A Ranar
17/5/1417 Magajin Ganuwa ya jagoranci 'yan tauri, da
zauna Gari banza da muggan Makamai suka kai ma
wakilin 'yan uwa na Ganuwa hari da nufin su
hallaka shi. amma cikin ikon Allah ba su sameshi
ba. amma sun sami saran wani dan uwa mai suna Adamu
Abdussalam da hauya a kafada. haka kuma sun faske wani
yaro m ai suna Maharazu Abdussalam a keya. tare da buge
Liman Malam Sayudi, tsoho dan kimanin Shekaru 65. A
waccan Waki'a an cabke 'yan uwa kimanin 20. ciki har da
masu shekaru 60-70. ciki har da Mahaifin Wakilin 'yan
uwa na Garin Alh. Iliyasu Ganuwa. Sa'annan ya sa
aka danne wasu 'yan uwa da karfin tsiya aka aske musu
kai da Gemu. ya kuma hana duk wata harka ta
Gwagwarmayar Musulunci a Garin. haka kuma ya gayyato
'yan Sanda suka cika Gari har da Dazuka, suna neman
'yan uwa.ya kuma hana Wazifar da aka dade ana yi
Shekaru da dama.
Shi ma bagargajiyen Bakori ta Jihar Katsina, wato
Hakimi Sule Idris ya bada tasa Gudummawar a waccan
lokaci. domin a Tsakankanin ranakun 27- 29/ Jumada
thani na Shekarar 1417 ya sa aka kamo wakilin 'yan uwa
na wancan lokacin Malam Usman. Suka yi masa Mummunar
duka, wanda hakan ya sanya ko ji da Kunnen sa baya iya
yi.laifinsa shi ne ya ce zagin Manzo [S] da kayi a
Kafancan, da kama Sayyid Zakzaky [H] zalunci ne.kuma
dole a saki Malam [H].
Tun da ma wannan Hakimi ya yi kaurin suna wajen dukan
masu Wa'azi tun yana tsiga. kuma shi ne ya
haddasa rikicin da ya faru a Kurami, da unguwar
na-bukka, da kakumi. wadda a wancan lokacin ya yi
sanadiyyar kama 'yan uwa kimanin 21. ciki har da
Liman Ali u/nabukka.da wani babban Malami na Kurami mai
suna Malam Umar. shi ma bamu manta dashi ba. kuma
matukar ba ya tuba ba ne watan watarana sai ya
amsa tambayoyi.
Tarihin wannan harka ba zai taba mantawa da Garin Bargi
ta Jihar Kano ba.da irin Ta'addancin da akayi a
Garin.domin a Ranar 26/10/96 ne wasu gungun 'yan tauri
karkashin Jagorancin wani dan tauri Alh. Na-dabo suka
shirya wani harin Ta'addanci don gamawa da 'yan uwa na
Garin.
Sun yi Nasarar Shahadantar da dan uwa Shahid Malam
Abubakar a kan hanyarsa ta zuwa Markaz.inda suka auka
masa da duka, da sara. wanda a sanadiyyar haka washe
gari ya yi Shahada. haka kuma sun yi kokarin halaka
wasu zababbun 'yan uwa kamar haka Wakilin 'yan uwa na
Garin Malam Yahaya. sai Sa'idu galadima. sai Sa'idu
namadi. da kuma Malam Ado.
Cikin Jagororin da suka shirya wannan Ta'addanci har da
Lawal mai gora. Hafizu. da Malo. wannan duk ya faru ne
a lokacin Janar Abaca.
Na tuna Ranar 29/10/96 Ranar da 'yan sanda suka dira a
Masallacin Tudun-wada Kaduna. inda Shaik Dahiru Usman
Bauci ke gabatar da Tafsiri. suka shiga antaya Tiyagas
a daidai lokacin da 'yan uwa ke gabatar da
Ta'alim. bayan 'yan uwa sun fita sai suka shiga
Masallacin, suka kwashe lasfikokin 'yan uwa guda biyu,
amfilfaya, da kuma Rediyo. da lasifikar Masallaci. da
Darduma. da Agogon bango.da Gadajen wani Dillalin Gadaje
da ke wajan. da Injin Oyal din wani mai sai da Injin
Oyal a wajan.suka loda a wata babbar Mota mai lamba
kamar haka KN 71 K. kuma sun tafi da Malam Bashir
Sufi.da Malam Habibu Kakuri. wannan duk ya faru ne a
lokacin Mulkin Abaca, da Hamid Ali.
Ba ni mantawa da wani kamu na babu gaira bab dalili da
'yan sanda suka rinka yi a Garin Kaduna a watan Jimada
Thani 1417. a wannan rana da misali karfe 12 na dare
suka kai hari Markaz, suka kama 'yan uwa 6. daga cikin
su akwai Malam Ibrahim Mujahid. da Malam Haruna.
da Malam Yakubu. da Malam Yahaya Alaramma. bayan sun yi
musu mummunan duka.
