da ya hau kan kowane mutum, wani ba ya daukewa wani; kamar sallolin wajibi) da na Kifa'i (shi ne wajibin da ya hau kan mutane a matsayin su na jama'a, idan wasu suka yi shi ya fadi a kan sauran; kamar sallar gawa), za ta bayyana gare mu, ta hanyar nazarin wajibin Kifa'i, cewa tsarin Musulunci ya wajabta wa daidaiku, ba tare da iyakance jinsin mace ko namiji ba, ya wajabta musu samar da bukatun al'umma da duk kashe-kashensu; kamar likitanci, injiniyanci, karantarwa, noma, kasuwanci, sufuri, tsaro da wasunsu na daga ayyukan da al'umma ke bukata; kai! wajibin Kifa'i ma na sauyawa ya zama wajibi Aini a kan mutum ko wasu mutane da ikon aiwatar da wannan wajibi ya kebanta da su; ba kuwa tare da la'akari da jinsin namiji ko mace ba.
Daga wannan za mu fahimci cewa kasa ayyukan hidima cikin al'umma da aiwatar da su, ya ginu ne a bisa asasai biyu: na mutum shi kadai da na tarayya; kuma a cikin dukkan halayen biyu, Musulunci bai bambanta tsakanin namiji da mace ba, maimakon haka, a wasu fagagen wajibcin Kifa'i, kamar wajibcin aikin likita da ya kebanci mata da karantar da su, yana fuskantar da wajibcin ne zuwa ga jinsin mace.
Mace Da Harkokin Siyasa
Daga cikin al'amurra na asasi da aka sanya a teburin tattaunawa da muhawara ta tunani da wayewa a karni na ashirin, akwai al'amarin hakkokin mace, daga ciki kuwa har da shigar ta cikin rayuwar siyasa da harkokin siyasa.
Abin da ke ba da mamaki shi ne cewa wadannan masu kira ga hakkokin mace na siyasa, suna fuskantar da tuhumarsu ga tunanin Musulunci da akidunsa, suna siffanta su da cewa tunane-tunane da akidu ne da suka haramta wa mace shiga cikin rayuwar siyasa, kuma su ke hana ta aiwatar da ayyukan siyasa; suna dogara da abin da suke ikirari da yanayin zamantakewa da siyasa wadanda suke shaidawa a garuruwan Musulmi, ba tare da sun tantance Musulunci a matsayinsa na tsari, shari'a da dokoki; da masu bin Musulunci wadanda ke misalta shi a cikin halayyarsu ta siyasa da zamantakewa ba; da cewa abin da suke shaidawa a kasashen Musulmi ya sabawa yadda ya kamata ya kasance cikin al'ummar Musulmi ba; domin surar mace a wadannan kasashe na Musulmi da hanyar yin mu'amala da ita da kimarta a cikin al'umma, a yanayin da yake na sabawa Musulunci, ya samo asali ne daga wasu tunane-tunane da al'adu da ayyuka na zamantakewa da ba sa misalta Musulunci, masamman ma matsayin mace a fagagen aiki, al'adu, zamantakewa, siyasa da alakarta tare da namiji.
Siyasa a yanayin Musulunci na nufin lura da sha'anonin al'umma a dukkan fagagensu na rayuwa, da ja-gorancin tafiyar da suke yi a hanyar Musulunci; don haka ita (siyasa) wani nauyi ne na zamantakewa baki daya da aka kallafa wa Musulmi baki daya. Wannan nauyi malamai sun kira shi da Wajibi na Kifa'i; wato game da shi ake horo da magana da dukkan Musulmi, ba tare da la'akari da kasancewarsu maza ko mata ba, in banda wanda aka toge (saboda wani dalili) daga cikinsu; misali fad'ar Allah Madaukaki:­ "..Cewa ku tsayar da addini kuma kada ku rarraba". Surar Shura, 42:13.
Da irin fadarSa Madaukaki:­ "Allah kuma Ya yi wa wadanda suka ba da gaskiya daga cikinku suka kuma yi aiki na gari alkawarin lalle ba Zai sanya su masu mayewa a bayan kasa kamar yadda Ya sanya wadanda suka gabace su masu mayewa..." Surar Nuri, 24:55.
