Wednesday, 22 August 2012


[S4I5]Daga:www.harkarmusulunci.org
Fassarar hudubar sallar Idi na jagora Ayatullah Sayyid Ali Khamana'i

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Ina gode masa da neman taimakonsa da neman gafararsa da kuma dogaro da shi. Ina salati da sallama ga Abin kaunarsa kuma zababbensa cikin halittunsa, mai kare masa sirrinsa kuma mai isar da sakonsa, mai bishara ga .............................

Shimfida: Abin da ke biye fassarar hudubobin sallar idin karamar salla ta bana (1433 hjiriyya) da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi ne bayan ya jagoranci sallar idin a ranar lahadi 19, Augustan, 2012 wadda ta yi daidai da 1 ga watan Shawwal shekarar 1433 Hijiriyya:

Hudubar Farko:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Ina gode masa da neman taimakonsa da neman gafararsa da kuma dogaro da shi. Ina salati da sallama ga Abin kaunarsa kuma zababbensa cikin halittunsa, mai kare masa sirrinsa kuma mai isar da sakonsa, mai bishara ga rahamarsa sannan kuma mai gargadi da azabarsa, shugabanmu kuma annabinmu Abul Kasim al-Mustafa Muhammad tare da Alayensa tsarkaka kuma zababbu masu shiryar da shiryayyu musamman ma Wanzajjen Allah a bayan kasa. Tsira da aminci su tabbata ga Imaman musulmi da masu shiryar da raunana sannan masu kare muminai.
Ina kiran dukkanin ‘yan'uwa maza da mata masu girma zuwa ga tsoron Allah; sannan kuma ina isar da sakon taya murnar wannan idi na karamar salla, wacce rana ce ta rahama da gafara, rana ce ta ba da lada ga muminai da wadanda suka aikata ayyuka na kwarai saboda Allah kuma a tafarkin Allah sannan kuma suka yi abubuwan da za su kusata zukatansu zuwa ga Allah Mai rahama da gafara. Ina gode wa Allah da ya sake ba mu damar ganin wani watan na Ramalana da kuma wani idin na karamar salla, lalle wajibi ne mu girmama wannan ni'ima ta Ubangiji.
Alhamdu lillahi watan Ramalanan wannan shekarar, kamar yadda mutum yake ji a cikin labarai sannan kuma yake gani a nan da can, watan Ramalana ne mai cike da albarkoki. An kusata zukata zuwa ga Allah, zuwa ga hakika da ababen da suke kusata mutane ga Allah, bangarori daban-daban na mutane sun halarci tarurruka na addini da karatun Alkur'ani haka nan a darare masu albarka na Lailatun Kadari, mutane sun gudanar da wadannan darare cikin tawassuli da Allah da addu'oi inda suka sama wa kasar nan wani yanayi na kusaci da Allah sannan kuma mai tasiri cikin kasar nan. Wajibi ne a amfana da wannan yanayin sannan kuma a gode wa Allah Madaukakin Sarki.
Haka nan kuma a wani bangaren na daban cikin lamuran da suka shafi duniyar musulmi da al'ummar musulmi, mutane sun yunkura yunkuri mai kyau, wannan yunkuri kuwa shi ne yunkurin da suka yi a Ranar Kudus, sun girmama wannan abin da marigayi Imam Khumaini ya bari, sun nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da ake zalunta da kuma batu na asasi na duniyar musulmi. Sun fito kwansu da kwarkwatansu cikin wannan yanayi na zafin rana sannan kuma cikin kishirwar azumin watan Ramalana, lalle wannan abin godiya ne. Lalle muna gode wa dukkanin al'ummar Iran sakamakon wannan gagarumin yunkuri da ya dace kuma a daidai lokacin da ya dace da suka yi, wanda ko shakka babu zai yi gagarumin tasiri a duniyar musulmi; insha Allahu.
A wannan shekarar ma sauran al'ummomi sun biyo sahun al'ummar Iran sama da na shekarun da suka gabata a wannan fagen. A wasu kasashen ma da sakamakon ikon gwamnatocin dagutu a ke hana gudanar da irin wadannan zanga-zangogi (na Ranar Kudus) da hana mutane bayyanar da goyon bayansu ga batun Palastinu, amma alhamdu lillahi a wannan shekarar mutanen wadannan kasashen sun shigo fage; wannan wani lamari ne da insha Allahu zai ci gaba da wanzuwa. Wajibi ne mu roki Allah Madaukakin Sarki da ya karbi ibadun wannan al'umma masu girma a wannan watan da kuma samun kulawarsa ta musamman; kamar yadda ya zo cikin addu'ar da ke cikin Sahifar al-Sajjadiya inda ake cewa: "Ya mai karbar karamar kyauta sannan kuma mai gode wa dan karamin aikin da aka yi saboda shi....Ya mai kusatar duk wani wanda ya kusace shi, Ya mai kiran mutumin da ya juya masa baya zuwa gare shi" (Addu'a ta 46) wannan addu'a ce da Imam Sajjad (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake yi a irin wannan ranar - ranar idin karamar salla - sannan kuma yake kiran mutane da su dinga yi.
Idan kun yi wani aiki da zai kusata ku da Allah, lalle Allah Madaukakin Sarki zai kusato ku. Haka nan kuma mutanen da suka juya wa hakika da koyarwa ta Ubangiji da addinin Allah baya, to Allah Madaukakin Sarki cikin rahama da tausayinsa zai kiraye su, wannan wata tausayawa da rahama ce ta Ubangiji. Ina kiran matasanmu masu girma da su kiyaye irin wannan haske da suka samu a wannan watan, insha Allah; su kiyaye wannan ajiya da suka samu tsawon rayuwarsu ko kuma alal akalla saboda wannan shekara guda mai zuwa wato har zuwa ga ranar idi na gaba, zuwa ga watan Ramalana na gaba. Ku kiyaye irin wannan nuna kewa da Alkur'ani, komawa ga Allah, zikiri, kasantuwa a fagagen da Allah Madaukakin Sarki ya ke son bayinsa su kasance a wajen da kuka yi - shin fagagen da suke da alaka da shi kansa mutum ne ko kuma wadanda suke da alaka da duniyar musulmi da al'ummar musulmi - kuma Allah Madaukakin Sarki zai albarkace su.
Ya Ubangiji Allah! Ka saukar da rahama da albarkokinka ga wannan al'umma (ta Iran) da kuma dukkanin al'ummar musulmi. Ya Ubangiji Allah! Ka ba wannan al'umma haka nan da al'ummar musulmi nasara a kan makiyansu. Ya Ubangiji Allah! Ka kara irin wannan alaka ta ruhi da zuciya da mutane suke da ita da ababe masu kusata mutum da Ubangiji a kowace rana.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
Ka ce, Shi ne Allah Makadaici. Allah Wanda ake nufinsa da bukata. Bai Haifa ba, kuma ba a haife shi ba. Kuma babu daya da ya kasance tamka a gare shi" (Suratul Ikhlas 112:1-4)