Daga baya sun kama Malam Umar dan-ja bayan gama Fri
Khuduba.haka kuma a badikko sun kama wasu 'yan izala
biyu haka siddan bayan sun yi farautar 'yan uwa basu
samesu ba. sun je gidan Malam Ibrahim Yaro suka
yiwa Matansa dukan tsiya. daya ma sai da ta kwanta a
Asibiti. suka kuma kwashe masa 15,000. sun je
wani Gida suna neman Malam Aliyyu bakin ruwa, shi ma
basu sameshi ba.sai suka sace masa riga, da kudi 20,000
da wani ya bashi ajiya.
Sun dira a Unguwar Sanusi cikin dare.inda suka kama
'yan uwa 8. cikinsu har da Malam Kabiru Usman. da wasu
Mata biyu su ne Malama Amina Mujahid. da kuma Hadiza.
Na tuna tsohon Kantomar Mulkin Soja na Katsina na
wancan lokaci Samuel Bitrus Chama. wanda ya dira akan
'yan uwa, da kamu, Duka, da Tsarewa a Kurkuku. Akwai
wani Malam Sabo da ke cikin Katsina. Jami'an tsaro sun
je Gidansa da misalin Karfe 3:00 na dare. suka kama
shi. a Garin Huntuwa ma kamun ya tsananta a wancan Lokaci.
cikin wadanda suka kama har da Malam Bashir Imam. da
Abdurrashid. da kuma Malam Gambo mai kunun
Bara'a.
Sa'annan kuma a wata Juma'a Mataimakin kwamishinan 'Yan
sanda Akilu Bakori ya jagoranci 'Yan sanda sun kai wani
hari. inda suka kama ;yan uwa kimanin 30 a wancan
lokaci 1417. inda bayan bugunsu da akayi aka sako su.
Haka kuma a wata Juma'a 'yan sanda sun kaiwa 'yan uwa
na Dabai hari, sun bi gida-gida suna kama su.haka ma a
Garin Danja sun kai hari. inda suka kama Mutane da
yawa.sa'annan a Gora da ke Karamar Hukumar Manumfashi
'yan sanda cikin farin kaya sun yi awon gaba da Dan
uwan da ke tunatarwa a Garin. Duk wannan ya faru ne a
lokacin Mulkin Chama, da Abaca. kuma bamu yafe ba.
Shi ma Kantomar Mulkin Soja na Jihar Zamfara na wancan
Lokacin Jibrin Bala Yakubu ya shiga sahun yi wa 'yan
uwa Ta'addanci. inda a Ranar 4/11/1996 'yan Sanda suka
dira a Talatar Mafara, suka Cabke 'Yan uwa kimanin 15.
cikin 'yan uwan da suka kama a harin da suka kai da
rana tsaka har da Wakilin 'yan uwa na bakin Kasuwa
Malam Musa Umar.
Duk da wannan Bala'in Jarabawa da 'yan uwa na Kurkuku
suke ciki a ko ina a Kasarnan a wancan lokaci, sun
aikowa da 'yan uwa na waje sako. inda suke kiransu da
kada su sassauta.
'Yan uwa daga Garuruwan Malumfashi. Funtuwa. Bakori.
Mai ruwa. Layin Na-bukka. Daura. Jibya. Mashi. da
sauran su. sun aiko da sakon cewa ko daidai da rana
daya kada a sake a sassauta.
Haka su ma 'yan uwa da ke Kurkukun Garuruwan
Kadunada Zariya sun aikowa 'yan uwa na waje da kada su
kuskura su sassauta ko daidai da rana daya.
A ranar 4/11/1996 wakilin 'yan uwa na Garin Jibya Malam
Iliya Musa ya kai kansa ga D P O Bna 'yan sanda.
Tun kafin wannan Rana dai 'yan sandan sun yi ta bin
Gidajen makwantan Malamin suna cin Mutumcin su da sunan
wai suna neman Malamin. a irin haka sun kama 'yan uwa
kimanin 13.
Sun azabtar da wani Malami mai Wa'azin Turmi. domin ya
gayawa masu sauraronsa cewa '' Malam Zakzaky [H]
ne kadai cikakken masoyin Manzon Allah a Kasar nan.
akwai radi-radin cewa 'Yan kungiya ne suka gayyato
akazo aka yi wannan Ta'asar.
Har yanzu ba mu manta da Alh. Salisu Tulu na Unguwar
bawa ba.da irin takurawa 'yan uwa da yayi. shi da
Bagargajiyen Garin mai suna Ibrahim Bature. ba ni
mantawa da Ranar Laraba 3/Rajab/1417. inda inda
ya sanya 'yan banga suka dinga dukan 'y an uwa Malam
Zakariyya, da Malam Aminu hayin gada sai da suka kai
kasa a Masallacin Juma'ar Garin. bayan sun gama dukansu
suka mikasu ga Jami'an tsaro aka wuce da su Saminaka.
\Haka kuma bayan an wuce da su, sai suka jagoranci kame
'yan uwa, ciki har da Tsoffi guda uku. Alh. Musa
Sarkin Tasha. Tsoho ne wanda ya fi Shekaru 80. laifin
sa shi ne yaki ya basu hadin kai. sai Alh. Ya'u Gurasa,
Baban wani Dan'uwa. sai Alh. Dalladi, Baban
Wakilin 'yan uwa na Saminaka.wadanda suka rufa bayan
wannan Ta'addanci su ne Alh. Amadu Zaki. sai
Inuwa Tela. da Alh. Abdulkarim. da Alh. Ummar Baban
Gwanjo.duk wadannan ba mu manta da su ba.sai wadanda
suka tuba, suka daina abinda suke yi.suka kuma nemi
gafara.
