Wednesday, 22 August 2012


  [S4i5] Daga:www.harkarmusunci.org

Mutum ko dai dan uwan ka a addini ne, ko kuma tsaran ka a halitta

Wata kungiyar matasa ta musulmi da mabiya addinin kirista masu son ganin an zauna lafiya watau CMPIN a takaice sun kawowa jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaquob El-Zakzaky wata ziyara ta ban girma hade da taya murnar sallah karama a yau lahadi 1 ga watan..........

Shawwal a gidan sa dake unguwar Gyallesu cikin birnin Zaria.
Ita dai wannan kungiya ta Christian Muslim Youth Peace Initiative Of Nigeria watau CMPIN a takaice, aikin ta shine kokarin ganin sun wayar da kan al'ummar Nigeria game da muhimmancin zaman tare da kuma fahimtar juna da nufin kawo karshen tashin tashina da aka haddasa a tsakanin su.
Tun da farko dai daya daga cikin mambobin wannan kungiya Muhammad Garba wanda kuma yake cikin kungiyar yan jaridu ta kasa watau NUJ ya gabatar da mahalarta wannan ziyara da kuma matsayin su a cikin ta.
Sannan daga bisani sai Mr Diji O. Haruna shugaban matasa na kungiyar kiristocin Nigeria [CAN] ya gabatar da nashi jawabin inda ya nuna makasudin zuwan su wannan ziyarar, da kuma yiwa Malam barka da sallah karama.
Bayan ya kammala jawabin nasa sai ya mika abin magana ga Muhammad Garba wanda shi kuma ya gabatar da manyan baki musamman Pastor Osin Titus wanda Sheikh Zakzaky ya mika masa shimfidar sa ya zauna kusa da shi a gefen sa na dama.
A lokacin da yake gabatar da jawabin sa a lokacin ziyarar Sheikh Zakzaky ya fara ne da taya al'umma murnar sallah karama, sannan ya tabo muhimman abubuwa da ya kamata a lura da su wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a kasa.
Daga ciki ya kawo wani fadi na limamin farko na gidan Manzon Allah[SAWA] watau Imam Ali[AS] inda yake bayyana cewa: "Shi mutum imma dan uwan ka ne a addini ko kuma tsaran ka a halitta".
Watau ta ko wacce fuska shi mutum yana da alfarma da ya wajaba a kiyaye. In dan uwanka ne a addini watau kuna addini iri daya to wajibi ka rike shi a matsayin dan uwan ka na addinin musulunci, kuma yana da girma da mutunci da wajibi ka kiyaye, haka nan kuma in ma ba addinin ku daya ba, watau shi ba musulmi bane, shima yana da hakki na zama dan uwan ka a halitta watau shi mutum ne kamar kai kuma yana da karamci da dole ne ka kiyaye.
Sheikh Zakzaky yaci gaba da nuna cewa in har mutane zasu gane wannan sannan kuma su kiyaye ta yaya za'a sami tashin hankali a tsakanin su?
Malam ya bayyana cewa hatta sakataren majalisar dinkin duniya na baya Mr Kofi Annan wannan magana ta Imam Ali[AS] ta burge shi har sai da yayi umurni a rubuta ta a ofishin na Majalisar Dinkin Duniya.
Bayan kammala wannan ziyara dai tawagar ta matasan na CMPIN sun mika kyauta ta musaman wadda Pastor Osin Titus ya mika ga Sheikh Zakzaky a madadin su don nuna jin dadin su a kan wannan dama da suka samu.
Haka nan kuma an dauki hotuna na gaba daya sannan Malam yayi ban kwana da baki suka kama hanya.
Duka sun bayyana jin dadin su da yadda Malam ya karrama su a lokacin ziyarar.

No comments:

Post a Comment