Da fadarSa Madaukaki:­ "..ku bi Allah kuma ku bi ManzonSa da kuma majibinta al'amurranku (wato Imamai Ma'asumai).." Surar Nisa'i, 3:59.
Cikin dukkan wadannan ayoyin ana fuskantar da magana ne ga dukkan Musulmi maza da mata; ashe ke nan tsayar da addini da akidunsa da dukkan tsare-tsarensa na siyasa, zamantakewa, ibada da sauransu, nauyi a kan dukkan Musulmi, haka nan horon yin biyayya ga Majibinta al'amurra da ya zo a cikin wannan aya ana fuskantar da shi ne zuwa ga dukkan baligai; haka nan alkawarin mayewa ana fuskantar da shi ne ga dukkan wadanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari maza da mata.
Fadar Allah Madaukaki:­ "Ya kai Annabi idan muminai mata suka zo maka suna mubaya'a gare ka a kan ba za su hada wani da Allah ba, ba za su yi sata ba, ba za su yi zina ba, ba za su kashe `ya'yansu ba, ba za su zo da wata karya wadda za su kage ta da tsakanin hannayensu ko da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba maka cikin abin sarari na shari'a ba; to sai ka yi mubaya'a da su, kuma ka nema musu gafarar Allah, hakika Allah Mai yawan gafara ne Mai jin kai". Surar Mumtahanati, 60:12.
Wani aikatau ne kuma dalili na Alkur'ani da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya aikata shi cikin rayuwarsa ta isar da sako da siyasa, a kan kar6ar bai'ar mace ga Maji6incin AI'amari; kai! wajibcin haka ma, domin mubaya'a a wannan aya ita ce bai'ar biyayya ga Majibincin Al'amari, a kan lizimtar hukunce-hukuncen shari'a da dokokinta, da ikrari da shugabancinsa. Mubaya'a kuwa tana misalta mafi girman ma'anonin hakkokin siyasa a cikin al'ummar dan Adam.
Watakila daga cikin mafi bayyanar dalili a kan gudummawar mace ta siyasa da hakkokinta na siyasa a Musulunci, akwai abin da ya zo cikin ayar `Horo da aikin kirkidahanidamummuna', da ayoyin Wilaya da gamammen shugabanci wadanda suka hada maza da mata.
Hakika babban malamin furu'a nan, gawurataccen manazarcin Musulmi Shahid Sayyid Bakir Sadar (r.a) ya kafa dalili da wannan aya a kan cewa Mumini da Mumina sun cancanci shugabancin siyasa, da cewa namiji da mace a kan wannan daya ne; ya zo cikin nassin abin da ya fada cewa:­
"AI'umma na taka rawarta wajen Khalifanci a tsaikon shari'a, da dalilin ka'idoji biyu na AIKur'ani masu zuwa: 'AI'amurransu shawara ne tsakaninsu' da `Muminai maza da muminai mata kuwa, majibinta al'amarin juna ne; suna umurni da aikata alheri kuma suna hani daga mummunan aiki...' Domin nassi na tarko yana ba al'umma damar aiwatar da al'amurranta ta hanyar shawara ne matukar wani nassi na musamman bai zo da abin da ya sa6a da haka ba. Nassi nabiyu kuwa yana magana ne a kan ji6intar al'amari; da cewa kowane mumini majibincin al'amarin saura ne, saboda dalilin horo da aiki da alheri da hani da mummuna da ya biyo baya. Wannan nassi zahiri ne a kan gudanar wannan jibintar al'amari tsakanin dukkan muminai maza da muminai mata daidai wa daida. Daga nan za a iya fitar da ka'idar shawara da bin ra'ayin mafi yawa a yayin sabani. "[20]
Hakika mace Musulma ta shiga fagen siyasa a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.), kamar yadda ayar Bai'a ta tabbatar da haka; hakika sun shiga fagen siyasa sun kuma yi tarayya a rayuwar siyasa. Haka nan mace Musulma ta shiga kuma ta bayyana ra'ayinta game da Imamancin siyasa da Khalifanci bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a.); mafi girman dalili a kan haka shi ne matsayin Fadimatu `yar Manzon Allah Muhammadu (s.a.w.a.) kuma matar Imam Aliyu dan Abi dalibi (a.s.), wadda ta shiga fagen siyasa bayan rasuwar mahaifinta, ta kasance a gefen Aliyu cikin harkokinta da matsayinta na siyasa; har wasu taro mutane daga Muhajirai da Ansar suka hadu tare da ita; wannan ne ma ya samar da wannan kungiya ta akida da siyasa mai hamayya da bai'ar Sakifa, kuma mai kira zuwa ga sake yin mubaya'a ga Aliyu (a.s.). Hakika ta kasance tana ganawa da Ansar (mutanen Madina) a gidajensu tana neman su da su yi mubaya'a ga Aliyu (a.s.) alhali tana mai hamayya da bai'ar Sakifa.