Ba mu manta da kamun da Jami'an tsaro suka yiwa Malam
Bawo ba a Ranar Talata 5/11/96 a Markaz na Da'irar
Suleja.haka ma Malam Husaini Barde a Ranar 6/11/96 a
Fudiyyar Suleja. sun kuma je su kama Babangida mai
bidiyo, amma ba su sameshi ba. amma sun kwashe kasoshin
Bidiyon sa. sun kuma yi kokarin kame wakilin 'yan uwa
na wancan lokaci Malam Adam Usman [Allah ya ji kansa]
amma ba su sami nasarar kamashi ba.laifin su shi ne sun
nuna Kaset din Ta'addancin da Hukumomi suka yi a Kofar
Doka Zariya bayan kama Malam [H].
Wadanda suka kitsa waccan Makirci su ne Abdullahi
Bisallah. Ali, Buhari,Nura. da sauran su.A ranar
4/Rajab/1417 ne 'yan sanda suka dira a Giodan Malam
Abubakar Abdullahi da ke Unguwar Dan buwa Sakkwato,
suka kama shi.daga nan suka nufi Markaz suka kama wasu
'yan uwa su 2.suka zarce Gidan Wakilin Malam Malam
Kasimu Umar Sakkwato da nufin su kama shi, amma ba su
sameshi ba. anan ma sun kwashe wasu daga cikin
kayayyakin sa. suka tafi da su. daga baya da ya samu
labari sai yakai kansa Ofishin su.
Kafin wannan Rana 'yan sandan suna tsare da wasu 'yan
uwa 7 da suka kama su. 'Yan uwan kuwa su ne Mall.
Buhari Wurno. Mal. Bello A Bello. Sheik Khalid.
Alh. Namadina. Alh. Mustafa. Tukur Fadaru. da kuma
Dakta Musa. [wani babban likitar kashi a Jami'ar Dan
Fodiyo]. Sidi Munniru.Dahiru Umar. Abubakar Tudun Jukun.
Bello Tela. da Shehu Tambuwel. Dukkansu an tsaresu a
Ofishin 'yan sanda a wancan Lokaci.
A ranar 20/10/1996 'yan sanda ta da tarzoma suka dira a
layin nabukka a Garin Huntuwa ta Jihar Katsina. suka
kuma rusa Makarantar Fudiyyar Garin. a wancan lokaci bincike
ya tabbatar da cewa an yi wannan danyenaikinne bisa
Umurnin Mataimakin Kwamishinan 'yan sandan yanki
Funtuwa Akilu Bakori, yaya za mu manta da wannan?.
Ko-da-kowa ya manta da Magajin Ganuwa Zubairi Ali [LA]
da ke Kuraye a Karamar Hukumar Rimi ni ba zan manta
dashi ba. sabo da sanyawa da yayi aka yiwa 'yan uwa
mata biyu fyade. don haka muna binsa bashi.
Musamman wannan mugun bawa ya tara 'yan tauri, da zauna
gari banza. ya basu izinin su bi Gida-gida, su auikawa
'yan uwa, da Matan su.
An aiwatar da wannan Dabbancin ne bisa jagorancin wani
Dabban dan tauri wai shi Muntari.daga cikin 'yan taurin
da sukayi wannan aiki akwai Jari Gwanki. Barau. Dahiru.
Bello Soket. da sauran wadanda bamu fado sunayensu ba.
Duk da wannan Dabbancin da Tsinannun suka aikata sai da
'yan uwa Mata suka sami karfin Gwiwar fitowa Muzaharar
nuna kin yarda da wannan Dabbanci da aka yi wa 'yan
uwansu. inda suka yi Muzaharar Tafiyar Kilomita biyar.
suka kare Muzaharar a Kofar Dakacin Ganuwa. suka kuma
yi jawabin rufewa kafin su watse.
Bayan kamun Malam [H] dan uwa mai karatu a wancan
lokacinne aka gano Makircin kokarin Kashe Malam [H].
wanda Gwamnatin Abaca ta yi kokarin yiwa Malam Allurar
Guba wacce ba nan take za tayi kisa ba, sai ma bayan
Watanni, ko ma Shekaru. ganowar da 'yan uwa sukayi shi
ya dakatar da wannan mugun nufi nasu.
A Kastina ma haka abin yake. 'Yan sanda sunyi ta zuwa
Gidan Malam Yakubu Katsina da nufin su kama shi, amma
basu taba samunsa ba. sai sukayi alwashin matukar suka
sake zuwa basu sami Malamin ba, to 'yan unguwar su
shirya ganin wulakanci. hakan ya sanya Malamin ya kai
kansa da kansa wajan Jami'an tsaron.
An tuna mani da ranas 6/ Jimadal Ula 1417, lokacin
MulkinAbaca. inda 'yan sanda suka Shahadantar da Mutane
4 a Goronyo, da 'yarrimawa. duk a Jihar Sakkwato.
Wadanda sukayi Shahadar sune Shahid Malam Muhammad mai
Kasuwa, Goronyo. Shahid Malam Ibrahim 'Yarrimawa.
