Monday, 23 January 2012

JUYAYIN WAFATIN MANZON ALLAH {S.A.W.A}

Manzon Allah [SAWA] Muhammad dan Abdullah dan Abdul Mudallib dan Hashim dan Abdu Manaf dan Qusayy har zuwa Annabi Ibrahim [AS] an haife shi ne a ranar 17 ga watan Rabi'ul Awwal shekarar giwaye a garin Makka.
An aiko shi da manzanci a ranar 27 ga watan Rajab bayan cika shekaru 40.
Babbar mu'ujizar sa wadda ta wanzu har zuwa wannan lokacin ita ne Al-kur'ani.
Yayi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi'ul Awwal bayan ya cika shekaru 13 da aiko shi.
Yayi wafati ne a ranar 28 ga watan Safar yana dan shekaru 63 a duniya, kuma makwancin sa na birnin Madina inda ake ziyarar sa.
SULEJA MEDIA WATCH: na taya al'ummar musulmi tunawa da juyayin wafatin Manzon Allah [SAWA].

No comments:

Post a Comment