Ya zo cikin wasu hanyoyin tarihi cewa:­ "Sai Aliyu ya fita yana dauke da Fadimatu 'yar Manzon Allah (s.a.w.a.) a kan dabba da daddare zuwa mazaunan Ansar, tana neman taimakonsu; su kuwa sun kasance suna cewa: Ya 'yar Manzon Allah, hafcika bai'armu ta gudana a kan wannan mutum, da mijinki kuma dan baffanki ya riga zuwa wurinmu kafin Abubakar da ba mu kauce daga gare shi ba".[21]
Haka nan tarihi ya rubuta muhawarori da matsayin siyasa na hamayya da ya gudana tsakanin Fadimatu (a.s.) da Khalifa Abubakar (r.a.) da Umar bin Khaddabi (r.a.). Ta hanyar lura da ayoyin nanbiyu (ayar Shawara da ayar Wilayar Muminai), kamar yadda bayanin fassarar su ya bayyana daga Sayyid Sadar, za mu same su a matsayin asasi na tunani mai fadi kan hakkokin siyasa; kai! wajiban siyasa ga al'umma da dukkan mutanenta maza da mata daidai wa daida.
Wata aya kuma wadda ke wajabta aikin siyasa da wajibcin Kifa'i a kan maza da mata, kamar yin tawaye wa mahukunta masu dagawa, tsayar da daular Musulunci, wayar da kan mutane ta fuskar siyasa da wasun wadannan, ita ce fadar Allah Madaukaki:­
"A sami wasu mutane daga cikinku, suna kira zuwa aikata kyakkyawan aiki da hani da mummuna, wadannan su ne masu babban rabo."
AIKur'ani Mai girma a wannan aya, yana wajabta samun wasu jama'a daga Musulmi da suke kira da kyakkyawan aiki suke kuma hani da mummuna; wadannan jama'a sun hada maza da mata daidai wa daida, da dalilin fadar Allah Madaukaki:­
"Muminai maza da muminai mata kuwa, majibinta al'amarin juna ne; suna umurni da aikata allied kuma suna hani daga mummunan aiki, wad'annan su ne masu babban rabo." Surar Taubati, 9:71.
Bayyanannen abu ne a tunanin Musulunci cewa fagen siyasa shi ne fage mai fadi da ya hada horo da aikin kirki da hani da mummunan aiki, wadanda suka kunshi kira zuwa tsayar da tsarin Musulunci, kalubalantar azzaluman shugabanni da karakatattun tsare-tsare na zalunci, kamar yadda suka kunshi shiga cikin gudanar da shugabanci, tsarin siyasar al'umma, wayar da kan mutane a fagen siyasa, shawara da mubaya'a kamar zaben shugaba da wakilin al'umma, shiga cikin wakilcin al'umma a majalisu da muke kira da 'majalisun wakilai', wadanda ke aikin horo da aikin kirki da hani da mummuna ta fuskar siyasa da sauran irin wadannan.
Ta hanyar nazarin yanayin zamantakewa da siyasa wadanda ya wajaba ayi aiki a tsaikonsu, za mu iya fitar da cewa wannan al'umma (ko mutane) da Alkur'ani ya yi kira da a same su da cewarsa: "A sami wasu mutane daga cikinku.." ba za su iya aiwatar da aikin su a matsayin su na mutane kamar yadda AIKur'ani ke so ba sai sun zama mutane tsararru, wadanda ke gudanar da ayyukansu ta wayayyun hanyoyi wadanda suka dace da yanayi da marhalar tarihi da Musulmi ke raye a ciki.