Huduba Ta Biyu:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu kuma annabinmu Muhammad tare da Alayensa tsarkaka. (Ya Ubangiji Allah) ka yi sallati ga Aliyu Amirul Muminin da Siddikatul Tahira Shugabar matan duniya da Hasan da Husaini jikokin rahama sannan kuma imaman shiriya tare da Aliyu bn Husain da Muhammad bn Ali da Ja'afar bn Muhammad da Musa bn Ja'afar da Aliyu bn Musa da Muhammad bn Ali da Aliyu bn Muhammad da Hasan bn Ali da al-Ka'im al-Mahdi amincinka ya tabbata a gare su gaba daya. Ka yi sallati ga Imaman musulmi da masu kare raunana da kuma shiryar da muminai. Ina muku wasicci da tsoron Allah.
Ina kiran dukkanin ‘yan'uwa maza da mata masallata da suka taru a wannan taro mai girma zuwa ga tsoron Allah da kuma nesantar zunubai. Abin da nake son fadi a wannan hudubar: wasu batutuwa ne guda biyu wadanda suke da alaka da kasar mu da al'ummarmu sai kuma wanda yake da alaka da duniyar musulmi. Dangane da abin da ya shafe mu, a matakin farko shi ne lamari mai sosa rai din nan na girgizar kasar da ta shafi wasu daga cikin ‘yan kasar mu masu girma. Abin da ya faru a wani yanki na kasar nan da ya cutar da wasu daga cikin mutane, wani lamari ne da ya shafi dukknain mutanen kasar nan ba wai kawai wadancan mutanen da abin ya ritsa da su, su kadai ba. Lalle na sani kuma ina ji a jikina sannan kuma abubuwan da suka faru a baya suna tabbatar da hakan cewa babu yadda al'ummarmu za su nuna halin ko in kula kan wani bala'i da ya fada wa wani bangaren na kasar nan. To alhamdu lillahi a wannan lamarin ma mutane sun shigo cikin fage, kuma wajibi ne a ci gaba da yin hakan. Lamarin dai wani lamari ne mai sosa rai; ya yi barna ainun, wasu ma sun rasa rayukansu wanda jami'an gwamnati sun fadi yawan adadin mutanen da suka rasa rayukan na su. Abin da ke wuyan jami'an gwamnati da kuma sauran daidaikun al'umma shi ne su yi aiki da nauyin da ke wuyansu.
Alhamdu lillahi an gudanar da ayyuka masu kyau; a lokacin da mutum ya kalli lamarin daga kurkusa, a lokacin da mutum ya tambayi mutanen da abin ya ritsa da su; lalle zai iya fahimtar cewa an gudanar da ayyuka masu kyau; to amma fa aikin yana bukatar a ci gaba da yinsa. Nauyin da ke wuyan dai, wani nauyi ne mai girma; muna fatan insha Allahu jami'an gwamnati za su yi kokari wajen kawar da damuwar da mutane suke ciki sakamakon wannan bala'in. Baya ga haka kuma su yi kokari wajen mayar da hakan ta zamanto wata hanyar da mutanen wannan yankin za su bude wani sabon shafi mai kyau cikin rayuwarsu, haka nan kuma insha Allahu a kokarin sake gina wadannan garuruwa da za a yi ta hanyar himmar jami'ai da kuma hadin kan mutane, za a sami damar insha Allahu a kawar da bakin cikin da ya kunno kai a wannan yankin.