Shahid Malam Umar Takuri, 'yarrimawa. da Shahidiyar
farko a wannan Harka Malama Aliya 'Yarrimawa.
Shi Shahid Malam Muhammad mai Kasuwa Goronyo yadda akayi
ya yi Shahada shi ne Wakilin 'Yan uwa na Garin Goronyo
Malam Aliyyu Adamu Takakume yana cikin yin tunatarwa a
Masallaci kamar yadda aka saba sai ga wani dan saddu
wai shi Abu Yudi [UD] ya nufoshi da wuka tsirara zai
caka masa. sai Shahidin ya shiga tsakanin. ai nan take
Abu UD ya cakawa Dan uwannan wukar a ciki, kuma
nan take ya fadi yayi Shahada.
Su kuwa Shahidan 'Yarrimawa yadda akayi sukayi Shahada
shi ne 'Yan uwa na cikin yin Ta'alim a Masallaci sai ga
'yan sanda sun kawo hari. daga zuwansu sai suka shiga
antayo musu Hayaki mai sa Hawaye. zuwa can sai suka
shiga aiko da Harsasai cikin Masallacin.
Ana cikin haka sai Harsashi ya sami Wakilin 'yan uwa na
Garin, Shahid Malam Ibrahim. sai ya cewa 'yan uwa an
harbeshi. sai dan uwansa na Jini Shahid Malam Umar
Takuri ya kawo masa dauki. ai nan take shi ma suka
harbeshi. a wancan lokaci sai Dattijiya, kuma
Shahidiyar farko a wannan harka, kuma Mahaifiyar
Wakilinj 'Yan uwa Shahid Malam Ibrahim Malama Aliya ta
nufo wajan da abin ke faruwa.ko tausayi babu, haka 'yan
sanda suka bude mata wuta, inda nan take tayi Shahada.
Bayanai sun tabbatar da cewa wani Kansila ne mai
suna Dan tsamaye ne ya gayyato 'yan sandan suka zo suka
yi wannan Ta'addanci.
Tarihin wannan Gwagwarmaya ba zai taba mantawa da Abu
UD. da Dan tsamaye ba.da Babban Jami'in 'yan sandan da
ya bada wancan Mammunan Umurni. in har suna raye sai
sun Fuskanci Hukuncin Laifukan su. ba da kama-karya
kamar yadda sukayi ba.
Na tuna da rusa mana Zawiyya da Gwamnatin
Ala-tsine ta Abaca tayi. 'yan uwa ne, mai taro,
mai Sisi, aka tara kudin da aka gina waccan Zawiyya.
amma a lokaci guda, bayan har gini ya kai linta sai
Gwamnatin Abaca, da na Mugu Dan masara Hamidu Ali [LA]
suka aiko aka rusa mana Zawiyya. to ba mu yafe ba. ba kuma
za mu yafe ba. Lallai Hamidu Ali in kana raye watan
watarana sai ka amsa tambayoyi akan haka.
An tuna mani da Ranar 18/9/1996 lokacin da 'yan uwa
suka taru a Kaduna don yin Muzaharar nuna kin yarda da
Zagin Manzo [S] da wani arne wai shi Monday Yaknot yayi
a Garin Kafancan, da kuma nuna kin yarda da kama Malam
[H]. a wannan Muzahara 'yan sanda sun Hallaka Mutanen
da har yau babu wanda ya san adadin su. kana tsammanin
an Hallaka Mutane nawa?. ka san Lokacin?. kana wajan?.
to har yau babu mahalukin da yasan yawan Adadin Mutanen
da aka Hallaka.wasu su ce 30. wasu 40. wasu 50. kai
gasunan dai.kuma duk a lokacin Hamid Ali [KKK]. da kuma
Abaca.List din 'yan uwa yananan a gare su. na Mutanen
Gari ma yananan a gare su. watan watarana kowa zai zo
ya baje abinda ya sani game da wancan Ta'addanci. ni
kaina shaida ne. na san [KKK] ya Shahadantar da Dan
uwana Shahid Muh'd Sani Sufi. kuma ba zan taba yafewa
ba.
Tarihi ya riga ya rubuta Barden Jema'a Alh. Ya'u
Kafancan. sabo da irin Gudummawar da ya bada a wancan
lokaci. aka rinka bi Gida-gida, da wajajen Sana'o'in
'yan uwa ana kama su.
SAI NA AZABTA 'YAN SHI'A.
Inji Hamid Ali Gwamnan Jihar Kaduna na wancan Lokaci.
ya ci-gaba da cewa ''Zan kuma yi amfani da Matsayin
Kaduna cibiyar Arewa, in sanya Gwamnoni su takurawa
'yan shi'a''. ya ci-gaba da cewa '' A tarihin shiga ta
aikin Soja, tunda na fara, har zuwa yanzu ana turani ne
domin yin bincike. na sha azabtar da masu taurin kai.
kuma in biyar dasu yadda nakeso, ko yadda akeso. babu
wadda ya taba gagara ta tunda na fara. yau gani-ga
'yanm shi'a''. inji Hamid Ali. ya fadi hakane a wani
taro na Jami'an Soji.
