Sunday, 15 January 2012

Imam Ali Ridha (a.s) da shahadar sa.



Imam Ali Ridha (a.s}
 
Imami Na Takwas: Imam Ali Ridha dan Musa Al-Kazim (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: Ali dan Musa dan Ja'afar dan Muhammad. Mahaifiyarsa:
Kuyanga ce mai suna Najma. Alkunyarsa: Abul Hasan, Abu Ali. Laqabinsa:
Arrida, Assabir, Arradiyyu, Alwafi, Alfadil. Tarihin haihuwarsa: 11
Zul-ka'ada 148H. Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: kuyanga ce mai suna: Sakina, an ce sunanta Al-hizran, da Ummu Habib

'yar Al-mamun. 'Ya'yansa: 1-Muhammd Al-jawad 2-Al-kani'u 3-Ja'afar 4-Ibrahim

5-Al-Hasan ko Al-Husaini 6-A'isha.
Tambarin zobensa: Masha'Allah la Kuwwata illa bil-Lahi. Tsawon rayuwarsa:
shekara 55. Tsawon Imamancinsa: Shekara 20. Sarakunan zamaninsa: Abu Ja'afar
r
Al-mansur da Muhammad Al-Mahadi da Musa Al-Hadi da Harunar-Rashid da Al-amin

da Al-ma'amun dukkaninsu sarakunan Abbasiyawa ne.
Tarihin shahadarsa: qarshen Safar 203H. Inda ya yi shahada: Garin duss a
Khurasan. Sababin shahadarsa: Shan guba a lokacin halifa Al-ma'amun. Inda
aka binne shi: A Al'karyar San'abad a duss Khurasan. A yau wurin yana cikin
birnin Mash'had.
Shi ne Imam Ali Ridha dan Musa (A.S) kuma babarsa ita ce Najma, an haife shi

a ranar alhamis a goma sha xaya ga zulqi'ida, shekara ta xari da arba'in da
takwas a Madina, kuma ya yi shahada da guba a ranar juma'a qarshen watan
safar shekara ta xari biyu da uku, kuma xansa Imam Jawad (A.S) shi ne ya
shirya janazarsa, kuma ya binne shi a Khurasan inda kabarinsa yake yanzu.
Ya kasance mafi ilimi da fifiko da baiwa da kyawawan halaye da qasqan da kai

da ibada.
Ma'amun ya kira shi daga Madina zuwa Khurasan kuma ya sanya shi halifan
musulmi, sai dai Imam mai zuhudun duniya (A.S) bai karva ba, saboda ya san
makirci da yaudara da take cikin hakan, kamar yadda kakansa Imam Ali (A.S)
bai karva ba a yayin da xan Auf ya bijiro masa da sharaxin tafarkin halifofi

biyu, domin Imam ya san cewa halifanci a wannan zamani ta tsayu a kan
abubuwa biyu ne kuma dukkansu qarya ne ga Allah kuma Allah bai yarda da
wannan ba.
Na farko: ya karvi sharaxi sannan sai ya qi aiki da shi kamar yadda Usman ya

yi, wannan kuwa qarya ce ta magana kenan kuma abin qi wajen Allah (S.W.T).
Na biyu: ya qarvi sharaxin sai ya yi aiki da shi, wannan kuwa yana nufin
tafarkin halifofi biyu, wanda shi kuma bai yarda da su ba kuma qarya ce
wannan ta aiki kenan kuma abin qi wajen Allah. Don haka ne ma Imam Ali (A.S}
)
bai ga wata hanya ba da zai samu yardar Allah sai dai ya qi karvar hakan .
Da Imam Ali Rida (A.S) ya qi karvar halifanci sai Ma'amun ya samu rushewa
mai tsanani kuma abin da ya kira Imam saboda shi, kenan bai samu nasara a
kansa ba, sai ya bijiro masa da ya karvi mai jiran gado, kuma ya tilasta shi

a kan hakan, sai dai Imam (A.S) ya sharxanta masa cewa ba zai shiga sha'anin

daula ba, kuma ya karvi mai jiran gado a kan wannan sharaxi ne.
Ya gaji ilimi daga kakanninsa masu daraja da girma (A.S) kuma wannan ya
bayyana ga addinai da mazhabobi da fikirori a majalisin tattaunawa da
Ma'amun ya shirya masa tare da manyan mazhabobi da addinai.
Haka nan ya kasance mai yawan ibada, kuma yana raya dararensa da ita, yana
sauke Kur'ani a kwana uku, kuma saudayawa yakan yi salla da dare da wuni har

raka'o'i dubu, kuma yana yin sujada mai tsayi har sai ya xauki wasu sa'o'i,
kuma ya kasance mai yawan azumi. Ya kasance mai yawan kyawawan halaye, mai
yawan baiwa da sadaka a voye musamman a darare masu duhu.
Daga kyawawan halayensa da ladubbansa ya kasance bai tava yi wa wani magana
ta jafa'i ba kuma bai tava kaurara wa wani magana ba. Bai tava yin dogaro
tsakanin abokin zamansa ba, kuma bai tava yin qyaqyata dariya ba, bai tava
yin tofi a gaban wani ba kuma idan aka zo masa da abinci sai ya kira dukkan
ahlinsa da masu yi masa hidima ya ci tare da su.