Wannan na nufin wajibcin shigar mace yadda ya kamata cikin jama'a da ayyukan siyasa, da cikin kungiyoyi, jam'iyyu da mu'assasosin tunani da kawo gyara dabam-dabam, matukar aiwatar da wannan wajibi kamar yadda ake bukata ya ta'azzara ba tare da haka ba.
Daga wadannan asasai na AIKur'ani za mu fahimci cewa rayuwar siyasa a Musulunci a bude take ga mace kamar yadda take bude ga namiji a dukkan matsayinsu -na wajibi Aini da Kifa'i- ko halaccin shiga cikin rayuwar siyasa da dukkan fagagenta.
Kalma Ta Karshe: Karin Bayani
A karshe: mace ba ta da hakki ko karimci sai a Musulunci, wanda ya tabbatar da ka'idojin hakkoki da karama ga daidaikun nau'in dan Adam baki daya da fadarsa:­
"Hakika Mun karrama bani Adama, Muka kuma dauke su a tudu da ruwa, Muka kuma fifita su a kan da yawa daga abubuwan da muka halitta da fifita wa mai yawa."
"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.."
Da fadar Manzon Allah (s.a.w.a.):­ "Daga cikin dabi'un Annabawa akwai son mata".[22] don haka ba abin da ya rage ga mace sai ta nemi hakkokinta kamar yadda AIKur'ani ya tanadar mata, ta kuma lizimci abin da ya wajaba a kanta kamar yadda AIkur'ani ya iyakance mata; a matsayinta na uwa, 'ya, kuma mata; kuma a matsayin ta na mutum da ke da hakkin wilaya da kauna a cikin al'umma; da ke amfani da iyawarsa na tunani, rai da jiki a wuraren alheri, tsarki da kawo gyara. Bayan ta jarabci dacin rayuwa a rudun rayuwar sha'awe-sha'awe munana a duniyar wayewar duniyanci watsattsiya.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

[1] Dabrisi ya I;ida n cikin Majma'al F3avan, a lokncnn da vakc fassara wannan ava, ccwa: "Waun su na mn w:asu hoclim;v"­'Sai dayansu ya amfana da aikin da dayan v_ a vi mishi, d. haka sai tsavuwar duniva ta rama bisa tsari.'
[2] Darihi cikin Tafsirul-Kur'anil-Karim, da Allama Dabadaba'i cikin Tafsir al-Mizan.
[3] Wurarcn da aka ambata a sama.
[4] Ma'ajam al-Wasid.
[5] Inda aka ambata a sama.
[6] Bukhari, littafin Ladubba, babi na 27.
[7] Dokta Anwar Suldan, cikin littafin `Mabadi'ul-Kanuniyya al-Ammah', shafi na16.
[8] Hurrul Amili, cikin Wasa'ilul-Shi'ah, littafin Salla, babin hukunce-hukuncen tufafi, babi na13.
[9] Inda aka ambata a sama.
[10] Bukhari, juz'i na7, shafi na 55.
[11] Dokta Nadim Ada al Yas, cikin littafin `Sayakharul-Ma'i Thummal-Hajar, shafi na 42.
[12] Inda aka ambata a sama.
[13] Inda aka ambata a sama.
[14] Inda aka ambata a sama.
[15] Inda aka ambata a sama.
[16] Littafin da aka ambata a sama, shafi na 15.
[17] Is'aful-Ragibin, wandaaka buga a hamishin Nurul-Absar, na Shabalanji, shafi na 96.
[18] Sahih Muslim, juz'i na1>, shafi na 201, bugun Darul-lhv [19] Sunan al-Tirmiri, da Masnad Ahmad bin Hambali, juz'i na 4, shafi na s; da Khasa'is na Nasa'i, shafi na 25.
[20] Dabari, cikin Dakha'irrul-Ukba, shafi na 37.
[21] Bukhari, juz'i na3, shafi na 196.
[22] Al-Kulaini, cikin Furu'ul-Kafi, juz'i na 5, shafi na 320, bugu na 3.