Ya ci-gaba da cewa '' Babu abinda nake Shi'awa
irin inga ana bude wuta ga masu taurin kai''. wani
wanda ya san Hamid Ali ya ce Kanar din bai san komaiba
sai Musiba ta Soja kawai. an taba tambayarsa da cewa me
yafi Shi'awa a Rayuwar sa?. sai yace ''Kashe masu
bore, da Azabtar da wadanda ake bincike''. to yau gashi
ana Shi'a. kuma Harkar Musulunci na tafiya.
tana kuma ci-gaba. kuma yana gani, yana kuma raye babu
yadda ya iya. Allah kenan!. wanda kowa ya ja dashi sai
ya fadi kasa warwas.
Na tuna da rusa mana Zawiyya da Gwamnatin Allah tsine
ta Abaca ta yi. Gini ne wanda aka yishi, da
taro-da-sisi 'yan uwa suka hada akayi karo-karo har
Ginin ya kai Linter. amma cikin 'yan Mintuna Gwamnatin
Allah tsine ta Abaca da Hamid Ali KKK suka ruguza shi.
Ko a dokan gine-gine idan an lika maka Notice
Ma'aikatar kula da gine-gine na Jihar Kaduna KASUPDA
sukan bada mako biyu zuwa uku kafin su dauki mataki.
amma a Zawiyya sam ba'a samu haka ba. ana likawa yau
gobe akazo aka Rushe Zawiyya. kana tsammanin za mu
yafe?.
Mai karatu ka tuna da ranar 18/9/1996 lokacin da 'yan
uwa suka taru a Kaduna don yin Muzaharar kin yarda da
kama Sayyid [H], da kuma kin yarda da zagin Manazo
[SAWA] da wani wai shi Monday Yaknot daga Garin
Kafancan yayi?.kana tsammanin an hallaka Mutane
nawa?.ka san lokacin?. kana wajan?. to har yau babu
wanda yasan iyakan Mutanen da aka hallaka a wancan
lokacin. wasu suce 30, wasu 40, wasu 50. kai gasunan dai.
kuma duk a lokacin Hamid Ali ne, da Abaca. List
din 'yan uwa yananan a garesu, na Mutanen Gari ma
yananan a garesu. watan watarana kowa zaizo ya baje
abinda ya sani game da waccan Ta'addanci. ni kaina
shaida ne akan kisan da aka yiwa Dan uwana Shahid Muhammad
Sani Sufi, kuma dan yafe ba.
Tarihi ba zai taba mancewa da Barden Jema'a Alh. Ya'u
Kafancan ba.sabo da irin gudummawar da ya bada a wancan
lokaci. aka rika bi gida-gida da wajajen Sana'o'in 'yan
uwa yana nunasu ana kamasu.
Ana cikin haka sai Azzalumar Hukuma ta sanya aka rushe
Cibiyar Musulunci ta Bekaji dake Jihar Adamawa.
Cibiyar wacce aka ginata tun Shekarar 1979 ta kunshi
Masallaci, Makaranta. Karamin Asibiti. Gidan Liman. da
sauransu. an baje ta cikin 'yan awoyi bayan ta Shekara
17 tana ayyukan taimakawa Musulunci da Musulmin
Kasarnan. Musamman da yake a wancan Lokaci 'yan uwa ne
ke gudanar da ita.
Ba zan taba mantawa da kyakkyawar Jagorancin da
muka samu daga Malam Muhammad Turi ba, wajan tafiyar da
Abubuwa bayan kama Sayyid Zakzaky [H]. Malam Turi ya
nuna Juriya da dakewa da iya Jagoranci cikin Natsuwa
kwarai da gaske.
Ga wata hira da Al-mizan tayi da shi a wancan lokaci.
Danjuma Katsina ne yayi Hirar.
AL-MIZAN:- Allah ya gafarta Malam da yake lokacin da
Jami'an tsaro suka zo sun sameka, kuma da kaine aka
tafi can Kaduna inda ake tsare da Malam. ko za ka iya
yi mana bayanin yadda suka zo, da kuma yadda suka tafi
da Malam, da irin karbar da suka yi masa?.
MALAM TURI:- Bismillahir rahmanir rahiim.Wasallalahu
ala Nabiyyul Kariim.Wa'alihi Addayyibina Addahirin.Wa
ba'ad, Assalamu alaikum.
Da farko dai wannan rana ta Alhamis mun kasace mun yi
Sallar Subahi da Malam.kuma muna zaune a falo har zuwa
wajen Karfe bakwai.sai mukaji wata 'yar hayaniya a
waje. daga karshe ma sai aka yi mana bayanin cewa 'yan
sanda ne sukazo suka kewaye Gidan Malam.ba-ma Gidan
Malam kadai ba, kusan ma ace Unguwar gaba daya an
kewaye ta.
Kuma sai ya zama sun yi Sallama da cewa Malam yana
nan?. A daidai wannan Lokaci na fito na tambaye su cewa
me suke bukata?. na tambayi Jagoran nasu wai shi
Muktar.sai yayi bayanin cewa wai sunzo da takarda ta
Izinin binciken Gidan Malam. wsai na karba na
karanta. a ciki wani Majistre ya sa Hannu ranar
10/9/1996.cewa wannan ''Search Warrant'' ne, wadda aka
basu Izini su binciki Gidan Malam wai ana neman
Makamai.
