Friday, 27 January 2012

Jawabin Shaikh Abubakar Gumi a wajen Maulidi a Kaduna


                                              Marigayi: Shaikh Aubakar Gumi
       
Wannan shi ne jawabin da Alkalin-Alkalai na jihohin Arewa, kuma Shugaban Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam, Shaikh Abubakar Mahmoud Gumi ya yi a wajen taron maulidin Manzon Allah da aka yi ranar 28/5/69 a Dandalin wasanni na Ahmadu Bello da ke Kaduna . MUJALLAR HASKE ta watan Yuni ta shekarar 1969 ce ta kawo ‘SULEJA MEDIA WATCH’ ne ta nakalto mana wannan jawabi.

Assalamu Alaikum, wa Rahmatullahi wa barakatuhu. ’Yan uwa Musulmi, ina fuskantar da maganata a yau ta ranar tunawa da haihuwar Shugaban Halitta duka, Jagoran shiriya, Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ina gabatar da ita ga dukkan Musulmi, musamman na kasar nan wadanda suka halarci nan da wadanda ba su halarta ba.
Da fari dai ina taya dukkan Musulmi baki daya farin ciki da zagayowar wannan rana ta haihuwar wannan babban mutum wanda ba a taba samun irin sa ba, kuma har abada ba za a samu ba. Ba haihuwar ce, ko ranar abin lura ba, a’a, abin da aka haifa shi ne abin lura. An haifi Annabawa da Manzanni, kamar su Annabi Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Isa (AS), amma ba a haifi cikakken mutum, wanda ya cika komai ba a halitta da halaye da zamantakewa da shari’a kamar Annabi Muhammad (S) ba.
Saboda haka wannan babbar rana, rana ce wadda ya kamata dukkan halitta su yi alfahari da ita, ba lalle sai Musulmi kurum ba, domin shi Manzon Allah (S) rahma ne ga dukkan talikai.
A wannan rana, ina tunatar da kaina da kuma sauran ’yan uwana Musulmi kan irin nauyi da hakkin da ke gabanmu a yau, a wannan zamanin game da addinin Allah wato addinin Musulunci. Domin Allah Madaukakin Sarki ya umurce mu da tunawa junammu ayyukan alheri; kamar mu yi wa junanmu wasicci da gaskiya da hakurin bin ta.
Shi addinin Musulunci shi ne addinin da Allah ya yarda da shi, Allah ya ce, “Hakika addini a wajen Allah shi ne Musulunci”. Sura ta 3, Aya ta 19. Shi ne addinin da ya dace da addinin Annabawan da suka gabata, kamar su Annabi Adam da Nuhu da Ibrahim da Sulaiman da Musa da Isa, wanda kuma ya cika shi da aiko Annabi Muhammad (S). Saboda haka Musulunci shi ne ciko ga abin da sauran addinai suka rage.
Annabi Muhammad (S) shi ne cikamakin Annabawa, kuma Shugaban Manzannin Allah, saboda haka idan muka ce “La’ilaha illallahu Muhammadur Rasulluhi”, muna nufin cewa, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma bauta masa wajibi ne, amma ba ta hanyar da mutum ya ga dama ba, sai ta hanyar da shi Allah yake so. To, hanyar da Allah yake so ita ce wadda ya aiko Annabi Muhammad (S), saboda Annabi Muhammad shi ne babban Jakadan Allah wanda yake bayyana sakon Ubangiji; wanda sakonsa ya kunshi yadda ake bauta ga Allah.
Sakon nan kuma shi ne Alkur’ani mai tsarki, littafin Allah, wanda ba a sauya wani abu daga cikinsa. Babu wani abin da yake sauyawa a cikinsa don sauyawar zamani. Canjin zamani kuwa duk yadda ya ratsa a kansa zai dawo. Abin mamaki kuma babbar mu’ujiza ta Alkur’ani ita ce, kowane littafi, kowane iri, bayan ya shekara 50 sai ya canza kamaninsa, ko kuma a ce an shige shi. Wato dole a ce ya tsufa, ko kuma a yi ta gyara a kai, amma banda Alkur’ani. Shi tun saukar sa har zuwa yau babu wani abin da ya sake cikin sa. Shi ne dai tun tuni, kuma shi kenan! A duniya duka-duka, babu wani littafi wanda ya samu wannan siffar mai tsarki mai ban mamaki sai Alkur’ani. Dalili kuwa ya kunshi gaskiya ne, kuma gaskiya har abada ba ta sauyawa.
Manzon Allah (S), shi ne babban mai bayani game da Allah, maganarsa da aikinsa sune bayanin Alkur’ani. Saboda haka idan muka ce “La’ilaha illallah Muhammadur Rasullulah”, a takaice muna nufin, “Allah kurum shi ne ya cancanta a bautawa, kuma ta hanyar koyi da Annabi Muhammad, Manzon Allah (S) kawai”.
Annabi Muhammad (S) shi ne wanda Allah ya aiko duniya don ya zamo fitila mai shiryar da bani Adama baki daya kan hanyar da ta fi dacewa a bi game da rayuwar duniya har a sami kyakkawan sakamako a lahira. Saboda haka dole ne mu yi koyi da shi cikin ayyukansa da zantukansa da halayensa, kamar yadda Allah ya ce: “Hakika kuna da abubuwan koyi da masu kyau daga Manzon Allah ga wanda yake kaunar rahmar Allah da samun rahma a ranar lahira”, sura ta 38, Aya ta 2.
