TARIHIN SAYYID ZAKZAKY {H}

                                                                 
Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
                                                         
Rana da wajen da aka haifi Sheikh:
An haifi Sheikh ne a ranar 5 ga watan Mayu shekara ta 1953[15 ga Sha'aban 1372 AH] a garin Zaria dake cikin jihar Kaduna a Tarayyar Nigeria, kuma sunan sa Zakzaky kalma ce dake nufin 'mutumin zazzau'.
Sheikh Ibrahim Zakzaky shine dan Yaqoub shi kuma dan Aliyu shi kuwa dan Tajuddin dan Imam Hussain. Shi Imam Hussain wani bawan Allah ne daya fito daga Mali yazo garin Sokoto a lokacin Mujaddadi Sheikh Usman dan Fodio[RA] ya zauna tare da shi a matsayin almajirin sa, ta haka nema a lokacin da Shehu Usman dan Fodio[RA] ya nada Mallam Musa a matsayin Amir na lardin zazzau sai ya hada shi da Imam Hussain a matsayin mai bashi shawara. Ta haka ne a hankali-a hankali auratayya ta rika shiga tsakanin iayalen su kuma suka zama yan uwan juna ta wannan tun a farkon karni na 19.
Mahaifin Sheikh Ibrahim Zakzaky ya rasu ne tun shekara ta 1972, sai dai mahaifiyar sa har yanzun tana nan raye, Sheikh shine na biyar a wajen mahaifin su.
Karatun sa:
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya fara karatu ne tun yana yaro karami a makarantar koyon karatun Al-kurani mai girma a makarantun Allo na al'ada kamar yadda aka saba tare da surkawa da karatun ilmin addinin musulunci wajen manyan malamai na wancan lokacin har ya zuwa lokacin da ya kai shekaru goma sha shida inda ya fara haduwa da tsarin karatu na zamani a shekara ta 1979 inda ya fara karatu a makarantar horar da malaman Arabiyya dake Zaria. Sannan daga shekara ta 1971-1975 ya shiga makarantar koyon larabci ta Kano watau School for Arabic Studies[SAS] wadda aka gina tun 1934 a matsayin makarantar koyon aikin lauya. sannan kuma daga baya ita ce ta haifar da babbar jami'ar Bayero da aka sani a yanzu. Kusan baki dayan alkalin alkalan jihohin Arewa daga wannan makaranta suka sami horon su. Saboda irin yadda Sheikh Zakzaky yake da ra'ayin fadada ilmin sa kan wasu darussa da ba'a koyarwa a wannan makaranta yasa ya gwama karatun nasa na Grade II da wasu maddoji ba tare da yayi su a baya ba kamar sanin gwamnati [Government] da ilmin tattalin arziki[Economics] inda yayi jarabawar GCE a kansu. Daga bisani Sheikh yayi jarabawa ta gaba[Advanced level GCE] akan wadannan maddojin:Government, Economics,Hausa,da kuma Islamic Studies inda ya sami kyakyawan natija wadda ta bashi damar shiga jami'a kai tsaye a shekara ta 1976 zuwa 1979 inda ya fara karatun digirin farko [B. Sc] akan sanin tattalin arziki [Economics].
Sheikh yayi musharaka cikin kungiyar dalibai ta musulmi inda ya zama fitaccen mamba a cikin makaranta da kuma  matsayin kasa baki daya inda a shekara ta 1978 ya zama babban sakataren kungiyar na kasa sannan kuma yayi zama mataimakin shugaban kungiyar bangaren harkokin kasashen waje a shekara ta 1979. Sheikh Zakzaky yana daya daga cikin wadanda suka jagoranci kare Shari'ah a lokacin da aka yi wani jerin gwano na nuna goyon baya ga Shari'ah a baki dayan kasar.
Sheikh Zakzaky bisa sha'awar da yake da ita na fadada karatun sa ya ci gaba da zuwa wajen malamai da suka hada da Malam Sani Abdulkadir, Malam Isa na Madaka, Malam Sani Na'ibi da kuma Malam Ibarhim Kakaki dukkanin su a birnin Zaria. Haka nan kuma a Kano Sheikh yayi karatu wajen Shawish Abdallah na Sagagi da Malam Nuhu limamin Yola.
Ayyukan sa:
Babban aikin da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya sanya a gaba shine karatu da kuma yada ilmi tun yana matsayin dan makaranta har ya zuwa wannan lokacin. An mayar da koyarwan sa cikin yan littafai a harshen Hausa da Turanci wadanda aka watsa su a ko ina cikin kasar sannan da yawa daga cikin wa'azuzzukan sa a yanzu suna cikin CD na Computer da kaset-kaset na Recorder a ciki da wajen kasar. Dr. Iqbal Siddiqui ya taba siffanta Sheikh a matsayin "Kashin bayan harkar musulunci a Nigeria"  Babban manufar harkar musulunci da Sheikh yakewa jagoranci shine wayar da kan musulmi abin daya doru a kansu a matsayin su na daidaiku da kuma al'umma. 
Yanzun haka harkar musulunci tana da makarantu dake karkashin ta na Primary da kuma gaba da Primary sama da dari uku wadanda suke a garuruwa daban daban dake fadin kasar. Wadannan makarantu an yi musu suna da makarantun Fudiyya. Haka kuma akwai cibiyoyi da da wuraren bincike da dama a manyan garuruwa na kasar karkashin wannan harka. Harkar ta mallaki jaridar da tafi ko wacce a kasar shiga ko ina da harsheen Hausa wadda ake kira Al-mizan. Sheikh ya sami matsala da hukumomi cikin kaki ko fararen kaya wadanda suke ganin cewa irin salon wa'azin nasa yana barazana ga mulkin su. A lokacin General Sani Abacha an kama Sheikh ne da tuhumar yana wa'azin 'babu hukuma sai ta Allah'.
A halin da ake ciki dai yanzun haka harkar musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta cika shekaru 30 tana kira kan komowa karkashin tsari na musulunci.
Tsawon tsarewar da aka yiwa Sheikh:
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya kwashe shekaru tara a tsare a kurkuku daban-daban na kasar, daga shekara ta 1981-1984 an daure shi a kurkukun Enugu sai kuma kurkukun neman bayanai da bincike na jami'an leken asiri na kasa dake Lagos[Intorregation center] a shekara ta 1984-1985 sai kuma Kiri-kiri a shekara ta 1985 kurkukun Port harcout daga 1987-1989 sannan daga 1996-1997 duk dai a can Port Harcout. Sai kuma kurkukun Kaduna a 1987 sannan daga 1997-1998.
Tafiye-Tafiyen sa:
Sheikh Zakzaky yayi tafiya zuwa kasashe kamar su Britaniya, Saudi Arabia, Iran, Lebanon, Afrika ta kudu, Amurka, da Rasha. Dukkanin wadannan tafiye-tafiye yayi sune ta hanyar gayyata don dalilai na addini ko halartan tarurrukan karawa juna ilmi.
Mata da yara:
Sheikh yana da mace daya da kuma yaya tara.