Sannan ban da wannan akwai wata takarda ta daban
wadda ita kuma an nuna cewa duk wani wanda ake tuhuma
ko suke so to su bincike Gidan nashi. To bayan na yi
magana eda su sai na dawo cikin Falo inda na yiwa Malam
Bayanin ga abinda ke tafe da su.
To shikenan sai Malam yace ana iya shigowa da su.
wsai ya shiga Dakin Kwamfuta, inda na yiwa su
Shuwagabannin nasu magana. suka yi masa bayanin abinda
suka shaida mani a waje.sannan Malam yace wannan abu
sassaukar abu ne suna iya zuwa su bincika.suka fa
bincike daidaikun 'yan uwa, wato kowanne dan uwa ya
fito waje, in an dubashi sai ya koma gefe guda ya
tsaya.har aka bincike duk 'yan uwa.
Sannan kuma kafin su shigo sai sukace mu ma muna da
damar mu bincike su, kafin su shigo su fara bincike.sannan
aka bincike su domin a tabbatar da basu dauke da wani
abu wanda za su dasawa Malam [H]. To shi ne suka
baincike Gidan Malam ga-baki daya. to amma hakarsu bata
cimma ruwa ba. domin suna burin su samu wasu muggan
Makamai da za suyi amfani da su wajen kullawa Mallam
Sharri, to Allah [T] bai biya musu Bukatarsu ba. kuma
baicin haka ma sai da suka hau garu na sassa guda biyu
wadanda suke makwabtaka da Malam wanda babu Gida a
wajen.
Sai muka ji daya daga cikin su ya yanka ihu.da muka ce
masa yaya?. ashe wai daya daga cikinsu ne wanda yake
dauke da bindiga ya hangoshi ta daya bangaren, har zai
daukeshi da harbi, don shi ya dauka dan uwa ne. to ashe
dan uwansa ne. sai ya dakawa dan sanda tsawa yace
yana tare da su, da wani abu mai kama da haka. to sai
dai Allah ya kiyayeshi a lokacin. in ba haka ba da ya
harbeshi a lokacin.
Sannan kuma kamar makwabtan Malam su ma an bincike
Gidajen su, duk dai don neman Makamai. bayan sun gama
sun tambaye ni wai ina nake da zama?. na zo na nuna
musu. suka zo suka yi bincike har kimanin awa uku, duk
sun duba ko ina da ina. sun laluba to amma basu samu
biyan bukata ba.
To bayan haka sai sukace ai umurnin da aka basu shi ne
in sun gama bincike to su tafi da Malam. to shi ne
Malam yace '' To wannan abin naku ai ya zama yaudara,
domin tun farko da kukazo sai kawai kuce kun zo
kamani ne. to amma da kunce kun zo bincike ne na
Makamai. amma bayan an gama baku samu komai ba sai kuce
ance ku tafi da niinje in yi bayani?, to dai abin naku
ya zama yaudara''.
Anan dai aka dan tirza da su.to a likacin ya kasance
'yan uwa sun da fara harzuka. danin yanayin irin abinda
ake ciki sai Malam yace musu to babu damuwa zai
tafi da su.ya shiga cikin Gida ya shirya, ya fito da
jakar sa, sannan ni ma tun lokacin da na ji sun fara
cewa za su tafi da Malam na je Gida na debo wasu
'yan kaya da abin goge baki na dawo.
Lokacin da Malam ya fito tuni 'yan uwa sun riga sun
harzuka, sun nuna damuwarsu kwarai, su kuma Mobayil
hankalin su ya soma tashi. domin Mutane suna ta taruwa,
su kuma 'yan uwa suka yi ta ketowa ko ta ina. su kuma
Mutane sun tsaya suna kallo. Duk dai an yi cirko-cirko,
wuri ya dau zafi. sai Malam ya fito, yayi jawabi akan
cewa wadannan Mutane sun zo su kamashi ne, kuma zai
tafi da su. kuma ya yi kokarin kwantarwa da Mutane
Hankali.kuma abu nakarshe wanda ya fadi shi ne zai tafi
da wadannan Mutane kuma bayaso kowa ya bishi.
To anan ne fa Jama'a suka yi
ta rusa kuka.a da har anyi Alwallah an fara shiga
Sahuza'aje a shiga Motar 'yan sanda, to amma sai
Malam yace a'a, babu wanda zai bishi ya
kuma ce shi ba zai shiga Motarsu ba, a motarsa
zai tafi. ya bani Makulli na fito da Motar sa.ya
shiga tare da mu. a cikin Motar har da kanin
Malam [H] wato Malam Badamasi. wanda Malam ya
gayyace shi domin yaga abinda ake ciki. sannan
kuma akwai Shugaban ''Operation'' din wato A/C
Mukhtar, wanda ya jagoranci su wadannan 'yan
sanda.
