RAHOTON KWAMITIN SHURA NA MUTANE SHIDA WADDA KHALIFA UMAR BIN KHADDABI YA KAFA.
{1.}Wannan shi ne rahoton kwamitin shura wadda da Khalifa Umar Bin Khaddabi ya kafa, wacce za ta zabi wanda zai zama sarkin musulmi na uku a bayansa. Duk da cewa Manzon Allah {s.a.w.a} ya nada Imam Ali {a.s} a matsayin shugaban kowane mai imani bayansa. Kuma sayyadna Umar shine mutum na farko day a yi wa Imam Ali mubaya’a sannan sa Abubakar sai Usman sai Dalha da Zubair suka biyo baya. Ana iya duba tarikh! Na Muh’d Isma’il Bukhari vol. 1, p. 375 ko kuma Tafsirin Jalaluddin Suyudi mai suna: Durrul-manthur ko tafsirul-kabeer na Muh’d Ibn Jarir Dabari ko kuma tafsirul-kashaful-bayan na Imam Ahmad Sa’alabi ko kuma tafsirul-mafatihul-Gaibi na Fakhuddeen Razy Duk sun kawo cewa: “ lallai Manzon Allah ya nada Imam Ali {a.s} matsayin Khalifansa na farko bayan babu shi a ranar 18/ga watan zul-hijja a wani muhalli da ake ce masa {Ghadeer-Khum} al’amarin daya fi shahara da Hjjin ban-kwana. Amma sai gashi an shure umurnin Manzon Allah {s.a.w.a}
{2.} Mutanen da Umar dan Khaddabi ya zabo don yi wannan zama sun hada da:
{1.}Sa’ad dan Abu Wakkas
{2} Usman dan Affan
{3} Ali dan Abi-Dalib
{4}Adburrahman dan Awf
{5}Zubair dan Awwam
{6} Dalha
{3} A lokacin da Imam Ali ya ga wannan kwamitin sun karkata daga barin sa, kuma ya tabbata cewa basu da niyyar bada ragama {bai’a} ga wanda ya fi cancanta to sai ya mike ya kawo hujjojinsa domin yanke hanzari ga wanda ya ki bashi wula’a, musammam ma dayake Manzon Allah ya nada shi a matsayin shugaban kowane musulmi bayansa.
{4} IMAM ALI: {a.s} dai ya fara ne da cewa:
“Dayake fara Magana yana da wayan gasket zan farad a sunan Allah, ban taho nan ba, sai don in murkushe magan da ake ta yadawa agari cewa: Annabta da Khalifanci basu haduwa a Gida guda. Zan yarda da duk sakamakon da wannan kwamiti ta fitar da shi kuma masu yarda da shi ne.”
{5} IMAM ALI: “Ina gama ku da Allah! Shin a cikin ku akwai wani banda ni wanda yake da Baffa kamar Hamza, zakin Allah, zakin Manzon Allah kuma shugaban shahidai?” Sai kuwa yace: “wallahibabu”
{6} IMAM ALI: “Ina gama ku da Allah shin a cikin ku akwai wanda ya riga ni shiga musulunci kuma bai taba bautar wanin Allah ba a rayuwar sa? Sai kuwa y ace: “wallahi babu”
{7} IMAM ALI: “Ina gama ku da Allah shin acikin ku akwai wani banda ni wanda aka kira sunansa daga sama, ana cewa: “babu takobi sai na Zulfkar, babu wani namiji matashi sai Ali?” sai kowa yace: “wallahi hakane”
{8} IMAM ALI: “Ina gama ku da Allah akwai wani banada ni a lokacin yakin Handak lokacin da Amru bin Abdul-wuddi yake cika baki, acikin ku akwai wani wanda ya fito banda ni, shi kuma Manzon Allah yana cewa: “ku duba ku gain kafircin duniyane ya fito da karfinsa don ya yi fito-na-fito da musulunci. Don haka saran Ali nay akin Handak it ace mafi daraja a gurin Allah fiye da dukkan ibadar mutane da aljannu.” Sai kuwa yace: “wannan haka yake ya dan Abi-Dalibi”
{9}IMAM ALI: “Ina gama ku da Allah Shin akwai wani mutum wanda Manzon Allah yace masa: “ya Ali babu mai sonka sai mumini haka babu mai kin ka sai kafiri?. Sai kowa ya amsa: “wallahi babu”
{10} IMAM ALI: “Manzon Allah nacewa: “Ali har yanzu ba’a ci wannan garin da yaki ba, ka je ka debi dakarun ka ka bude garin, fatar mug are ka it ace nasara. Daga nan kuma Manzon Allah ya bani tuta na kai farmaki, inda na kada Haris da Marhab din garin Khaibar kasa. na kuma banbare jibgegiyar kofar shiga garin musulmi suka sami dammar shiga.” Kuwa yace: “lallai babu shakka wannan al’amari ya auku.”
{11} IMAM ALI: “Ina gam ku da Allah shin acikin ku akwai wani banda ni wanda yake dad an uwa kamar Ja’afaruddayar, wanda Allah ya ba shi fuka-fukai biyu yana tashi da su a cikin gidan Al’jannah?” kowa y ace: “wallahi babu}
Ana iya duba littafin Al-Ihtijaj na Shaikh Dabrisy don Karin bayani.
TAMBAYA: Ya aka yi wadannan mutane suka watsar da umurnin Manzon Allah???
TO! MU DAI: Muna fata Allah ya kara tabbatar dam u cikin cikin mabiya Imam Ali bin Abi-Dalib na hakika, karkashin jagorancin maulana sharfuddeen Syyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky {H}
MUNGODE: SULEJA MEDIA WATCH
No comments:
Post a Comment