Wani lamarin kuma na daban shi ne batun Ranar Kudus. Ranar Kudus dai, wato wannan yunkuri wanda marigayi Imam (Khumaini) mai girma ya faro shi, sannan kuma cikin yardar Allah a kowace rana yana dada karuwa da bunkasa, wani yunkuri ne mai girma da ke cike da ma'ana. Lamarin ba shi ne kawai wannan zanga-zangar ba, wani sabon jini ne da a cikin ranakun nan aka sanya shi cikin jijiyoyin al'ummar musulmi. Duk kuwa da kokarin da wasu suke yi na sanyawa a mance da wannan batu na Palastinu da al'ummar Palastinu, amma alhamdu lillahi a kowace rana sai dada bunkasa lamarin ya ke yi; kuma haka lamarin zai ci gaba da tafiya. Akwai wani gagarumin nauyi a wuyan jami'an kasashen musulmi, wanda muke fatan Allah Madaukakin Sarki zai shiryar da kuma taimakawa kowa da kowa wajen sauke wannan gagarumin nauyi da ke wuya.
Tabbas batutuwan da ke faruwa a duniyar musulmi a wannan lokaci, wani lamari ne maras tamka. Irin wadannan sauye-sauye da ke faruwa a duniyar musulmi, sauyi ne mai ban mamaki da kuma ayyana makomar yunkuin al'ummar musulmi a nan gaba. Muna fatan insha Allahu kamar yadda ya zuwa yanzu al'ummomin wannan yankin suka sami damar aiwatar da manyan ayyuka haka nan ma jami'ai suka aiwatar da abubuwan da suka kamata, wannan yanayi zai ci gaba sannan kuma makiya al'ummar musulmi wadanda a kowace rana suke kara kaimi cikin irin makirce-makircensu sannan kuma suka shigo fage da dukkan karfinsu ba za su sami nasarar yin galaba a kan wannan himma ta al'ummar musulmin ba; wanda tabbas ne cewa ba za su sami nasarar ba. Lalle an bude wani sabon shafi, an samar da wani sabon yanayi a duniyar musulmi wanda kuma wannan yanayi a sannu a hankali zai yi tasiri a kan dukkanin al'ummomin duniya.
Mu yi kokari wajen ganin cewa ba mu yi kuskure ba cikin sharhin da za mu yi da kuma fahimtar lamurran da suke faruwa. Mu san cewa Amurka da yahudawan sahyoniya makiya al'ummar musulmi ne; shugabannin gwamnatocin girman kai na duniya, makiya al'ummar musulmi ne. A duk lokacin da muka gansu sun koma wani bangare, mu san cewa wannan bangaren na bata ne, bangare ne da ke cike da kuskure; a saboda haka kada mu yi kuskuren fahimta. Ba su taba damuwa da al'ummar musulmi ba, duk wani abin da za su iya yi wajen bata al'ummar musulmi za su yi. A yau din nan dukkanin wadannan rikici da tada jijiyoyin wuya da suka haifar, duk kuwa da cewa a wasu lokuta wasu gafalallun mutane ma suna sake nanata irin wadannan maganganu; irin sabani na mazhaba da kabilanci da launin fata da yare da ke faruwa, su suka haifar da su da kuma kambama su; alhali kuwa babu dukkanin wadannan abubuwan a Musulunci "Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (shi ne) wanda ya fi ku tsoron Allah" (Suratul Hujurat 49:13) dukkanin al'umma daya suke, dukkaninku ‘yan'uwa ne. Wajibi ne dukkanin mu farka, mu zamanto masu basira, mu bude idanuwanmu, kada mu fada tarkon kuskuren sharhi.
Ya Ubangiji Allah! Albarkacin Annabi Muhammadu da Alayen Muhammadu, ka sanya wannan yunkuri mai girma na al'ummar musulmi ya zamanto mai alheri da albarka da kuma sa'ada a gare su. Ka kaskantar da makiyan al'ummar musulmi.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
Ina rantsuwa da zamani. Lalle ne mutum yana a cikin hasara. Face wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri. (Suratul Asr 103:1-3)
Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.
Shafin Jagora

No comments:

Post a Comment