A haka dai muka fita daga
Kwarbai, suna ta harba Tiyagas, suna ta kokarin
harzuka Jama'a. A haka mukaje Kofar doka suna ta
harba Tiyagas, sai muka ga sunyi Hanyar
Kaduna. muka kama hanya har zuwa ''Toll
Gate'' na Kaduna. muna shigewa ne sai suka
tsaya. sai shi A/C Mukhtar su fa ba zxa su
iya shiga Kaduna alhali Malam na cikin
Motarsa ba. domin su suna jin tsoron 'yan na iya
kawo musu hari. sabo da haka suka bukaci Malam ya
koma wata Motar ta su. to dai Malam bai wani bata
lokacin gardama da su ba. Da yayi musu bayanin
cewa ai wannan babu wani ab u da zai faru, domin
can ma gun da yake ya baiwa Mutane hakuri
ba kuma abinda ya faru, sai muka koma Motarsu.
inda wani dan sanda ya tuka Motar Malam [H]. ya
shiga da ita Hedkwatar 'yan sanda ta Kaduna. mu
kuma ga-baki dayammu da su Mobayil din sai muka
tafi Hedkwatar Mobayil da ke Unguwar Talabijin.
aka shiga damu ciikin Jiniya, da tsaro mai
tsananin gaske. duk suka tayar da Hankalin Jama'a
kamar yadda suka saba. A haka muka shiga
Hedkwatar Mobayil, sa'annan aka shiga da mu wani
Ofis.wato da ni da Malam, da kuma Malam Badamasi.
Bayan wani da Lokacin sai shio
A/C ya zo yace zayyi magana da Kwamishina, sabo
da haka sai aje wani Ofis na daban ya buga masa
waya, kamar yadda ya gaya mana. ko da yake
hakikatan na ji yana Magana yana cewa ya zo da
su. kaza-kaza. sai daga bisani ya zxo ya gaya
mana cewa akwai mataimakin Sufeto Janar [AIG]
wanda yake shiyyar Kano da wasu Jihohi na kusa,
yana tafe shi da Kwamishina.to amma kafin su zo
akwai bukatar mu bayar da Stetment. kuma
kafin nan zayyi mana bayanin abinda ake tuhumar
mu da shi.
To yayi maganan abin da yua
shafi tara makamai domin yakar Gwamnati, sannan
kuma ta bangaren Malam [H] da Alh. Dallami sun yi
maganar wai buga Al-mizan, da kuma abinda ya
shafi kafa Gidan Rediyo. sannan kuma har wala yau
sun kawo abinda ya shafi Rikicin Kafancan. an
yiwa 'yan uwa da aka kamo a Gidan Alh. Dallami
tambayoyi akan haka, har ma suna bugun cikin 'yan
uwa da cewa kun je kun ta da hargitsi a Kafancan
a 1987 wannan karon ma kun tayar.
Da yake sun kama har da yara
masu kananan Shekaru suka tambaye su wai ina
Makaman da Alh. Dallami ya basu?. bayan mun gama
Stetmen sai A/C ya zo yace wai sun tattauna da
duk Shuwagabannin nasu. akan cewa za su sallami
Mutane, to amma banda Mutane Hudu. wato
Malam [H]. Alh. Dallami. Abubakar Al-mizan
[Marigayi]. da Kuma Shitu. To amma sauran Mutane
ba'a da bukatar a ci-gaba da tsare su. har akwai
wata 'yar uwa ma da suka kama akan wai ta watsa
musu kasa.
Duk abinda ake ni da Badamasi
mun kasance tare da Malam [H] a Ofis daya.da
akazo aka yi wannan bayani sai Malam [H] yace
musu ''Su wadannan sun rakoni ne domin su ji
menene zai faru. sabo da haka akwai bukatar ka yi
takamaiman Jawabi ka ce ga matakin da za'a dauka,
alabashshi sai su koma da bayanin da za suyi
Misalito amma yanzu bakace komai ba. da kace
Kwamishina zai zo, yaushe zai zo?.wannev mataki
za'a dauka dunk bakayi bayani ba. to amma in za
ka yanke magana kace kun kamani akan kuma tuhuma
ta da kaza-kaza, za ku dau mataka kaza-kaza to da
shikenan''. inji Malam [H].
Sai yace A'a, ai shi basu kama Malam [H]
ba. su dai kawai za suyi Bincike ne.tana iya
yuwuwa ma in anjima ma Malam ya koma abinsa. irin
dai wannan yaudara nasu. har nace masa kar ka
mayar da mu yara mana, sau nawakake yi mana
haka?.
Har ma nake bashi Misali nace ni a
1987 sun sameni ne a wani wuri a Kaduna. suka ce
mani kar ma in damu, zan je ne inga Kwamishina n
'yan sanda, kar in damu. to Kwamishinan da ban
ganiba kenan tun wancan lokaci har yanzu. mun dau
dan lokaci mana dan tirzawa da shi har yace to su
fa ko da karfi zai iya rabamu da Malam [H]. sai
Malam yace da mu ba bukatar ayi haka kawai mu
kyaleshi mu tafi. ka ji yadda suka rabamu da
Malam.suka kaimu Hedkwatarsu ta cikin gari.suka
bbani Dan makullin Motar,sannan na dawo Zariya ni
da Malam Badamasi.ko da na dawo sai na taras 'yan
uwa sun yi dandazo.
AL-MIZAN:- Allah ya gafarta
Malam akwai labarin da ke yawo cewa sun yi niyyar
su yi harbi da ace a lokacin 'yan uwa sun gwada
zafiakwai alamar wannan sosai?.