Koyi da Manzon Allah (S) shi ne ainihin son Allah da Ma’aikinsa. Wanda duk yake son Allah da Manzonsa, to, ya yi koyi da Annabi (S). Domin Allah ya ce: “Ka ce da su, ‘in dai kuna son Allah da Manzonsa, to, ku yi koyi da ni sai Allah ya so ku”, sura ta 3, Aya ta 31.
Manzon Allah (S) ya fi kowane abin halitta kyawawan halaye. Kuma da sune Allah ya yabe shi, ya ce: “Hakika kana bisa halaye masu girma”. Sura ta 68, Aya ta 3, kuma Manzon Allah ya ce, “An aiko ni ne don in cika kyawawan halaye.”
An tambayi Nana A’isha (RA), shin wadanne halaye masu girma ne wadanda Allah ya ce ya aiko su? Menene halayen Annabi? Sai ta ce: “Halayensa sune Alkur’ani”. Wato wanda duk bai san halayen Annabi ba, kuma yake son ya sani, don ya yi koyi da shi, to ya buda Alkur’ani, ya yi aiki da shi. Domin duk abin da Alkur’ani ya ce a yi ya aikata, kuma duk abin da Alkur’ani ya ce a bari , ya bari , bai saba ba.
To, a nan ina son in ambaci wasu kadan daga cikin halayen rayuwa masu kyau duniya da lahira.
Neman ilimi:- Ina jawo hankalin Musulmi a yau su tasar wa neman ilimi. Neman ilimi shi ne babban mabudi na dukkan alheran zaman duniya da na lahira. Ya ishe mu ishara cewa Allah a Alkur’anisa mai tsarki bai fara da komai ba sai da kalmar “Ikra’a”, yi karatu. Ita ce Ayar da ta fara sauka ga Manzon Allah. Wajibi ne mu nemi ilimi kowane irin kuma saboda Allah. In mun yi haka, babu mai cim mana balle a bar mu a baya. Mai ilimi a kodayashe shi ne a sama, jahili kuma komai ibadarsa shi ne a kasa. Don haka kada mu sake, mu kai yara makaranta, mu gina makarantu namu na kanmu. Mu koya wa yaranmu ilimin addini da na zaman duniya da sunan Musulunci, za su tashi da tarbiyya da Musulunci don su zama shugabannin duniya masu yin aiki da taimakon mutane tsakani da Allah.
Mu kyautata halayenmu:- Wato mu zamanto masu ‘makarimul akhlak’. Mu kyautata mu’amalarmu tsakaninmu da junanmu da kuma abokan zamanmu. Mu yi koyi da Manzon Allah (S) cikin mu’amalarsa da sauran jama’a. Kamar yadda muka ambata ne a baya cewa kyawawan halaye sune abin da Allah ya yabi Manzonsa da shi. Mu yi kokarin sauya halayenmu da ba su dace da shari’armu ba. Mu yi koyi iyakar karfinmu da halayen Sahabbai da sauran Musulmin farko game da son juna da taimakon juna da rashin zamba da yaudara, mu guji karya da saba alkawari da mugun zato ga junanmu. Mu zama mutanen kirki na Allah iyakar kokarinmu. Hali shi ne mutum. Al’ummar da duk halayenta suka yi kyau, za ta daukaka ta fitita ta buwaya. Al’ummar kuma da duk halayenta suka baci, za ta kaskanta ta wulakanta a nan duniya.
Sana’a:- Mu kula da sana’a, mu koyi sana’o’i na zaman duniya don rayuwarmu. A wajen Musulunci sana’a yanki ne na ibada. Wanda duk ya yi noma ko kira ko sassaka ko fatauci ya kyautata ta don Allah don taimakon kansa da iyalansa da jama’ar kasarsa da dukkan musulmi baki daya, babu shakka ya yi ibada wadda kuma take faralin kifaya. Shugaban dukkan Annabawan Allah (S), ya ce: “Dukiya ’yar uwar rai ce”. Wato dole ne a neme ta don rayuwa. Kuma ya ce, “mafificin mutane shi ne wanda ya fi su amfanar mutane”. Babu shakka wannan hadisi ya nuna cewa wanda yake yin sana’a yana taimakon mutane ya fi wanda ba ya yin komai ana taimakon sa ne.
Abin da aka sani ne a littattafan fikihu shi ne cewa sallar Juma’a ba ta inganta sai garin da jama’ar garin suka wadata da kansu. Wato kowace sana’a ko aiki akwai masu yin su.
To ’yan uwa wannan shi ne kadan daga cikin abubuwan da Musulunci ya umurce mu da aikata su. Ya kamata mu farka mu raya addinin Allah ta hanyar aiki da shi. To, wannan rana ta Maulid, babu shakka tana tuna mana hakkinmu a yau. Muna fatan Allah ya ba mu albarkar wannan ranar, ya taimake mu da son Manzon Allah da koyi da shi, amin.
Assalamu Alaikum Wa Rahamatullahi Wa Barakatuhu.

2 comments:

  1. Alhamdu lillah. Wannan bai saba da akidar Sheikh Gumi ba, da irin kiransa ga jamaar musulmi da su farka daga barci. Allah ya jikansa. Da fatan masu shirya maulidi a yanzu zasu yi koyi da wannan nasiha. Son Annabi shine koyi da abinda yazo dashi a aikace ba da fatar baki ba.

    ReplyDelete
  2. Mafi gaskiyan shaida shine abin da yafito makin abokin hasuma. Wanna shaida ne ga masu zagin maulidi a yau, cewa suna yin kuskure. Amma idan an zo da wani batanci ko al'ada a wurin mauldi Wanda bai yi daidai da tsarin addiniba, to lallai ne ayi wa'azi a hori mutane sudaina.

    ReplyDelete