 
 
*MATSAYIN IMAM RIDHA (a.s)*
 
Matsayin Imam Ridha (a.s) Ya zo cewa Imam Musa alKazim (a.s) ya ce wa
'ya'yansa: "Wannan dan'uwanku Ali dan Musa shi ne masanin alayen Muhammad
(s.a.w), ku tambaye shi addininku, ku kiyaye abin da yake gaya muku=E2=80=
=A6" .
Imam Ridha (a.s) ya kasance haske ne da ya sauko daga salsalar gidan hasken
da ya haskaka wannan duniya, kuma daya daga cikin waliyyan Allah (s.w.t)
masu sanar da mutane Ubnagijinsu, masu kama hannayensu zuwa ga shiriya.
Imami (a.s) shi ne wanda yake shiryar da mutane zuwa ga tafarkin tsira bayan

wucewar manzon rahama (s.a.w), domin su samu rabauta a duniya da lahira. Don
n
haka kowanne daga cikinsu haske ne da yake haskaka duniya domin mutane suka
ga hanyar da zasu taka zuwa ga Ubangiji wanda shi ne kololuwar kamalarsu.
Imami (a.s) ba kawai yana haskaka hanya ba ne, domin wannan duniyar ta taka
ta wuce zuwa ga kamala, har ma yana tafiya tare da mutane yana mai kama
hannayensu zuwa ga tsira, da kamalar isar cika.
Da wadannan bayanan ne zamu fahimci cewa; babu bambanci garemu a rayuwar
Imami (a.s) ya kasance yana halarta cikinmu ko kuwa ba ya halarta, saboda
babu bambanci gareshi a wannan yanayin, domin a kowane yanayi yana yin
aikinsa na haskaka wa bayin Allah hanyar da zasu bi domin kai wa zuwa ga
kamala.
Sai dai wani zai iya cewa me ya sa ba ma ganinsa idan ya faku daga
idanuwanmu koda kuwa yana boye a wannan duniyar?
Sai me ce masa: Muna ganin sa mana, sai dai ba ma iya gane shi, kamar dai
wani mutum ne da muke gani a hanya mu wuce ba tare da mun kiyaye shi ba,
saboda ba mu san shi ba da ma, kuma da za a tambaye mu shi zai yi mana
wahala mu gane mun wuce wani mutum, sai dai idan kuwa wani abu ya hada mu da

shi ko da kuwa tambayar wani abu ya yi a wurinmu.
Idan muka yi tunanin wannan zamu ga akwai sau da yawa wasu mutane da muke
wuce su sau tari, amma ba ma iya gane cewa; muna wuce su saboda ba mu san su

ba. Amma da zamu kalli inda suke a kowace rana, mu yi musu sallama, to daga
wannan lokacin tunaninmu zai rika lissafa su cikin mutanen da muke da
sanayya da su.
A nan ne zamu gane kimar samuwar Imam Mahadi (a.s) a cikinmu, koda kuwa ba
ma ganin sa, domin ayyukansa masu muhimmanci ko yana halarta wurinmu ko ba
ya halatta wurinmu yana nan yana yin su, akwai kuskure da wasu suke yi na
tsammanin cewa; aikinsa yana takaituwa da bayar da taimako ga miskinai, da
taimakon wanda ya bace hanya.
A yau cikin fa'idar da muka samu daga karatun Sayyid Allama Kamal Haidari
(d.z) ta Irfani mun samu wannan ma'ana madaukakiya a ciki, don haka wannan
lamari ne mai daraja da kima a sanin Imami (a.s).
Ba muna kore cewa; Imami (a.s) yana taimakon mutane ne a wurare mabambanta
ba, sai dai muna cewa ne; wannan ba shi ne aikinsa na asali ba, don haka
yana da kyau mu sanar da duniya hakikanin aikinsa na asali domin a san shi
da shi.
Idan da taimakon talakawa, da raunana, da marayu, da marasa galihu ne
aikinsa na asali da ma'anar da wasu mutane suke fassarawa, da ayyukan Imam
Mahadi (a.s) sun kasance masu karancin kima, da kampanonin Micro Soft, da
Rotary Club, da sauran kungiyoyi, hatta da Amurka sun yi alafaharin cewa; ai

gudummuwar da muke ba wa duniya ta fi tasa ke nan, domin tasu ana ganin
tasirinta a fili.
Don haka aikin Imam Mahadi (a.s) aiki ne mai muhimmanci ba karami ba,
ruwayoyi sun nuna cewa: "Da duniya zata yi kwana daya ba tare da Imami daga
cikinmu ba, da ta kisfe da mazaunanta=E2=80=A6" .
Sa'annan wadannan lakabobi, da muke gani a sunayen wasiyyan manzon Allah
(s.a.w) goma sha biyu, ba wasa ba ne, Imam Ridha (a.s) sunan Allah da ya
bayyana gareshi ke nan, kamar yadda imamin wannan zamani Imam Mahadi (a.s)
ya samu bayyanar wannan suna na mai shiryarwa (a.s) gareshi.
Imam Ridha (a.s) yana da matsayin yardar Allah madaukaki, shi yardajje ne
abin yarda, kuma ya kasance wannan yardar tasa ta bayyana a zamaninsa, yayin
n
da ya kasance abin yarda ga kowane abin halitta, sai wanda ya fita daga
fidirar halittara ta dan'adamtaka.
Mu sani cewa duk yadda mutum ya kai yabon imamai (a.s) ba zai iya fadin
hakikanin abin da yake garesu na matsayi ba, domin wani harshe, ko tunani,
ko ilimi, ko dandano, ko hankali, ba zasu iya riskar hakikaninsu ba.
Amincin Allah (s.w.t) ya tabbata gareshi a ranar da aka haife shi, da ranar
da ya mutu, da ranar da za a tashe shi.
 
 
 

No comments:

Post a Comment