MALAM TURI:- Wannan ko
shakka babu.ko Miskala zarratin ba shakka.sun zo
da niyyar yaki ne. kuma wanna a zahiri yake.
domin daga cikin maganganun su za aga haka.ai
kamar Shugaban Mobayil A. Magaji, din ya
zaga baya inda yake shaida musu cewa
''Wannan A/C zai sa a kasheku kawai domin suna
taruwa ['yan uwa]''. kuma har sun matso da
Tankarsu ta Ruwan zafi.har ma sdun fara gyara
Bindigogin su. to amma babu shakka sun zo da
niyyar harbi. domin an basu damar cewa ko wanne
mataki za su dauka na wajen kama Malam to suna
iya dauka.
Sabo da haka wannan bai wai
labari ne bako abin yayi kama da haka, a
hakikatan haka abin yake.
AL-MIZAN:- Kamar a Takardar da
suka bada wanne Majistre ne ya sa Hannu, ko Malam
ya ga Sunan sa?.
MALAM TURI:- Ai sa Hannun na
Signature ne, ba na Suna ba.don haka ba Sunan sa
sai dai 'Signature' akan gun da aka rubuta
''Majisdtare'' din.
AL-MIZAN :- Takarnar warantin
ta bincike ce ko ta kamu [Arrest]?.
MALAM TURI:- Takardar ta
bincike ce ba ta kamu ba.ai ka ga akwai
yaudara.da ma sun zo da niyyar kamu, to amma
bbasu nuna cewa za suyi kamu ba.kuma lallai basu
nuna wata Takarda ta kamu ba. Illa iyaka an basu
umurnin cewa duk abinda za suyi to su tafi da
Malam, kuma su tabbatar sun gama sun isa Kaduna
karfe Tara [9:00 S].
Domin ko da muka isa
Kaduna na ji suna ce musu kun makara da awa
biyu, akan yadda aka shirya musu shi aikin
[Operation] kenan. to kuma lallai wani gagarumin
shiri neda aka dade ana shirya shi, domin sun
kawo 'yan sanda daga Jihohi daban-daban.haka kuma
na ji suna ambaton wasu Garuruwan Jihohi da aka
kawo 'yan sanda daga can, na kiyaye da biyu,
Minna da Jos.
Wannan shi ne Hiran da
Al-miozan tayi da Malam Mahammad Mahmud Turi a
wancan lokacin.
A tuna mani da 8/11/1996
lokacin da aka aukawa 'yan uwa a Masallacin
Unguwar Gangaren Tudu da ke Garin Keffin Dan
yamusa. 'yanh uwan da aka aukawa a wancabn lokaci,
aka yi musu jina-jina sabo da Imanin su sune
Muhammad Sani, Sulaiman Abubakar,
Rufa'i Kasim, Yusuf Isa, Ibrahim
MujahidAbdussalam, Mukhtar Shaibani, Malam
Sulaiman, Muhammad Lawal, da Magaji Abdullahi.
Wadanda suka kitsa wannan
danyen aiki su ne Mallam Ahmad Sarki.Mah'd
Dasabo.Malam mai Hannu Daya. Bala Dalladi.Adamu
Kafinta.Nasiru Habibu. Abul Jalil, bisa
Jagorancin Sanusi Hadisi.
Daga cikin Samarin da suka ba
Hadisi hadin kai don cin zarafin 'yan uwa sun
hada da Jibrin Gambo.Jibril Sabo. Tanko Dalladi.Maimako
yaron Mama.Yahaya. Yakubu Mamman.Abubakar
Kafinta. Malam kana tsammanin za mu manta da
wadannan?.
A cikin Watan Rajab na
Shekarar 1417 ne 'yan uwa mata na Garin Dandume
da ke cikin Karamar Hukumar Funtuwa cikin
Jihar Katsina suka yi wata gagarumar Muzahara.
sun yi wannan Muzaharar ne sabo da murnar fitowar
'yan uwansu Mata daga Kurkukun Funtuwa.wanda
Galadiman Dandume ya sa aka kama su sabo dea
neman sanin inda Mazajen su suke.
Kwamandan 'yan Sanda na yanki
Akilu Garba Bakori shi ma ya taka Muhimmiyar
rawa, shi da wasu Dagatan yankin wajen tursasawa
'yan uwa. inda har takai ga in kana tsama da wani
Mutum sai ka je wajen Kwamandan yankin ka yiwa
Mutum Kazafin shi dan Shi'a ne.wanda da kyar zai
kwaci kansa da makudan kudade don ya tsira.
An yi wani Bagargajiye a
wancan lokaci a Garin Makuwana, cikin Karamar
Hukumar Sabon Birnin Gobir ta Jihar Sakkwato,
maqi Suna Ibrahim mai Kudi. wanda ya rantse da
Allah sai ya hallaka duk Dan uwa da ya sake yin
Wa'azin a koma ga Allah [T], kuma sai ya ganawa
Mahaifin Dan uwan Azaba.
Musamman Bagargajiyen ya kafa
wani Kwamiti da ya sanya ya yi masa List din
Iyayen 'yan uwa su 78. ban manta da
'yan kwamitin ba Haruna Hedimasta. Sule dan Kolo.
Dadi Kangala.tare da wani Dan Izala mai suna Dan
aya.
|
|
|
|